Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (2)
Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa! Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan mako, za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantacciya kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya: Malam Baba yana saurarensa cikin natsuwa, shi kuwa ya […]
Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa! Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan mako, za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantacciya kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya:
Malam Baba yana saurarensa cikin natsuwa, shi kuwa ya ci gaba da bayaninsa. “Ina da sana’a, amma duk da haka ba na gamsuwa da abin da nake samu a sakamakonta. Kullum gani nake ya kamata a ce na samu fiye da abin da nake samu, musamman idan na yi la’akari da abokan sana’ata da irin rayuwar da na ga suna gudanarwa. Wannan yanayi da na shiga ta fuskar sana’a, ya sanya na kulla gaba tsakanina da abokan sana’ata. A kullum ina jin haushinsu, ina ganin kamar su ne suke tare mini gaba, suke hana ni samun isasshen cinikin da ya kamata in samu. A sanadiyyar wannan yanayi, bakin ciki nake da kowa, fada nake da duk makwabcina a kasuwa. Wannan matsala ma tana ci mini tuwo a kwarya, domin kuwa a kullum abin da ke zuciyata ke nan. Duk lokacin da na fita wurin sana’ata, wannan tunani ne ke sanya ni takaici da bakin ciki.”
“Wata matsala kuma da ke dugunzuma ni da tunani da ciwon zuciya, ita ce wadda ta danganci iyalina da dangina. Ba ni gamsuwa ko kadan da duk abin da matata ta aikata. A kullum gani nake tana cikin kuskure da kasawa. Don haka ba na ganin farin ciki idan ina tare da ita. Su kuma dangina, nakan kalle su a matsayin wadanda ba su kaunata da ci gabana. Nakan kalle su ma a matsayin abokan gaba, saboda kullum suna neman in biya musu wannan ko waccan bukata. Sanadiyyar haka, na kaurace musu, ba na sauraren al’amuransu. Wannan dangantaka da ke gudana tsakanina da dangina, sai ta haifa mini wata sabuwar matsala. A duk lokacin da na tuna wani ko wata daga cikinsu, sai takaici ya cika mini rayuwa. Wannan ya sanya ba ni da sukuni ko kadan. Nakan ji kamar ni jemage ne a cikin tsuntsaye da rana. Kowane lokaci sai in rika zargin wane ko wance suna gulmata ko kuma suna zagina.”
“Assha, asha! Lallai kana cikin matsala,” inji Malam Baba. “Kwantar da hankalinka, ci gaba da bayaninka har zuwa karshe.”
Ya gaya masa haka ne da nufin kwantar masa da hankali, domin kuwa ya ankara da yadda Baban Larai ya kece da hawaye, har ma yana shessheka, magana na neman gagarar fitowa daga bakinsa. Dalili ke nan ya dafa kafadarsa, yana lallashinsa, domin ya samu natsuwa. Haka kuwa ta kasance, domin cikin kankanen lokaci ya daina zubar da hawayen, ya samu natsuwa. Ya ci gaba da bayaninsa:
Za mu ci gaba