Darussan rayuwa daga littafin ‘Dan Agwai Da Kura’ na Taskar Tatsuniyoyi

Sunan Littafi:                        Dan Agwai Da Kura (Da Wasu Labarai) Sunan Marubuci:                 Dokta Bukar Usman OON Shekarar Wallafa:                2009 Kamfanin Wallafa:              Gidan Dabino Publishers, Kano-Najeriya. Lambar Hakkin Mallaka:   978-37416-1-6 Yawan Shafuka:                   61 Farashi:                              […]

Darussan rayuwa daga littafin ‘Dan Agwai Da Kura’ na Taskar Tatsuniyoyi

Marubuci Dokta Bukar Usman

Sunan Littafi:                        Dan Agwai Da Kura (Da Wasu Labarai)

Sunan Marubuci:                 Dokta Bukar Usman OON

Shekarar Wallafa:                2009

Kamfanin Wallafa:              Gidan Dabino Publishers, Kano-Najeriya.

Lambar Hakkin Mallaka:   978-37416-1-6

Yawan Shafuka:                   61

Farashi:                                  Ba a bayyana ba

 

Kowace al’umma tana da al’adunta, tana da hanyoyin yada labaru da hanyoyin ilimantar da mutanenta, kamar kuma take da hanyoyin nishadantarwa. Al’ummar kasar Hausa ma ba a bar ta a baya ba, kasancewar ta mallaki kyakkyawar hanyar fadakarwa, ilimantarwa da nishadantarwa ta hanyar TATSUNIYA.

A wannan littafi mai suna Dan Agwai Da Kura (Da Wasu Labarai), wanda ya kasance na 8 cikin littattafai 14 na Kundin Taskar Tatsuniyoyi, wanda shahararren marubuci, Dokta Bukar Usman OON ya tattara kuma ya kattaba, yana kunshe da tatsuniyoyi 11 da ke dauke da darussan rayuwa daban-daban. Taskace tatsuniyoyin nan cikin littafi, babban aiki ne na adana al’adun Malam Bahaushe kuma hanya ce ta sake farfado da ilimi da samar da nishadi a gargajiyance.

Kamar yadda kamfanin da ya wallafa littafin ya bayyana a shafi na biii, ya ce: “Rubutun tatsuniya abu ne mai wuyar gaske, watakila shi ya sa babu wadatattun littattafan tatsuniyoyi a cikin harshen Hausa. Amma idan ana samun masu yin hobbasa irin su Dokta Bukar Usman, za a cike wannan gibi. Lallai wannan Taskar Tatsuniyoyi nasa babban abin yabawa ne wanda zai taimaka wa masu sha’awar karartun tatsuniyoyi.”

Littafin Dan Agawai Da Kura, yana kunshe ne da babi goma sha daya, inda kowane babi ke dauke da tatsuniya guda daya, bayan shafukan da ke kunshe da bayani a kan mawallafi, abubuwan da ke ciki, godiya, sharhi daga kamfanin wallafa, gabatarwa da kuma ta’aliki. Haka kuma yana kunshe da hotuna mabambanta da suka kara wa littafin tagomashi da jan hankali, musamman ga yara.

Tatsuniya ta farko mai taken sunan littafin, wato ‘Dan Agwai Da Kura,’ ta fito ne a Babi na Daya, daga shafi na 5 zuwa na 9. Dan Agwai ne ya kiwata dan akuyarsa bul-bul, ya kai kasuwa domin ya sayar bisa farashin cewa duk mai so sai dai su fafata kokowa sau bakwai a jere, idan aka kayar da shi a jere to dan akuya ya zama nasa. Babu wanda ya amshi kalubalen sai kura amma daga karshe ba a wanye lafiya ba, domin da shi da kurar gaba daya hallaka suka yi.

Wasu daga cikin darussan tatsuniyar sun hada da cewa kwadayi mabudin wahala, domin kuwa kwadayin kura ne ya ja mata kayi ba adadi daga Dan Agwai kuma ya ja mata mutuwa daga hannun Mai-barci-bana-ya-tashi-badi. Tana nuna cewa komai karfinka, akwai wanda ya fi ka. Yadda Dan Agwai ya nuna wa kura fin karfi, haka shi ma aka nuna masa, aka halaka shi. Akwai darasin da ke nuna cewa dubara ta fi karfi muhimmanci a lamurran duniya. Abin da dabara ba ta ba kura, karfi bai ba ta ba, musamman yadda ta nemi dabara daga boka, na yadda za ta hilaci Dan Agwai har ta hada shi da ajalinsa a hannun Mai Barci. Tatsuniyar kuma tana nuna muhimmancin mai ilimi a cikin al’umma. Dubi dai yadda mutanen da suka dogara da bokaye wajen magance matsalolinsu na rayuwa. Hakan ta bayyana a tatsuniyar, yadda kura ta nemi magance matsalarta daga boka.

Babi na Biyu, daga shafi na 11 zuwa na 14 yana dauke da tatsuniya ta biyu mai taken ‘Tsintuwa.’ Labari ne da ke bayyana yadda wasu magidanta suka kasa haihuwa bayan sun kwashe shekaru da dama da yin aure. Kan haka matar saboda son haihuwa ta tsinto wani yaro kuma suka rike shi da nufin nasu, wanda daga baya ya zame masu annoba. Daga karshe dai, saboda tsananin barnar da yake masu, kan dole suka nemi hanyar rabuwa da shi, inda da kyar da taimakon shawarar boka suka samu rabuwa da shi, domin kuwa ashe dan aljani ne. Wannan tatsuniya ta koyar da darussan cewa ba zafin nema ne ke kawo samu ba, kamar kuma yadda aka nuna cewa wani hanin ga Allah baiwa ne. Allah zai iya hana ka wani abu domin hana ka fadawa matsala. Kamar dai yadda ta faru ga wadannan magidanta biyu. Tatsuniyar kuma na yin ishara ga muhimmancin hakuri da godiya da abin da Allah Ya ba ka. Idan mutum bai hakura da rabonsa ba, zai iya shiga matsala da damuwa, kamar dai yadda magidanta biyun nan suka samu kansu a wannan tatsuniya.

Tatsuniya ta uku, mai taken ‘Ya Tsinci Dami A Kala’ ta fito ne a Babi na Uku, daga shafi na 15 zuwa na 21. Labari ne na wasu yara uku da suka je daji farauta, suka kama maciji kuma suka yi shirin kashe shi domin su ci amma yaro daya daga cikinsu ya tseratar da shi saboda tausayi. Ashe macijin nan dan sarki ne ya rikida zuwa maciji, don haka sai ya saka wa yaron da alheri, inda daga karshe ma ya samu arziki mai yawa, a sakamakon wani zobe da ya samu, wanda yake masa dukkan hidimar da yake bukata a rayuwa. Wasu darussa da za a iya koya daga tatsuniyar nan sun hada da muhimmancin yin alheri da tausayi da kyautata wa mutane a rayuwa, domin kuwa shi alheri danko ne, ba ya faduwa kasa banza. Kamar dai yadda yaro ya tausaya wa maciji, inda a can gaba ya samu alherin da ya amfana har iya rayuwarsa. Akwai darasin da ke nuna illar yi wa wani mugunta da hassada. Hakan ya bayyana ga sarki da matarsa, wadanda suka yi wa yaro mai zobe mugunta, amma daga karshe suka halaka.

A Babi na Hudu, daga shafi na 23 zuwa na 26, tatsuniya ce mai taken ‘Cin Amanar Dan Uwa’ inda wa da kane suka je daji dibar fure, kamar yadda mahaifinsu ya aike su. Dan uwan da ya ga kanensa ya samu fure mafi kyau, sai ya kashe shi ya dauke nasa ya kawo gida a matsayin nasa. Daga bisani asiri ya tuno, aka gane cewa shi ne ya halaka dan uwansa.Tatsuniyar ta zo da salo mai inganci na jan hankali da tura sako, musamman ga yara; saboda wakar da ke cikinta mai dadi. Tana dauke da darussan da ke nuna sakamakon maci amana, mamugunci, kamar yadda take nuna illar hassada da kuyashi da rashin gaskiya. Haka kuma, tana nuna cewa zafin nema ba shi ke kawo samu ba. Dukkan wadannan sun bayyana ne a tsakanin wadannan yara biyu, ’yan uwan juna.

Shafi na 27 zuwa na 31 yana kunshe da babi na biyar, wanda ke dauke da tatsuniya mai taken ‘Dogarawa Uku’ masu suna ‘Gi’ da ‘Da’ da ‘Do wadanda suka kasance maha’inta kuma azzalumai a aikinsu na kula da dukiyar sarki. Sun aikata laifin sace kajin sarki, amma daga bisani aka hukunta wani mutum can na daban, sakamakon dogara da aka yi da wata gurguwar shaida. Tatsuniyar na koya mana muhimmancin yin bincike mai kyau kafin a zartar da hukunci, domin da an yi bincike yadda ya dace, da ba a hukunta Gidado ba kan laifin da wasu suka aikata. Haka kuma tatsuniyar na nuna mana illar zalunci da munafunci, kamar dai yadda wadannan dogarawa uku suka aikata. Tatsuniyar kuma ta fassara mana karin maganar da ke cewa, kama da wane ba wane ba.

A shafi na 33 zuwa na 36 kuwa, dauke suke da babi na shida da ke kunshe da tatsuniyar ‘Abotar Biri Da Kifi.’ Labari ne da ake nuna yadda wani kifi ya kulla abota da biri, abotar da ta kusa haifar da cin amana da zalunci. Babban darasin da take kowa mana shi ne, amfanin hikima da dubara. Da biri bai yi amfani da hikima ba, da ya halaka a hannun kifaye. Haka kuma akwai darasin da ke nuna mana nauyin amana da riko da gaskiya. Haka kuma, tatsuniyar ta fassara mana karin maganar da ke cewa, kwarya ta bi kwarya shi ne rayuwa, ba kamar yadda biri ya yi abota da kifi ba, wanda rayuwarsu da yanayinsu suka bambanta da juna, wanda haka ya sanya aka samu akasi.

Babi na Bakwai, daga shafi na 37 zuwa na 41, yana kunshe da tatsuniya ta bakwai, mai taken ‘Muwa Muwa’ wata rakumar dawa da ta nuna wa ’ya’yanta wariya; ta nuna kauna ga uku daga cikin ’ya’yan nata hudu. Daga karshe dai su ’ya’yan uku da take kauna sai kura ta cinye su, dayan da ba ta kaunar, shi ya rayu kuma kan dole ta dawo tana kaunarsa da tattalinsa.

Wakar da ke cikin tatsuniyar tana saka nishadi da jan hankalin, musamman yara. Tatsuniyar na nuna illar nuna bambanci tsakanin ’ya’ya kuma tana nuna illar rashin adalci. Rashin daidaito ne ya sanya rakumar ta killace ’ya’yanta uku a rami daya, inda ta bar dayan a wuri daban a waje. Da sannu kura ta gano ukun ta halaka su.

Tatsuniya ta takwas na cikin Babi na Takwas, daga shafi na 43 zuwa na 47. Labarin wasu barayi uku ne da suka addabi garinsu da sata, inda daga bisani suka tafi wani wurin suka yi aiki da sana’a suka samo dukiya suka dawo garin nasu. Abin kaddara, sai ga shi duk dukiyar da suka dawo da ita ta koma hannuwan mutanen da suka taba yi wa sata a baya.

Darussa manya guda biyar ke cikin tatsuniyar, wadanda suka hada da cewa duk mai cin amana ba ya wanyewa lafiya, kamar dai yadda barayin nan uku suka kasance. Tana nuna muhimmancin fayyace al’amari dalla-dalla, ba kamar yadda barayi uku suka yi ba, a lokacin da za su ba tsohuwa ajiyar dukiyarsu. Akwai darasin da ke nuna cewa komai hikimarka da wayonka, wani ya fi ka. Hakan ta bayyana ga tsohuwa da aka kai kararta wurin alkali, inda wani malami ya taimaka mata da dubarar da ta fitar da ita daga kangin shari’a. Akwai darasin da ke nuna cewa komai wayon marar gaskiya ba zai fita daga hukunci ba. Duba dai yadda barayi suka kasance masu wayau, amma ya zama na banza saboda sun saka kansu cikin sha’anin rashin gaskiya. Akwai babban darasin da ke nuna cewa, duk wani abu da dan Adam zai iy, to akwai sakayya daga Allah, kamar dai yadda Allah Ya yi wa masu gona sakayya daga zaluncin da barayi uku suka yi masu.

Sai kuma Babi na Tara, wanda ya fara daga shafi na 49 zuwa na 53, wanda ke dauke da tatsuniyar ‘Auta Da Dodanniya. Labarin wata dodaddniya ce da ta addabi mutanen wani gari, ta hana su sukuni, tana kashe masu mutane. Kan haka Auta maharbi ya bakunci garin amma suka hana shi makwanci, sai da kyar wani mutum ya ba shi kangon gidansa. A haka Auta ya samu nasarar kashe dodanniya, wanda dalili ke nan sarki ya yi masa sha tara ta arziki, sannan kuma ya raba garin nasa biyu ya ba shi sarautar rabi, sannan ya nada shi sarkin yakin kasar baki daya.

Darussan da suka bayyana a tatsuniyar sun hada da muhimmancin alheri, wato misalin yadda Auta ya yi wa al’umma alheri, ya kashe dodanniya saboda makwanci da aka ba shi. Shi kuma sarki ya yi masa alheri, sakamakon raba su da muguwa da ya yi. Darasin zaman duniya, na cude-ni-in-cude-ka ya bayyana, musamman al’amarin da ya faru tsakanin mutanen garin da Auta. Muhimmancin amsa da karrama bako, shi ma darasi ne ga al’umma.

Babi na Goma, daga shafi na 55 zuwa na 56, gajeruwar tatsuniya ce mai taken ‘Kuda Mai Kwadayi.’ Tatsuniyar na koya mana darasin illar kwadayi da kuma rashin kyawun hadama da abin da ka iya biyo bayan mai hadama. Hakan ta bayyana yadda wata macen kuda da ta saba zuwa kiwo a kwata ta nuna hadama, bayan ta samu abinci daga kwata amma ta ki dangana, ta nuna kwadayi wajen bin mai zuma. A garin kwadayin bin mai zuma ne ta makale ta mutu.

Babi na Goma Sha Daya kuwa ya faro ne daga shafi na 57 kuma ya karkare a shafi na 61. Yana dauke ne da tatsuniya mai taken ‘Barayin Albagadadi.’ Albagadadi wani attajiri ne mai yawan kyauta da kyautata wa mutane, mai karrama baki. Wannan kyauta da ihsani ne suka jawo masa farin jini da soyayya daga mutane, sannan kuma ya rika samun budi da arziki da kariyar Allah ga duiyarsa.

Tatsuniyar na koya mana darussan da suka hada da muhimmancin ladabi da biyayya, yadda suke kawo arziki da wadata. Haka kuma tana koya mana cewa duk mai kyauta ba ya rasawa, domin Allah zai wadata shi sannan ya ba shi kariya daga duk abin da zai cutar da shi, kamar dai yadda Albagadadi ya samu kariyar Allah daga barayin da suka je gidansa domin yi masa sata.

Babu shakka littafin nan ya tabbata rumbun koya tarbiyya, ilimantarwa, fadakarwa da nishadantarwa, kamar dai yadda Malam Salisu Saleh Na’inna ya bayyana a shafi na dbii, a ta’alikinsa ga wannan littafi, inda yake cewa: “Duk wanda ya yi sa’ar samun wadannan littattafai na Taskar Tatsuniyoyi, ba shakka ya sami abokin hira, kuma rumbun hikima da basira, da za su zama masu amfani wajen debe kewa ga yara da manya.”