Darussan rayuwa uku daga labarin Malam Baba (5)

Baban Larai ya saki wani murmushi, sannan ya ambata cewa: “Babu shakka na gamsu da bayaninka, don haka ka ci gaba kawai, ina sauraren ka.”“Madallah.” Inji Malam Baba. “Abu na biyu da a kullum ya kamata ka rika tunawa a rayuwarka shi ne: ‘Ka waiwayi baya, ka nazarci dukkan baiwa da ni’imomin da Allah Ya […]

Darussan rayuwa uku daga labarin Malam Baba (5)
Darussan rayuwa uku daga labarin Malam Baba (5)

Baban Larai ya saki wani murmushi, sannan ya ambata cewa: “Babu shakka na gamsu da bayaninka, don haka ka ci gaba kawai, ina sauraren ka.”
“Madallah.” Inji Malam Baba. “Abu na biyu da a kullum ya kamata ka rika tunawa a rayuwarka shi ne: ‘Ka waiwayi baya, ka nazarci dukkan baiwa da ni’imomin da Allah Ya yi maka; sannan ka yi godiya a gare Shi.’ Wannan ita ce shawara ta biyu a gare ka. Ba haka nan zan bar ka ba da gundarinta, ya zama wajibi in yi maka fashin baki. Don haka ka ci gaba da biyo ni da kunnuwan basira.”
Malam Baba ya ci gaba da cewa: “Idan kana saurare na, ginshikai uku ke cikin wannan shawara ta biyu, wato waiwayen baya, ni’imomin da Allah Ya yi maka da kuma mika godiya ga Allah.
“A kullum ka wayi gari da safe, abin da za ka yi shi ne, ka waiwayi dukkan abin da ya faru a rayuwarka ta jiya. Cikin wannan waiwaye naka, ka maida hankali kacokan wajen nazarin ni’imomin da Allah Ya yi maka a wannan rana. Babu shakka za ka samu cewa ni’imomin da Allah Ya yi maka, ba su da iyaka kuma ba za ka iya kammala tantance su ba. Idan kuwa ba ka iya tantance dimbin ni’imomin da Allah Ya yi maka a cikin kwana daya ba, babu yadda za ka samu lokacin tunawa da wani abin bacin rai da ya same ka a wannan ranar.
Bari in ba ka misalin irin wannan nazari da za ka rika yi. Misali, a jiya, ka wayi gari a matsayin mutum kake ba dabba ba. Wannan ni’ima ce mai girma, wacce dukiya ba za ta iya samar maka da ita ba. Haka kuma ka wayi gari a matsayinka na mai lafiya ba marar lafiya ba. Ka wayi gari a matsayin mai cikakkar halitta, ga kafafuwanka a tsaye, ba ka kasance gurgu ba. Ga shi kana da yatsunka sumul, ba ka kasance kuturu ba. Ka kasance mai idanu dara-dara, ba makaho ba. Ga shi ka kasance mutum mai hankali, ba mahaukaci ba. Haka kuma sai ka yi tunanin cewa akwai fa wasu da Allah Ya halitta, duk ba su da wadannan abubuwa da ka wayi gari kana da su, wato akwai guragu da makafi da kutare da mahaukata. Kai sai Allah Ya zabe ka, Ya wadata ka da wadannan ni’imomi. To ashe ba ka da wani dalili da za ka yi bakin ciki ko ka yi fushi da rayuwa, domin kuwa Allah Ya yi maka komai. Me ya kamata ka yi ke nan da wannan arziki da ka samu? Babban abin da za ka yi shi ne, sai ka gode wa Allah, ta hanyar bin ummurninSa da bauta maSa. Sai kai ma ka yi kokarin faranta wa ’yan uwanka mutane rai, ta hanyar yi musu alheri. Ka yi musu alheri da duk abin da ya sawwaka gare ka, koda kuwa murmushi ne ka yi wa dan uwanka, tamkar ka yi masa alheri ne. Idan ka kasance a haka, babu shakka za ka samu farin ciki da kwanciyar hankali a rayuwarka.
“Wani misalin da zan kara ba ka shi ne, a labarin da ka ba ni, ka gaya mini cewa kana da matar aure da ’ya’ya, kana da gidan kanka, kana da abin hawa, kana da sana’a, inda kake samun abin masarufi na rayuwar yau da kullum. To sai ka sanya ranka a inuwa, ka yi nazari da tunanin cewa shin wadannan abubuwa da Allah Ya ba ka, ba ni’imomi ba ne? Ni’imomi ne kam, manya a rayuwa. Domin kuwa a yau din nan, wani na nan ba shi da matar aure kamar yadda kai kake da ita. Wani kuma yana da matar amma bai da ’ya’ya kamar yadda kai Allah Ya ba ka. Kamar yadda kake da gidan kanka, inda kake zaune tare da iyalinka, wani na nan a kasuwa yake kwanciya, wani kuma a gidan haya yake. A yayin da Allah Ya sanya kana da sana’ar da kake samun kudin kashewa, wani na nan bai mallaki komai ba, ba ya da sana’a ko aikin yi, sai ya yi bara ko roko sannan yake samu. Ashe ke nan Allah Ya gama yi maka komai, abin da kawai ya rage maka shi ne, ka yi godiya a gare Shi.”
A lokacin da Malam Baba ke ta bayani dalla-dalla, shi kuwa Baban Larai sai gyada kai yake, alamar dai yana fahimta kamar kuma yadda yake gamsuwa da shi. “Wallahi Malam, wadannan bayanai naka duk haka suke. Yanzun nan, ba ka ji irin farin cikin da nake ciki ba da na kalli hoton wadannan ni’imomi da Allah Ya yi mini. A yanzu haka ma ina tuna wasu makwabtana da nake ganin Allah bai ba su irin abubuwan da ya ba ni ba. Akwai Malam Naturunku, wanda makaho ne shi duk tsawon rayuwarsa. Akwai wani abokina da muka taso tun muna yara, shi bai da sana’a, bai da aikin yi, bai da gida; kai bai da ma iyali har yanzun nan da nake maka magana!” Inji Baban Larai, yana magana cike da farin ciki.
“Yauwa, haka nake son ji.” Malam Baba ya fadi haka, sannan ya ci gaba da cewa: “Don haka, a kullum abin da ya kamata ka sanya wa ranka ke nan, ka waiwayi baya, ka nazarci ni’imomin da Allah Ya yi maka, sannan ka gode masa. Babu shakka idan ka kwatanta da wasu mutane da kake rayuwa a cikinsu, sai ka ga kamar ma kai kadai ne Allah Ya yi wa arziki. Idan kuwa ka gode wa ni’imar da Allah Ya yi maka, za ka kasance mai wadatar zuci. Idan ka kasance mai wadatar zuci, za ka dawwama cikin farin ciki. Ba za ka samu bakin ciki ba, domin kuwa za ka zauna tsakaninka da jama’a cikin salama da fa’ida.” Malam Baba Ya kawo karshen bayaninsa na biyu ga Baban Larai.
“Gaskiya na ji dadin wadannan shawarwari naka, amma bari in yi maka tilawar gundarin abubuwan nan biyu da ka koya mini, kafin ka bayyana mini na uku. Na daya ka ce mini: ‘Ka tattara al’amuran rayuwarka, ka rayu a yau kadai.’ Na biyu ka ce mini: ‘Ka waiwayi baya, ka nazarci dukkan baiwa da ni’imomin da Allah Ya yi maka; sannan ka yi godiya a gare Shi.’ Hakika na gamsu kuma da zarar ka bayyana mini abu na uku ko shawara ta uku, zan hada su wuri guda in ci gaba da amfani da su domin bunkasa rayuwata.”
Za mu ci gaba