Darussan rayuwa goma daga bakin Ibni kayyim Al-Jawziyyah (4)

Assalamu alaikum. Ya ku ma’abuta bibiyar filin Sinadarin Rayuwa, kamar yadda muka faro wannan sabon maudu’i a makonnin da suka gabata, mun tsaya ne a darasi na biyar daga darussa goma da muke nazarta daga bakin mashahurin malami, Ibni kayyim Al-Jawziyya. A yau kuma za mu ci daga daga darasi na shida: kauna: Darasi na […]

Darussan rayuwa goma daga bakin Ibni kayyim Al-Jawziyyah (4)
Darussan rayuwa goma daga bakin Ibni kayyim Al-Jawziyyah (4)

Assalamu alaikum. Ya ku ma’abuta bibiyar filin Sinadarin Rayuwa, kamar yadda muka faro wannan sabon maudu’i a makonnin da suka gabata, mun tsaya ne a darasi na biyar daga darussa goma da muke nazarta daga bakin mashahurin malami, Ibni kayyim Al-Jawziyya. A yau kuma za mu ci daga daga darasi na shida:

kauna: Darasi na shida ya ta’allaka ne a kan kauna. Wannan kalma, tana da tsananin muhimmanci ga dan Adam, wanda dalili ke nan ya sanya Malam ya nemi mu kula da ita. Kowane mutum yana da yanayin kauna a cikin zuciyarsa. Duk yadda ta kai ta kawo, akwai abin da mutum yake kauna a zuciyarsa. Bisa ga wannan dalilin, Malam yana nuna mana cewa, duk abin da za mu kaunata, mu kaunaci abin kirki da mutumin kirki ba akasin haka ba. A lokacin da mutum ya gina kaunarsa zuwa ga karkataccen abu, wanda ba zai amfane shi ba, ke nan ya banzatar da kaunarsa, kuma ba zai cimma wani abin kirki ba.
Duk wanda ya gina kaunar mugun aiki, da sannu zai zama mai aikata muggan abubuwa a rayuwarsa. Idan kuwa mutum ya siffatu da aikata muggan abubuwa, da sannu zai zama mai cutar da kansa da al’ummar da yake rayuwa a cikinsu. Idan kuwa ya kasance mai kaunar abubuwan kirki, da sannu zai zama mutumin kirki, wanda zai zauna cikin al’umma cikin kirki da mutunci. Ke nan zai zama mai bayyana al’amuran kirki, mai tafiyar da ayyukansa zuwa ga al’umma. Malam yana nuna mana cewa, mu karkatar da kaunarmu zuwa ga Allah. Duk abin da za mu kaunata, ya kasance Allah Ya yarda da shi. Duk wanda za mu kaunata cikin mutane, mace ko namiji, yaro ko babba, mu tabbatar da cewa yana ko tana kaunar Allah. Mai kaunar Allah shi ne zai kaunaci abin da Allah Ya yarda da shi. Abin da Allah Ya yarda da shi kuwa, shi ne zai tabbatar da ci gaba a cikin rayuwa. Akasin haka kuwa, zai haifar da lalata da lalacewa a cikin dukkan al’amura. Allah ya sa mu dace, amin!
Lokacinmu: Malam ya gaya mana cewa, a duk cikin al’amuran dan Adam, babu wani abu da ya kai muhimmanci da kimar lokaci. A cikin lokaci ne duk wani al’amari ke gudana ko kuma yake faruwa, abu mai kyau, mai amfani ko akasinsa. Ke nan, da lokaci ne mutum zai gudanar da al’amarin da zai kawo masa ci gaba, ya kawo masa nasara a rayuwa, musamman idan ya yi amfani da damar da lokacin ya ba shi cikin fa’ida. Haka kuma, da lokacin ne mutum zai girbi asara da rashi, idan ya yi kuskuren banzatar da damar da lokacin ya ara masa.
Haka kuma, bayanai gamsassu bisa hujja sun tabbatar da cewa, kowane al’amari na duniya yana da kayyadadden lokacinsa. Haka shi ma mutum dan Adam, yana da lokacin rayuwa, wanda Allah (SWT) Ya kayyade masa ya rayu. Akwai lokacin yarinta, lokacin kuruciya, lokacin tsufa da lokacin mutuwa. Haka ita kanta duniyar, an karkasa ta zuwa yanayi-yanayi da lokaci-lokaci. Misali, akwai yanayin damina da yanayin rani. Akwai lokacin hudowar rana da lokacin faduwarta. Ke nan akwai dare da rana, kuma kowane yanayi ko lokaci yana da abubuwan da suka kamace shi na musamman.
dan Adam, dole ne ya kula da yanayi da lokaci kafin ya ci gajiyarsa. Abubuwan da zai aikata da rana, sun sha bamban da wadanda zai aikata da dare, kamar kuma yadda abubuwan da zai aikata lokacin damina, suka sha bamban da wadanda zai aikata da rani. Haka kuma, abubuwan da zai aikata lokacin da yake da kuruciya, sun sha bamban da wadanda zai aikata a lokacin da ya girma, ya manyanta.
Za mu ci gaba