Darussan rayuwa uku daga labarin Malam Baba (1)

Assalamu alaikum ga ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan makon, mun kalato muku wani labari ne, wanda ke dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantatta kuma mai nasara.Wani bawan Allah ne ya samu kansa cikin rikicin rayuwa, rikici da kidimewar da suka nemi halakar da […]

Darussan rayuwa uku daga labarin Malam Baba (1)
Darussan rayuwa uku daga labarin Malam Baba (1)

Assalamu alaikum ga ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan makon, mun kalato muku wani labari ne, wanda ke dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantatta kuma mai nasara.
Wani bawan Allah ne ya samu kansa cikin rikicin rayuwa, rikici da kidimewar da suka nemi halakar da shi da duk abin da ya mallaka. Wannan mutum, Allah Ya wadata shi da abubuwa masu yawa na alheri, domin kuwa yana da ilimi, yana da sana’a, yana da gida na kansa, inda yake zaune da iyalinsa. Amma duk da haka ya kasa samun farin cikin rayuwa. A kullum yana cikin damuwa da tunani, wanda haka ya sanya ba ya da hakuri ko juriyar duk wani abin bakin ciki ko wata jarabawar rayuwa da ta fuskance shi. Yakan yi fada ko ya bata da abokai ko makwabta saboda wata rashin jituwa komai kankantar ta, koda kuwa shi ne sanadin faruwar ta. Wannan rikicewa da ta samu wannan bawan Allah, har ta dauki aniyar zauta shi.
Wata rana yana cikin tafiya, sai Allah Ya hada shi da wani mutum mai hikima, wanda ya fahimci rayuwa sosai. A sakamakon mu’amalar da suka yi ta takaitaccen lokaci da wannan kidimammen mutum, sai mai hikimar nan ya fahimci mafi yawan matsalolin da ke yi masa tarnaki; ya kuwa dauki kudurin taimaka masa da shawara, yadda zai magance wannan mataloli da suka dabaibaye shi.
Malam Baba (mai hikima) ya samu shawo kan Baban Larai (mai fuskantar matsalar rayuwa). Sun samu wuri mai inuwa sun kebe, da niyyar nazari da neman mafita ga al’amarin da ke damun shi.
“Kamar yadda na fara gaya maka matsalolina jiya,” Inji Baban Larai, ya fara bayyana wa Malam Baba abin da ke wahalar da shi a rayuwa. “Na rasa abin da ke damu na, a kullum cikin bakin ciki nake.”
“Wane irin bakin ciki kuma? Daure ka yi mini bayani dalla-dalla, ta yadda zan fahimci matsalolin, sannan in san shawarwarin da zan ba ka, domin magance su.” Inji Malam Baba.
Har Baban Larai ya buda baki zai yi magana, sai Malam Baba ya dakatar da shi, a yayin da ya sake buda baki yana cewa: “Abu ne da masana ke fada, suna cewa idan mutum ya sani kuma ya gano matsalolinsa, to ya samu rabin maganinsu. Babbar matsala ga likita ita ce idan ya kasa gane irin cutar da ke damun majinyacinsa. Don haka, kada ka boye mini duk abin da ke damun ka, ni kuma insha Allahu zan san irin matakin da za ka dauka domin shawo kansu.”
“Na farko dai, ni a kullum gani nake na fi kowa fuskantar matsalar rayuwa. Nakan tuno matsalolin da na fuskanta tun shekaru masu yawa da suka gabata. Nakan tuna kura-kuran da na yi, da yin nadamar me ya sanya ma na aikata su. Ciwon wadannan kura-kurai da na aikata sukan dabaibaye mini zuciya, wanda haka kan kidima ni da bakin ciki.”  
 Malam Baba yana saurarensa cikin natsuwa, shi kuwa ya ci gaba da bayaninsa. “Ina da sana’a, amma duk da haka ba na gamsuwa da abin da nake samu a sakamakonta. Kullum gani nake ya kamata a ce na samu fiye da abin da nake samu, musamman ma idan na yi la’akari da abokan sana’ata da irin rayuwar da na ga suna gudanarwa. Wannan yanayi da na shiga ta fuskar sana’a, ta sanya na kulla gaba tsakanina da abokan sana’ata. A kullum ina jin haushin su, ina ganin kamar su ne suke tare mini gaba, suke hana ni samun isasshen cinikin da ya kamata in samu. A sanadiyyar wannan yanayi, bakin ciki nake da kowa, fada nake da duk wani makwabcina a kasuwa. Wannan matsala ma tana ci mini tuwo a kwarya, domin kuwa a kullum abin da ke zuciyata ke nan. Duk lokacin da na fita wurin sana’ata, wannan tunani ne ke sanya ni takaici da bakin ciki.”
“Wata matsala kuma da ke dugunzuma ni da tunani da ciwon zuciya, ita ce wadda ta danganci iyalina da dangina. Ba ni gamsuwa ko kadan da duk abin da matata ta aikata. A kullum gani nake tana cikin kuskure da kasawa, don haka ba na ganin farin ciki idan ina tare da ita. Su kuma dangina, nakan kalle su a matsayin wadanda ba su kauna ta da ci gaba na. Nakan kalle su ma a matsayin abokan gaba, saboda kullum suna neman in biya musu wannan ko waccan bukata. Sanadiyyar haka, na kaurace musu, ba na sauraren al’amuransu. Wannan dangantaka da ke gudana tsakanina da dangina, sai ta haifa mini wata sabuwar matsala. A duk lokacin da na tuna wani ko wata daga cikinsu, sai takaici ya cika mini rayuwa. Wannan ya sanya ba ni da sukuni ko kadan. Nakan ji kamar ni jemage ne a cikin tsuntsaye da rana. Kowane lokaci sai in rika zargin wane ko wance suna gulma ta ne ko kuma suna zagi na.”
“Assha, asha! Lallai kana cikin matsala.” Inji Malam Baba. “Kwantar da hankalinka, ci gaba da bayaninka har zuwa karshe.” Ya gaya masa haka ne da nufin kwantar masa da hankali, domin kuwa ya ankara da yadda Baban Larai ya kece da hawaye, har ma yana shessheka, magana na neman gagarar fitowa daga bakinsa. Dalili ke nan ya dafa kafadarsa, yana lallashinsa, domin ya samu natsuwa. Haka kuwa ta kasance, domin cikin kankanen lokaci ya daina zubar da hawayen, ya samu natsuwa. Ya ci gaba da bayaninsa:
Za mu ci gaba