Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (6)

Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa! Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan mako, za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantacciya kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya:   Jin haka, sai Baban Larai ya zaro idanu, […]

Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (6)
Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (6)

Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa! Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan mako, za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantacciya kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya:

 

Jin haka, sai Baban Larai ya zaro idanu, fuskarsa ta cika da mamaki. “Ta yaya zan tattara dukkan al’amurana kuma in gabatar da su duk a cikin rana daya?” Tambayar da ya yi wa kansa ke nan kuma ya shiga laluben amsa. Shi kuwa Malam Baba da ya ankara cewa mutumin nasa ya lula cikin kogin tunani, sai ya taba masa kafada domin ya juyo da hankalinsa. Haka kuwa aka yi, sai ga shi ya yi firgigi, kamar wanda aka tasa daga barci. Daga nan sai ya ci gaba da sauraren malamin nasa.

“Bari in yi maka fashin baki game da wannan gundarin bayani da na bijiro maka da shi. Kamar yadda Allah Ya halicce ka, ka sani cewa akwai wani babban dalili na yin haka. Wannan babban dalili kuwa shi ne ya sanya kake zaune a doron kasa. Wannan zama da za ka yi a doron kasa, kayyadadde ne; wato wani dan lokaci ne marar yawa. Ke nan akwai bukatar ka san cewa ya zama dole ka ririta wannan lokaci naka domin ka cimma nasarar rayuwarka,”

Baban Larai ya kara natsuwa, yana nadar bayanin malamin nasa. Shi kuwa ya ci gaba da cewa: “Ba za ka samu nasarar cimma biyan bukatar rayuwa ba, sai ka ci gajiyar duk wata rana da ka samu kanka a raye. Domin kuwa ba ka san ranar da za ka mutu ba. Wannan dalili ne ya sanya na ce maka ka tattara dukkan al’amuranka, ka rayu a yau kawai.

“Ta yaya za ka tattara al’amuranka a wuri guda kuma ka rayu a rana daya? Ga karin bayani: Tunda kana da yakinin cewa yau ne fa kadai kake raye, to kada ma ka kawo wa kanka abin da zai faru gobe, domin goben ba ta zo ba, kuma ba ka da tabbacin ma za ta zo. Ke nan yau da kake raye ce kadai hajarka, ita kadai ce lokacinka. To me ya kamata ka yi da lokacin rayuwarka na yau? Me ya kamata ka samu na guzuri a yau? Na tabbata kana son ka samu farin ciki, kana son ka samu arziki a matsayin guzuri. Idan har da gaske ne kana son wadannan abubuwa su same ka a rayuwarka ta yau din nan, to tabbas sai ka aikata ayyukan kwarai a yau din nan. Ba za ka iya aikata ayyukan kwarai ba sai ka kyautata dangantakarka da al’ummar da kake zaune a cikinsu. Wadannan kuwa sun hada da iyayenka, da ’yan uwanka na jini da iyalinka da makwabtanka na gida da na kasuwa ko na wurin aiki da sauransu. Duk wata dangantaka da za ka yi da su, ka tabbata ka yi ta kamar yadda ka’ida ta tanada – gaskiya da adalci da tausayi da jinkai da sanin ya kamata.

 

Za mu ci gaba

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos