Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (8)

Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa! Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan makon, za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantacciya kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya: Baban Larai ya saki wani murmushi, sannan ya ce: […]

Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (8)
Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (8)

Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa! Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan makon, za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantacciya kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya:

Baban Larai ya saki wani murmushi, sannan ya ce: “Babu shakka na gamsu da bayaninka, don haka ka ci gaba kawai, ina saurarenka.”

“Madallah,” inji Malam Baba. “Abu na biyu da a kullum ya kamata ka rika tunawa a rayuwarka shi ne: ‘Ka waiwayi baya, ka nazarci dukkan baiwa da ni’imomin da Allah Ya yi maka; sannan ka yi godiya a gare Shi.’ Wannan ita ce shawara ta biyu a gare ka. Ba haka nan zan bar ka ba da gundarinta, ya zama wajibi in yi maka fashin baki. Don haka ka ci gaba da biyo ni da kunnuwan basira.”

Malam Baba ya ci gaba da cewa: “Idan kana saurarena, ginshikai uku ke cikin wannan shawara ta biyu, wato waiwayen baya, ni’imomin da Allah Ya yi maka da kuma mika godiya ga Allah.

“A kullum ka wayi gari da safe, abin da za ka yi shi ne, ka waiwayi dukkan abin da ya faru a rayuwarka ta jiya. Cikin wannan waiwaye naka, ka maida hankali kacokan wajen nazarin ni’imomin da Allah Ya yi maka a wannan rana. Babu shakka za ka samu cewa ni’imomin da Allah Ya yi maka, ba su da iyaka kuma ba za ka iya kammala tantance su ba. Idan kuwa ba ka iya tantance dimbin ni’imomin da Allah Ya yi maka a cikin kwana daya ba, babu yadda za ka samu lokacin tunawa da wani abin bacin rai da ya same ka a wannan ranar.

Bari in ba ka misalin irin wannan nazari da za ka rika yi. Misali, a jiya, ka wayi gari a matsayin mutum kake ba dabba ba. Wannan ni’ima ce mai girma, wacce dukiya ba za ta iya samar maka da ita ba. Haka kuma ka wayi gari a matsayinka na mai lafiya ba marar lafiya ba. Ka wayi gari a matsayin mai cikakkar halitta, ga kafafuwanka a tsaye, ba ka kasance gurgu ba. Ga shi kana da yatsunka sumul, ba ka kasance kuturu ba. Ka kasance mai idanu dara-dara, ba makaho ba. Ga shi ka kasance mutum mai hankali, ba mahaukaci ba. Haka kuma sai ka yi tunanin cewa akwai fa wasu da Allah Ya halitta, duk ba su da wadannan abubuwa da ka wayi gari kana da su, wato akwai guragu da makafi da kutare da mahaukata. Kai sai Allah Ya zabe ka, Ya wadata ka da wadannan ni’imomi. To ashe ba ka da wani dalili da za ka yi bakin ciki ko ka yi fushi da rayuwa, domin kuwa Allah Ya yi maka komai. Me ya kamata ka yi ke nan da wannan arziki da ka samu? Babban abin da za ka yi shi ne, sai ka gode wa Allah, ta hanyar bin ummurninSa da bauta maSa. Sai kai ma ka yi kokarin faranta wa ’yan uwanka mutane rai, ta hanyar yi musu alheri. Ka yi musu alheri da duk abin da ya sawwaka gare ka, koda kuwa murmushi ne ka yi wa dan uwanka, tamkar ka yi masa alheri ne. Idan ka kasance a haka, babu shakka za ka samu farin ciki da kwanciyar hankali a rayuwarka.

Za mu ci gaba

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos