Darussan rayuwa goma daga bakin Ibni kayyim Al-Jawziyyah (2)
Assalamu alaikum. Gaisuwa ga ma’abuta bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Bayan haka, a makon jiya ne muka faro tambihi a kan maudu’in da muka kira da taken Darussan rayuwa goma daga bakin Ibni kayyim Al-Jawziyya, yau kuma za mu ci gaba. A makon jiya, mun tsaya ne a darasi na uku, inda wannan mashahurin […]
Assalamu alaikum. Gaisuwa ga ma’abuta bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Bayan haka, a makon jiya ne muka faro tambihi a kan maudu’in da muka kira da taken Darussan rayuwa goma daga bakin Ibni kayyim Al-Jawziyya, yau kuma za mu ci gaba.
A makon jiya, mun tsaya ne a darasi na uku, inda wannan mashahurin malami ya nemi mu maida hankali a dukiyarmu, sannan ya nuna mana yadda za mu tafiyar da ita, yadda za ta amfane mu a rayuwarmu ta yau a nan duniya da kuma yadda za ta yi mana amfani a gobe kiyama. Bari kuma a yanzu mu duba darasi na hudu:
Zukatanmu: Kowane mutum yana da tsokar zuciya a kirjinsa, wacce da ita jikinsa ke amfani wajen dorewar rayuwa. Dukkan bincike ya tabbatar da cewa zuciya ita ce ke tafiyar da dukkan al’amuran dan Adam. Idan zuciyar mutum ta kasance mai karfi, lallai mutum zai kasance kakkarfa mai karfin kuduri. Idan zuciya ta kasance tattausa, mai saukin al’amari, haka mamallakinta zai kasance. Idan zuciya ta kasance ballagaza, mai tunanin ashararanci da shashanci, babu shakka haka mutum zai kasance. Don haka, babban abin da ya kamata mu duba shi ne, mu yi wa kanmu fandeshin mai karfi, ta hanyar ladabatar da zukatanmu domin su kasance zukata masu kyawawan kuduri, zukata masu tafiyar da kyakkyawan tunani. Idan muka samu tsarkakakkar zuciya, sai ta taimaka mana mu kasance mutane masu tsarki. Za mu kasance mutane masu godiya da hamdala da yanayin rayuwar da muka samu kanmu a ciki. Zuciya mai kyau, mai tsarki, ita za ta hana mu aikata muggan abubuwa, ita za ta sanya mu sanya kaunar Allah a cikin al’amuranmu. Idan kuwa muka kasance cikin kaunar Allah a kowane lokaci, babu yadda za mu tabe, babu yadda za a yi mu rika aikata ayyukan da ba Ya so; sai dai mu kasance masu sara suna duban bakin gatari. Idan kuwa muka banzatar da zukatanmu, lallai za mu kasance karkatattu, ashararai, tababbu, domin kuwa zukatan namu za su jagorance mu ne zuwa ga asara da ayyukan fasadi da badala. Don haka, Malam Al-Jawziyya yana gaya mana cewa lallai mu tabbatar da cewa mun tsarkake zukatanmu, domin mu ci gajiyar kyawawan al’amura a duniya da lahira.
Jikinmu: Darasi na biyar da za mu duba, shi ne jikinmu. Koewane dan Adam yana da jiki, jikin nan kuwa ya kunshi kai, ciki, hannuwa, kafafu da sauransu. Ba a banza muka kasance a duniya ba, don haka kamata ya yi mu yi aiki da jikinmu wajen gudanar da rayuwar da ta dace, rayuwar da ta kamata. Idanuwanmu, mu yi amfani da su wajen kallon abubuwan da za su amfane mu, ba wadanda za su gadar mana da illa ba. Hannuwanmu, mu yi amfani da su wajen aikata abubuwan da za su taimake mu da ’yan uwanmu. Kada mu yin amfani da hannuwanmu wajen kulla wani mugun abu da zai halaka mu da al’ummarmu gaba daya. A takaice, malam yana nuna mana cewa, madamar ba mu yi amfani da karfin jikinmu yadda ya dace ba, to babu shakka za mu kasance marasa amfani ga kauwananmu, marasa amfani ga al’ummarmu. Abin da Malam yake fada mana shi ne, mu yi amfani da jikinmu wajen bautar Allah. Bautar Allah a nan, ba ta tasya ne kawai ga Sallah da Azumi da Zakka da sauransu kadai ba. A’a, hatta aikin da kake gudanarwa domin samun abin masarufi, ka sanya Allah a cikinsa, yadda zai zama mai amfani. Duk aikin da ka san babu Allah a cikinsa, to ka yi saurin kaurace masa, idan ba haka ba kuwa, to lallai jikinka ya zama abin banza; domin ba zai tsinana maka abin alheri ba.
kauna: Darasi na shida ya ta’allaka ne a kan kauna. Wannan kalma, tana da tsananin muhimmanci ga dan Adam, wanda dalili ke nan ya sanya Malam ya nemi mu kula da ita. Kowane mutum yana da yanayin kauna a cikin zuciyarsa. Duk yadda ta kai ta kawo, akwai abin da mutum yake kauna a zuciyarsa. Bisa ga wannan dalilin, Malam yana nuna mana cewa, duk abin da za mu kaunata, mu kaunaci abin kirki da mutumin kirki ba akasin haka ba. A lokacin da mutum ya gina kaunarsa zuwa ga karkataccen abu, wanda ba zai amfane shi ba, ke nan ya banzatar da kaunarsa, kuma ba zai cimma wani abin kirki ba.
Duk wanda ya gina kaunar mugun aiki, da sannu zai zama mai aikata muggan abubuwa a rayuwarsa. Idan kuwa mutum ya siffatu da aikata muggan abubuwa, da sannu zai zama mai cutar da kansa da al’ummar da yake rayuwa a cikinsu. Idan kuwa ya kasance mai kaunar abubuwan kirki, da sannu zai zama mutumin kirki, wanda zai zauna cikin al’umma cikin kirki da mutunci. Ke nan zai zama mai bayyana al’amuran kirki, mai tafiyar da ayyukansa zuwa ga al’umma. Malam yana nuna mana cewa, mu karkatar da kaunarmu zuwa ga Allah. Duk abin da za mu kaunata, ya kasance Allah Ya yarda da shi. Duk wanda za mu kaunata cikin mutane, mace ko namiji, yaro ko babba, mu tabbatar da cewa yana ko tana kaunar Allah. Mai kaunar Allah shi ne zai kaunaci abin da Allah Ya yarda da shi. Abin da Allah Ya yarda da shi kuwa, shi ne zai tabbatar da ci gaba a cikin rayuwa. Akasin haka kuwa, zai haifar da lalata da lalacewa a cikin dukkan al’amura. Allah ya sa mu dace, amin!
Za mu ci gaba