Darussan rayuwa uku daga labarin Malam Baba (2)
Baban Larai ya ci gaba da bayaninsa da cewa: “Malam, in gajarce maka labari, irin wadannan matsaloli na rayuwa, wadanda ke ci mini tunanin zuciya kuma suka yi mani dabaibayi; na kasa zaune balle tsaye, ba su bar ni ba har zuwa ga al’amuran addinina. Ta fuskar ibada, ba na samun natsuwa ko kadan wajen […]
Baban Larai ya ci gaba da bayaninsa da cewa: “Malam, in gajarce maka labari, irin wadannan matsaloli na rayuwa, wadanda ke ci mini tunanin zuciya kuma suka yi mani dabaibayi; na kasa zaune balle tsaye, ba su bar ni ba har zuwa ga al’amuran addinina. Ta fuskar ibada, ba na samun natsuwa ko kadan wajen gudanar da Sallah ko karatun littattafan addini. Idan ina sauraren malami yana wa’azi, sai in ji kamar da ni kadai yake, sai in rika tsanarsa. Na rika tunanin ko ma shaidanun aljanu ne suka dabaibaye ni?”
Jin haka, sai Malam Baba ya yi murmushi, fararen hakoransa suka bayyana. Ya buda baki ya fara magana, bayan ya dakatar da Baban Larai daga ci gaba da bayaninsa. “Babu ruwan wasu shaidanun aljanu da suka yi maka dabaibayi.” Inji Malam Baba, yana ci gaba da murmushinsa. “Babu abin da ke damun ka sai shaidanun kai kanka. Matsalarka taka ce kai kadai, amma da ikon Allah zan ba ka shawarar yadda za ka ciwo kanta. Kuma insha Allahu, wasu abubuwa ne guda uku kacal za ka sanya a zuciyarka, su zame maka tamkar madubi, su kasance maka tamkar abinci. Madamar ka tsare wadannan shawarwari guda uku, da ikon Allah za ka samu waraka.”
Malam Baba ya dan dakata da maganarsa, a yayin da Baban Larai ya zura masa idanu, ya kasa kunnuwa yana saurarensa. Bai ci gaba da magana ba, sai da ya sanya hannu cikin aljihunsa na gefen riga, ya dauko wata leda mai dauke da goro. Ya dauki wani daushe guda daya, ya bara, sannan ya ballin gefe guda da hakori. Ya fara taunawa rukus-rukus. Bayan wasu dakikoki, sai ya ci gaba da bayaninsa.
“Baban Larai, na ji dukkan bayaninka kuma babu shakka kana cikin wani yanayi mai wuyar sha’ani. Amma duk da haka, idan ka natsu, ka saurare ni, matsalarka ta kawo karshe. Abin da zan sake shaida maka shi ne, ba kai kadai ka taba fuskantar irin wannan yanayi ba. Na sha haduwa da irinka, masu matsalolin rayuwa. Kai akwai ma wanda al’amarin nasa ya zarce naka muni, amma da ikon Allah ya samu sa’ida.”
“Ba maza, magidanta kamar ka ba, akwai ma matasa, wadanda suka fuskanci irin wadannan al’amura na rikicewar rayuwa. Bar batun maza ba, hatta mata ma, na sha haduwa da wadanda al’amuransu suka cunkushe. Kafin in zo kan shawarwarin da na ce zan ba ka, yi mani hakuri in ba ka labarin wata matar aure, wacce ita ma ta shiga irin wannan yanayin. Ka ga ke nan sai in jefi tsuntsaye biyu da dutse daya. Na farko, za ka karu sosai daga labarin rayuwarta, sannan kuma na biyu, da kai da ita da sauran al’umma za su karu.” Malam Baba ya dan dakata kadan. Shi kuwa Baban Larai ya kosa ma ya ji labarin matar nan.
“Ita wannan mata, ta samu kanta ne cikin wata irin rayuwa mai wuyar sha’ani.” Malam Baba ya ci gaba da bayaninsa. “Ta kasance matar aure, wadda ke auren wani attajiri. Sun yi aure ne tun bai mallaki dukiyar da yake da ita ba yanzu. Suna son juna kwarai matuka, matsalolinsa nata ne, haka ita ma nata nasa ne. Yau da gobe suna zaman fahimtar juna, sannu a hankali sai matar nan ta fara shiga wasu sha’anoni na daban, wadanda a da can baya ba ta yin su. Ta kasance tana tare da wasu karkatattun kawaye, wadanda suke kawo mata tsegunguma. Yau sai su kawo mata zancen uwar miji, ko kuma su kawo mata zancen ’yan uwansa ko abokansa. Ita kuma sai ta dauka ta sanya a zuciyar ta. Ana kan haka sai ga shi dabi’unta sun canza. Mijinta ya rasa kanta ya rasa gindinta, al’amarin da ya sanya shi shiga damuwa mai yawa.
Za mu ci gaba