Darussan rayuwa uku daga labarin Malam Baba (4)
Jin haka, sai Baban Larai ya zaro idanu, fuskarsa ta cika da mamaki. ‘Ta yaya zan tattara dukkan al’amurana kuma in gabatar da su duk a cikin rana daya?’ Tambayar da ya yi wa kansa ke nan kuma ya shiga laluben amsa. Shi kuwa Malam Baba da ya ankara da cewa mutumin nasa ya lula […]
Jin haka, sai Baban Larai ya zaro idanu, fuskarsa ta cika da mamaki. ‘Ta yaya zan tattara dukkan al’amurana kuma in gabatar da su duk a cikin rana daya?’ Tambayar da ya yi wa kansa ke nan kuma ya shiga laluben amsa. Shi kuwa Malam Baba da ya ankara da cewa mutumin nasa ya lula cikin kogin tunani, sai ya taba masa kafada domin ya juyo da hankalinsa. Haka kuwa aka yi, sai ga shi ya yi firgigi, kamar wanda aka tasa daga barci. Daga nan kuma sai ya ci gaba da sauraren malamin nasa.
“Bari in yi maka fashin baki game da wannan gundarin bayani da na bijiro maka da shi. Kamar yadda Allah Ya halicce ka, ka sani cewa akwai wani babban dalili na yin haka. Wannan babban dalili kuwa shi ne ya sanya kake zaune a doron kasa. Wannan zama da za ka yi a doron kasa, kayyadadde ne; wato wani dan lokaci ne marar yawa. Ke nan akwai bukatar ka san cewa ya zama dole ka ririta wannan lokaci naka domin ka cin ma nasarar rayuwarka.”
Baban Larai ya kara natsuwa, yana nadar bayanin malamin nasa. Shi kuwa ya ci gaba da cewa: “Ba za ka samu nasarar cin ma biyan bukatar rayuwa ba, sai ka ci gajiyar duk wata rana da ka samu kanka a raye. Domin kuwa ba ka san ranar da za ka mutu ba. Wannan dalili ne ya sanya na ce maka ka tattara dukkan al’amuranka, ka rayu a yau kawai.
“Ta yaya za ka tattara al’amuranka a wuri guda kuma ka rayu a rana daya? Ga karin bayani: Tun da kana da yakinin cewa yau ne fa kadai kake raye, to kada ma ka kawo wa kanka abin da zai faru a gobe, domin goben ba ta zo ba, kuma ba ka da tabbacin ma za ta zo. Ke nan yau da kake raye ce kadai hajarka, ita kadai ce lokacinka. To me ya kamata ka yi da lokacin rayuwarka na yau? Me ya kamata ka samu na guzuri a yau? Na tabbata kana son ka samu farin ciki, kana son ka samu arziki a matsayin guzuri. Idan dai har da gaske ne kana son wadannan abubuwa su same ka a rayuwarka ta yau din nan, to tabbas sai ka aikata ayyukan kwarai a yau din nan. Ba za ka iya aikata ayyukan kwarai ba sai ka kyautata dangantakarka da al’ummar da kake zaune a cikinsu. Wadannan kuwa sun hada da iyayenka, da ’yan uwanka na jini da iyalinka da makwabtanka na gida da na kasuwa ko na wurin aiki da sauransu. Duk wata dangantaka da za ka yi da su, ka tabbata ka yi ta kamar yadda ka’ida ta tanada – gaskiya da adalci da tausayi da jin kai da sanin ya kamata.
“Da zarar gari ya waye, ka samu kanka a raye, abu na farko da za ka yi shi ne, ka yi godiya ga Allah, sannan ka kuduri aniyar cin gajiyar dukkan lokacinka na yau. Idan kana da iyali, yi kokari ka fita hakkinsu a yau din nan. Duk nauyinsu da ke kanka a yau, yi kokari ka sauke shi. Haka ma iyayenka, idan suna raye, sanya su cikin tunaninka, wato ka yi kokarin sauke nauyinsu da ke kanka. Haka su ma danginka na jini da makwabtanka na gida, suna da wani hakki a wajenka, yi kokarin ka sauke wannan nauyin a yau din nan. Idan ka fita wajen aiki ko kuma kasuwa wajen sana’arka, babban abin da za ka yi a yau din nan shi ne, yi kokari ka fita hakkin ma’aikatarka, ta wajen gudanar da aikinka cikin gaskiya da adalci daidai iyawarka. Ka rayu cikin ingantattar dangantaka tsakaninka da abokan aikinka. Idan kuma kai dan kasuwa ne, to da zarar ka fita shagonka, yi kokari ka gudanar da sana’arka cikin gaskiya da adalci. Ka kyautata dangantakarka da abokan cinikayyarka. Haka su ma makwabtanka na kasuwa, ka rayu a yau din nan cikin kyakkyawar zamantakewa tsakaninka da su.”
“Kana saurare na sosai?” Tambayar da Malam Baba ya yi wa Baban Larai ke nan.
Shi kuwa ya amsa da cewa: “kwarai kuwa, ina saurarenka, kuma yanzu ne na kara fahimtar inda ka dosa.”
“Na’am. To ka kara ara mani kunnuwanka, ga wata ’yar tambaya da zan yi maka. Ka duba irin dimbin aikin da ke gabanka a yau kadai. Shin kana da lokacin da za ka bata wajen yin fushi ko yin mugunta ga wani? Na tabbata ba ka da wani isasshen lokacin da za ka bata wajen yin haka. A yau din nan, idan ka rayu cikin al’umma cikin kyautata dangantaka tsakaninka da rukunnan mutanen da na lissafa maka a baya, to tabbas za ka samu kanka cikin annashuwa da farin ciki. Lokacin da ka fita hakkin iyalanka da iyayenka da dangankinka da abokan aikinka ko sana’arka da sauran duk wanda za ka hadu da shi a yau, ina tabbatar maka da cewa ka ci ribar rayuwar yau din nan ke nan.”
“Don haka, sake sanya darasinmu na daya a ranka, ka wayi gari kullum kana tuna shi: Ka tattara dukkanal’amuranka, ka rayu a yau kadai. Sai kuma ka saurari darasi na biyu, cikin ukun da na ce zan shaida maka.
Za mu ci gaba