Darussan rayuwa goma daga bakin Ibni kayyim Al-Jawziyyah (02)
Assalamu alaikum. Gaisuwa ga ma’abuta bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Bayan haka, a makon jiya ne muka faro tambihi a kan maudu’in da muka kira da taken Darussan rayuwa goma daga bakin Ibni kayyim Al-Jawziyya, yau kuma za mu ci gaba. Dukiya: Dukiya na daya daga cikin abubuwan da ke tafiyar da al’amuran dan […]
Assalamu alaikum. Gaisuwa ga ma’abuta bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Bayan haka, a makon jiya ne muka faro tambihi a kan maudu’in da muka kira da taken Darussan rayuwa goma daga bakin Ibni kayyim Al-Jawziyya, yau kuma za mu ci gaba.
Dukiya: Dukiya na daya daga cikin abubuwan da ke tafiyar da al’amuran dan Adam. Kowa na bukatar dukiya, wanda dalili ke nan kowa ke hankoron ganin cewa ya mallake ta. Mallakar dukiya wani al’amari ne shi ma mai zaman kansa, kamar kuma yadda gudanar da dukiyar shi ma yake cin gashin kansa na musamman. A yayin da mutum ya mallaki dukiya, sai kuma ya tsaya kai da fata, ya tabbatar da ya gudanar da ita ko ya tafiyar da ita cikin fa’ida da dacewa. Idan mutum ya mallaki Naira hamsin, sai kuma ya tsaya ya tabbatar da cewa ya kashe ta yadda za ta amfane shi a rayuwarsa ko kuma yadda za ta kawo masa wani alheri da zai amfanar da shi duniya da lahira. Misali, ina amfanin dukiyar da ka samu, alhali ka salwantar da ita ta shan giya ko caca ko kuma wajen gudanar da wata sharholiya? Ta ina wadannan ayyukan za su amfane ka? Babu wani amfani a nan, domin kuwa giya da caca da sauran ja’iranci irinsu, babu abin da za su haddasa wa mutum da al’umma sai asara da lalacewa. Fa’idar da malam yake son mu amfana a nan ita ce, mu gudanar da dukiyar da muka samu bisa hanyar da ta dace, mu kaurace wa almubazzaranci da shashanci. Mu kasance dukiyarmu ta zama abar da ke sawo mana farin cikin duniya da na lahira, ta kasance dukiyar da za ta amfane mu da kanmu da kuma sauran al’umma da ke tare da mu. Allah Ya sa mu dace, amin.
Zukatanmu: Kowane mutum yana da tsokar zuciya a kirjinsa, wacce da ita jikinsa ke amfani wajen dorewar rayuwa. Dukkan bincike ya tabbatar da cewa zuciya ita ce ke tafiyar da dukkan al’amuran dan Adam. Idan zuciyar mutum ta kasance mai karfi, lallai mutum zai kasance kakkarfa mai karfin kuduri. Idan zuciya ta kasance tattausa, mai saukin al’amari, haka mamallakinta zai kasance. Idan zuciya ta kasance ballagaza, mai tunanin ashararanci da shashanci, babu shakka haka mutum zai kasance. Don haka, babban abin da ya kamata mu duba shi ne, mu yi wa kanmu fandeshin mai karfi, ta hanyar ladabatar da zukatanmu domin su kasance zukata masu kyawawan kuduri, zukata masu tafiyar da kyakkyawan tunani. Idan muka samu tsarkakakkar zuciya, sai ta taimaka mana mu kasance mutane masu tsarki. Za mu kasance mutane masu godiya da hamdala da yanayin rayuwar da muka samu kanmu a ciki. Zuciya mai kyau, mai tsarki, ita za ta hana mu aikata muggan abubuwa, ita za ta sanya mu sanya kaunar Allah a cikin al’amuranmu. Idan kuwa muka kasance cikin kaunar Allah a kowane lokaci, babu yadda za mu tabe, babu yadda za a yi mu rika aikata ayyukan da ba Ya so; sai dai mu kasance masu sara suna duban bakin gatari. Idan kuwa muka banzatar da zukatanmu, lallai za mu kasance karkatattu, ashararai, tababbu, domin kuwa zukatan namu za su jagorance mu ne zuwa ga asara da ayyukan fasadi da badala. Don haka, Malam Al-Jawziyya yana gaya mana cewa lallai mu tabbatar da cewa mun tsarkake zukatanmu, domin mu ci gajiyar kyawawan al’amura a duniya da lahira.
Jikinmu: Darasi na biyar da za mu duba, shi ne jikinmu. Koewane dan Adam yana da jiki, jikin nan kuwa ya kunshi kai, ciki, hannuwa, kafafu da sauransu. Ba a banza muka kasance a duniya ba, don haka kamata ya yi mu yi aiki da jikinmu wajen gudanar da rayuwar da ta dace, rayuwar da ta kamata. Idanuwanmu, mu yi amfani da su wajen kallon abubuwan da za su amfane mu, ba wadanda za su gadar mana da illa ba. Hannuwanmu, mu yi amfani da su wajen aikata abubuwan da za su taimake mu da ’yan uwanmu. Kada mu yin amfani da hannuwanmu wajen kulla wani mugun abu da zai halaka mu da al’ummarmu gaba daya. A takaice, malam yana nuna mana cewa, madamar ba mu yi amfani da karfin jikinmu yadda ya dace ba, to babu shakka za mu kasance marasa amfani ga kauwananmu, marasa amfani ga al’ummarmu. Abin da Malam yake fada mana shi ne, mu yi amfani da jikinmu wajen bautar Allah. Bautar Allah a nan, ba ta tsaya ne kawai ga Sallah da Azumi da Zakka da sauransu kadai ba. A’a, hatta aikin da kake gudanarwa domin samun abin masarufi, ka sanya Allah a cikinsa, yadda zai zama mai amfani. Duk aikin da ka san babu Allah a cikinsa, to ka yi saurin kaurace masa, idan ba haka ba kuwa, to lallai jikinka ya zama abin banza; domin ba zai tsinana maka abin alheri ba.
Za mu ci gaba