Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (9)
Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa! Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan mako za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantacciya kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya: Wani misalin da zan kara ba ka shi ne, […]
Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa! Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan mako za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantacciya kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya:
Wani misalin da zan kara ba ka shi ne, a labarin da ka ba ni, ka gaya mini cewa kana da matar aure da ’ya’ya, kana da gidan kanka, kana da abin hawa, kana da sana’a, inda kake samun abin masarufi na rayuwar yau da kullum. To, sai ka sanya ranka a inuwa, ka yi nazari da tunanin cewa shin wadannan abubuwa da Allah Ya ba ka, ba ni’imomi ba ne? Ni’imomi ne kam, manya a rayuwa. Domin kuwa a yau din nan, wani na nan ba ya da matar aure kamar yadda kai kake da ita. Wani kuma yana da matar amma bai da ’ya’ya kamar yadda kai Allah Ya ba ka. Kamar yadda kake da gidan kanka, inda kake zaune tare da iyalinka, wani na nan a kasuwa yake kwanciya, wani kuma a gidan haya yake. A yayin da Allah Ya sanya kana da sana’ar da kake samun kudin kashewa, wani na nan bai mallaki komai ba, ba ya da sana’a ko aikin yi, sai ya yi bara ko roko sannan yake samu. Ashe ke nan Allah Ya gama yi maka komai, abin da kawai ya rage maka shi ne, ka yi godiya gare Shi.”
A lokacin da Malam Baba ke ta bayani dalla-dalla, shi kuwa Baban Larai sai gyada kai yake, alamar dai yana fahimta kamar yadda yake gamsuwa da shi. “Wallahi Malam, wadannan bayanai naka duk haka suke. Yanzun nan, ba ka ji irin farin cikin da nake ciki ba da na kalli hoton wadannan ni’imomi da Allah Ya yi mini. A yanzu haka ma ina tuna wadansu makwabtana da nake ganin Allah bai ba su irin abubuwan da Ya ba ni ba. Akwai Malam Naturunku, wanda makaho ne shi duk tsawon rayuwarsa. Akwai wani abokina da muka taso tun muna yara, shi bai da sana’a, bai da aikin yi, bai da gida; kai bai da ma iyali har yanzun nan da nake maka magana,” inji Baban Larai, yana magana cike da farin ciki.
“Yauwa, haka nake son ji.” Malam Baba ya fadi haka, sannan ya ci gaba da cewa: “Don haka, a kullum abin da ya kamata ka sanya wa ranka ke nan, ka waiwayi baya, ka nazarci ni’imomin da Allah Ya yi maka, sannan ka gode masa. Babu shakka idan ka kwatanta da wadansu mutane da kake rayuwa a cikinsu, sai ka ga kamar ma kai kadai ne Allah Ya yi wa arziki. Idan kuwa ka gode wa ni’imar da Allah Ya yi maka, za ka kasance mai wadatar zuci. Idan ka kasance mai wadatar zuci, za ka dawwama cikin farin ciki. Ba za ka samu bakin ciki ba, domin kuwa za ka zauna tsakaninka da jama’a cikin salama da fa’ida.” Malam Baba ya kawo karshen bayaninsa na biyu ga Baban Larai.
“Gaskiya na ji dadin wadannan shawarwari naka, amma bari in yi maka tilawar gundarin abubuwan nan biyu da ka koya mini, kafin ka bayyana mini na uku. Na daya ka ce mini: ‘Ka tattara al’amuran rayuwarka, ka rayu a yau kadai.’ Na biyu ka ce mini: ‘Ka waiwayi baya, ka nazarci dukkan baiwa da ni’imomin da Allah Ya yi maka; sannan ka yi godiya a gare Shi.’ Hakika na gamsu kuma da zarar ka bayyana mini abu na uku ko shawara ta uku, zan hada su wuri guda in ci gaba da amfani da su domin bunkasa rayuwata.”
Za mu ci gaba