Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (5)
Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan makon, za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantatta kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya: Za ka yi mamakin abin da zan gaya […]
Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan makon, za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantatta kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya:
Za ka yi mamakin abin da zan gaya maka dangane da wannan mata.” Malam Baba ya kalli Baban Larai, ya yi murmushi, sannan ya ci gaba da bayaninsa. “Na hadu da mijin matar nan a kasuwa, wani makwabcinsa ya gabatar da ni gare shi. Da yake yana cikin damuwar al’amarin matar tasa, sai labari ya hada mu, shi kuwa ya bayyana mini abin da ke damunsa. Ni kuwa sai na yi masa alkawarin zan yi kokarin ba ta wasu ’yan shawarwari, kamar yadda na yi maka irin wannan alkawarin. Cikin kwana biyu zuwa uku ina zuwa gidanta tare da mijinta, sai ga shi Allah Ya taimaka an samu kanta.
“Ya kai Baban Larai! Ka ji yadda ta kaya tsakanina da matar nan, don haka yanzu sai ka sake kasa kunnuwa sosai, domin zan ba ka shawarwarin da na yi maka alkawari,” inji Malam Baba.
“Na shirya Malam, ina saurarenka; da fatar Allah Ya yi mana jagora.” Abin da Baban Larai ya fada ke nan, a lokacin da ya gyara zama, ya kalmashe kafafu, yana sauraren Malam Baba.
Shi kuwa malamin ya sake gyara zama, ya kuma gyara murya kadan, sannan ya ci gaba da bayaninsa, yana cewa: “Kamar yadda na gaya maka tunda farko, na shaida maka cewa abubuwa uku ne kadai za su magance maka wannan matsala taka. Ni kuwa na sha maka alwashin cewa, muddin ka bibiyi abubuwan nan uku cikin tsanaki, ba tare da raba daya biyu ba, to matsalarka ta kawo karshe. Ba wannan ba kadai, lokaci zai zo, yadda kai da kanka za ka zama jagora ga wadansu, ta yadda za ka yi amfani da wadannan shawarwari guda uku don warware musu matsalolinsu na rayuwa.” Malam Baba ya fara bayaninsa, a yayin da ya kafa wa Baban Larai ido, kamar wani likitan da ke neman gano wata cuta jikin majinyaci.
Baban Larai dai yana saurare, don haka sai malamin ya ci gaba da bayaninsa. “Abu na farko da za ka sanya a ranka, sannan ka lizimci tuna shi a kowace rana shi ne: Ka tattara al’amuran rayuwarka, ka rayu a yau kadai.” Har ya yunkura zai yi tambaya, sai Malam Baba ya nuna masa hannu, ya ce ya dakata; alamar zai yi masa karin bayani.
“Ba sai ma ka yi wata tambaya ba, zan yi maka karin bayani mai gamsarwa kuma mai tsawo, har sai ka fahimci abin da nake nufi da wannan mataki na farko da na gaya maka. Bari in kara nanata maka abin da na ce: Ka tattara al’amuran rayuwarka, ka rayu a yau kadai. Abin da nake son kara bayyana maka shi ne, yau din nan da ka samu kanka a cikinta, to ka dauka ita kadai ce ranar da za ka rayu. Don haka, duk wani abin kirki da kake bukata, yi kokari ka same shi a yau din nan, ba sai gobe ba.”
Za mu ci gaba
Dausayin Kauna