Darussan rayuwa daga nasihar dattijo
Ya ku ma’abuta bibiyar wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, yau mun samu gudunmawar wani labari daga LAWAL MU’AZU BAUCHI, wanda ya bijiro mana da darussa masu kyau game da rayuwar nan tamu ta duniya. Ga yadda labarin ya kasance, sai mu nazarce shi cikin tsanaki: Wani dattijo ne marar lafiya da ya samu kansa […]
Ya ku ma’abuta bibiyar wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, yau mun samu gudunmawar wani labari daga LAWAL MU’AZU BAUCHI, wanda ya bijiro mana da darussa masu kyau game da rayuwar nan tamu ta duniya. Ga yadda labarin ya kasance, sai mu nazarce shi cikin tsanaki:
Wani dattijo ne marar lafiya da ya samu kansa a gadon asibiti kuma ya shiga gargarar mutuwa. Dalili ke nan ya shiga tattaunawa da likitan da ke kula da shi.
“Kada ka damu Likita, na san mutuwa zan yi. Ban so in zo nan asibitin ba, amma lokacin da aka kawo ni babu yadda zan yi in hana su,” inji dattijon a gadon asibiti. Ya ci gaba da maganarsa ga likitan.
“Don Allah kada ka daga hankalinka a kaina. Ka kalli gashina, duk ya tafi. Na tsufa sosai amma ka ga kai matashi ne yanzu. Na koyi abubuwa da dama a wannan rayuwar, idan ba za ka damu ba, zan so in fada maka wasu daga cikinsu, ko za su amfanar da kai nan gaba.”
Dattijon nan dai ya natsu cikin gargarar ciwo, ya zayyana wa likita bayanansa:
“Lokacin da nake dan shekara hudu, na yi tsammanin wannan duniyar an yi ta domin ni kadai ne. Bayan na zama dan shekara 14, na so a ce wannan duniyar tana karkashina, ma’ana, ni nake juya ta. Na zaci zan zama wani namijin duniya, haziki kuma gwarzon da ba a taba irinsa ba a tarihin duniyar nan.
“Da na zama dan shekara 21 kuwa, tunani ya fara canjawa, na fara nazarin yadda zan zama hamshakin mai kudi.
“A shekara 25, na fara ji a raina cewa, ya kamata a ce yanzu na samu masoyiya, wadda za mu yi aure.
“Ina kai shekara 40, na so a ce ina taimakon kowa. Yanzu da ka gan ni a nan asibitin, babu abin da nake so kamar mutuwa. Ka ga rayuwa ke nan, na yi buri masu dimbin yawa, na so abubuwa ga kaina a wadancan lokuta. Abin da na fi so shi ne in zama ina cikin farin ciki, a ce ba ni da matsalar komai a rayuwa.
“Ni a tawa karamar fahimtar, na zaci idan kana so ka kasance cikin farin ciki da annashuwa, shi ne ka saurari abin da jama’a suke fada maka. Ashe dai ba haka ba ne.
“A lokacin da na zo shiga jami’a, na so in karanta abin da ya shafi dabbobi amma kowa sai ya ce min Injiniya ya kamata in zama saboda hazaka irin tawa. Na biye musu, na dauki tasu shawarar. Na zo rayuwa ta yi mini daurin goro, babu mai biya mini kudin makaranta. Nakan yi aiki ba dare ba rana, don in samu kudi in biya wa kaina kudin makaranta amma ina, abu ya ci tura!
“Bayan na bar makarantar, na kasa saboda matsalolin da na fada maka suka sa na bar jami’a. Su wadannan mutanen da suka ce in karanta kimiyya, sai suka ce ai da ma na karanta abin da na so daga farko.
“Ina cika shekara 28, kowa ya fara damuna da batun aure. Na biye musu, na je na yi auren. Bayan shekara shida da yin aurena, kawai na dawo daga nema mana abin sawa a bakin salati sai na kama matata da makwabcina. Da na tambaye ta dalilin yin haka, kawai sai ta daga hannunta ta dalla mini mari. Raina ya yi matukar baci, amma ban ce mata komai ba. Washegari bayan na dawo daga aiki, sai na samu ta kwashe ’ya’yanmu ta gudu da su. Yanzu ga shi ta bar ni cikin kadaici.
Za mu ci gaba