Darussan rayuwa uku daga labarin Malam Baba (3)

Ya ci gaba da bayaninsa, yana cewa: “Ana kan haka kuma sai dukiyarsa ta fara habaka, sannu a hankali dai ya zama attajiri sosai. Bisa kan haka ya kara aure, ya kasance mai mata biyu. Wannan aure da ya kara, shi ya kara saka rayuwar matarsa ta farko cikin garari. Abubuwan sai suka taru suka […]

Darussan rayuwa uku daga labarin Malam Baba (3)
Darussan rayuwa uku daga labarin Malam Baba (3)

Ya ci gaba da bayaninsa, yana cewa: “Ana kan haka kuma sai dukiyarsa ta fara habaka, sannu a hankali dai ya zama attajiri sosai. Bisa kan haka ya kara aure, ya kasance mai mata biyu. Wannan aure da ya kara, shi ya kara saka rayuwar matarsa ta farko cikin garari. Abubuwan sai suka taru suka cakude mata. Muggan kawayen nan da take tare da su, suka kara ingiza ta cikin bala’i, domin kuwa baya ga tsegunguma da suke kai mata, sai ma wasu daga cikinsu suka hada ta da bokaye; wai domin ta samu nasarar mallake mijinta, sannan  ta samu galaba kan kishiyarta.
“Bisa kan haka sai zama tsakaninsu ya munana, a dole mijin nan nasu ya raba musu gida, kowacce da nata gidan. Maimakon al’amari ya yi wa uwargidan sauki, sai ma ya kara bunkasa. Ta zama kamar mai rariyar hannu, duk abin da ta samu sai ya lalace. Wannan al’amari ya sanya ta fara ganin bakin kowa. Ta shiga rigima da fada da kowa. Tun daga kan mijinta da makwabtanta da sauran abokan zaman da Allah Ya hada ta da su, ba ta daraja kowa. A kullum tunaninta yana ba ta cewa ba su kaunar ta.
“In gajarce maka labari, wannan mata dai ta zama wata annoba cikin unguwarsu. Ita kanta ba ta da sukuni, domin kuwa tana cikin tunani da damuwa. Duk wani abu da Allah Ya ba ta, sai ta raina, gani take kishiyarta ta fi ta komai, sannan kuma mijinta, tana ganinsa kamar abokin gabar ta. Ko ya kwantar da hankali ya yi mata bayani, ba ta saurarensa, domin kuwa bai ma ishe ta ba. Wannan dalili ne ya sanya ya yi watsin karan mahaukaciya da ita. Tsakaninsa da ita, sai dai ya aika mata da kayan abinci da kudin cefane, domin kuwa gidanta ma bai shigo a gare shi. Kafin ya dauki wannan mataki, kullum ya shiga gidan, babu wata maganar alheri da ke fitowa daga bakinta a kansa. Haka kuma, idan ya kalli yanayinta da al’amarin da take ciki, sai hankalinsa ya rika tashi.
“Mijin nata, domin ya samo kan matar nan tasa, ya dauki matakai masu yawa amma a banza. Ya aika gidansu, an zo an y mata nasihohi, ta dan saduda. Kamar ta gyaru, bayan kwana biyu sai ga shi ’yar gidan jiya ta dawo. Akwai makarantar Islamiyya da take zuwa, mijin ya samu malaminsu ya shaida masa abin da ke gudana. Bayan ta saurari hudubarsa, amma duk a banza, kamar an shuka dusa. Dalili ke nan suka tara ta gefe daya, suka zuba mata ido, sai dai addu’a.
“Za ka yi mamakin abin da zan gaya maka dangane da wannan mata.” Malam Baba ya kalli Baban Larai, ya yi murmushi, sannan ya ci gaba da bayaninsa. “Na hadu da mijin matar nan ne a kasuwa, wani makwabcinsa ya gabatar da ni zuwa gare shi. Da yake yana cikin damuwar al’amarin matar nan tasa, sai labari ya hada mu, shi kuwa ya bayyana mani abin da ke damunsa. Ni kuwa sai na yi masa alkawarin zan yi kokarin ba ta wasu ’yan shawarwari, kamar dai yadda na yi maka irin wannan alkawarin. Cikin kwana biyu zuwa na uku ina zuwa gidanta, tare da mijinta, sai ga shi Allah Ya taimaka an samu kanta.
“Ya kai Baban Larai, ka ji yadda ta kaya tsakanina da matar nan, don haka yanzu sai ka sake kasa kunnuwa sosai, domin zan ba ka shawarwarin da na yi maka alkawari.” Inji Malam Baba.
“Na shirya Malam, ina sauraren ka; da fatan Allah Ya yi mana jagora.” Abin da Baban Larai ya fada ke nan, a lokacin da ya gyara zama, ya kalmashe kafafu, yana sauraren Malam Baba.
Shi kuwa malamin ya sake gyara zama, ya kuma gyara murya kadan, sannan ya ci gaba da bayaninsa, yana cewa: “Kamar yadda na gaya maka tun da farko, na shaida maka cewa abubuwa uku ne kadai za su magance maka wannan matsala taka. Ni kuwa na sha maka alwashin cewa, muddin dai ka bibiyi abubuwan nan uku cikin tsanaki, ba tare da raba daya biyu ba, to matsalarka ta kawo karshe. Ba wannan ba kadai, lokaci zai zo, yadda kai da kanka za ka zama jagora ga wasu, ta yadda za ka yi amfani da wadannan shawarwari guda uku don warware masu matsalolinsu na rayuwa.” Malam Baba ya fara bayaninsa, a yayin da ya kafa wa Baban Larai ido, kamar wani likitan da ke neman gano wata cuta jikin majinyaci.
Baban Larai dai yana saurare, don haka sai malamin ya ci gaba da bayaninsa. “Abu na farko da za ka sanya a ranka, sannan kuma ka lizimci tuna shi a kowace rana shi ne: Ka tattara al’amuran rayuwarka, ka rayu a yau kadai.” Har ya yunkura zai yi tambaya, sai Malam Baba ya nuna masa hannu, ya ce ya dakata; alamar zai yi masa karin bayani.
“Ba sai ma ka yi wata tambaya ba, zan yi maka karin bayani mai gamsarwa kuma mai tsawo, har sai ka fahimci abin da nake nufi da wannan mataki na farko da na gaya maka. Bari in kara nanata maka abin da na ce: Ka tattara al’amuran rayuwarka, ka rayu a yau kadai. Abin da nake son kara bayyana maka shi ne, yau din nan da ka samu kanka a cikinta, to ka dauka ita kadai ce ranar da za ka rayu. Don haka, duk wani abin kirki da kake bukata, yi kokari ka same shi a yau din nan, ba sai gobe ba.”
Za mu ci gaba