Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (3)
Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan mako, za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantacciya kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya: Baban Larai ya ci gaba da bayaninsa cewa: “Malam, […]
Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan mako, za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantacciya kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya:
Baban Larai ya ci gaba da bayaninsa cewa: “Malam, in gajarce maka labari, irin wadannan matsaloli na rayuwa, wadanda ke ci mini zuciya kuma suka yi mini dabaibayi; na kasa zaune balle tsaye, ba su bar ni ba har zuwa ga al’amuran addinina. Ta fuskar ibada, ba na samun natsuwa ko kadan wajen gudanar da Sallah ko karatun littattafan addini. Idan ina sauraren malami yana wa’azi, sai inji kamar da ni kadai yake, sai in rika tsanarsa. Na rika tunanin ko ma shaidanun aljanu ne suka dabaibaye ni?”
Jin haka, sai Malam Baba ya yi murmushi, fararen hakoransa suka bayyana. Ya buda baki ya fara magana, bayan ya dakatar da Baban Larai daga bayaninsa. “Babu ruwan wasu shaidanun aljanu da suka yi maka dabaibayi,” inji Malam Baba, yana ci gaba da murmushinsa. “Babu abin da ke damunka sai shaidanun kai kanka. Matsalarka taka ce kai kadai, amma da ikon Allah zan ba ka shawarar yadda za ka ciwo kanta. Kuma insha Allahu, wasu abubuwa ne guda uku kacal za ka sanya a zuciyarka, su zame maka tamkar madubi, su kasance maka tamkar abinci. Matukar ka tsare wadannan shawarwari guda uku da ikon Allah za ka samu waraka.”
Malam Baba ya dan dakata da maganarsa, a yayin da Baban Larai ya zura masa idanu, ya kasa kunnuwa yana saurarensa. Bai ci gaba da magana ba, sai da ya sanya hannu cikin aljihunsa na gefen riga, ya dauko wata leda mai dauke da goro. Ya dauki wani daushe guda daya ya bara, sannan ya saka ballin gefe guda a baki ya fara taunawa rukus-rukus. Bayan wasu dakikoki, sai ya ci gaba da bayaninsa.
“Baban Larai, na ji duk bayaninka kuma babu shakka kana cikin wani yanayi mai wuyar sha’ani. Amma duk da haka, idan ka natsu, ka saurare ni, matsalarka ta kawo karshe. Abin da zan sake shaida maka shi ne, ba kai kadai ka taba fuskantar irin wannan yanayi ba. Na sha haduwa da irinka, masu matsalolin rayuwa. Kai akwai ma wanda al’amarinsa ya zarce naka muni, amma da ikon Allah ya samu sa’ida,” inji shi.
“Ba maza magidanta kamarka ba, akwai ma matasa, wadanda suka fuskanci irin wadannan al’amura na rikicewar rayuwa. Bar batun maza, hatta mata ma, na sha haduwa da wadanda al’amuransu suka cunkushe. Kafin in zo kan shawarwarin da na ce zan ba ka, yi mini hakuri in ba ka labarin wata matar aure, wacce ita ma ta shiga irin wannan yanayin. Ka ga ke nan sai in jefi tsuntsaye biyu da dutse daya. Na farko, za ka karu sosai daga labarin rayuwarta, sannan kuma na biyu, da kai da ita da sauran al’umma za su karu.” Malam Baba ya dan dakata kadan. Shi kuwa Baban Larai ya kosa ma ya ji labarin matar nan.
Za mu ci gaba