Darussan rayuwa uku daga labarin Malam Baba (6)
Gaisuwa ga ma’abuta bibiyar Sinadarin Rayuwa, assalamu alaikum. Bayan haka, a wannan makon, da ikon Allah za mu karkare wannan maudu’i da muka faro makonni biyar da suka gabata. A makonn jiya, mun ji yadda Malam Baba ya gamsar da Baban Larai, inda ya bayyana masa shawara ta biyu daga cikin shawarwari uku da ya […]
Gaisuwa ga ma’abuta bibiyar Sinadarin Rayuwa, assalamu alaikum. Bayan haka, a wannan makon, da ikon Allah za mu karkare wannan maudu’i da muka faro makonni biyar da suka gabata. A makonn jiya, mun ji yadda Malam Baba ya gamsar da Baban Larai, inda ya bayyana masa shawara ta biyu daga cikin shawarwari uku da ya yi alkawarin ba shi. A wannan makon kuma za mu ji abu na uku ko kuma shawara ta uku da zai ba shi. Sai a biyo domin jin yadda za ta kaya.
“Tun da na ga ka fahimta da abubuwa biyu da na bayyana maka, bari kuma yanzu ba tare da bata lokaci ba in gaya maka cikon na ukun.” Abin da Malam Baba ya fadi wa Baban Larai ke nan, lokacin da ya ga hankalinsa ya kara kwanciya.
“A kullum, ka rika tuna wannan: ‘Kada ka yi fushi!’ Fushi na daya daga cikin munanan al’amura da ke halaka mutane, yake jaza musu asara da takaici a mafi yawan lokaci.” Malam Baba zai ci gaba da bayani sai ya ga kamar Baban Larai ya canza fuska cikin mamaki, har ma ya yunkura zai yi magana, amma sai ya dakatar da shi da hannu, ya ci gaba da bayaninsa.
“Na san abin zai ba ka mamaki, a ce wai mutum kada ya yi fushi. To lallai dai kam haka al’amarin yake. Duk wani mataki da za ka iya dauka a rayuwarka domin ya hana ka yin fushi, to ka yi kokarin daukarsa. Abu ne mai wahalar gaske a ce mutum zai daina yin fushi a rayuwarsa, amma idan ka saurare ni cikin natsuwa da fahimta, za ka ga cewa hakan mai saukin aiwatarwa ne.”
Baban Larai ya sake natsuwa don ya ji yadda mutum zai magance matsalar fushi.
“Idan na ce kada ka yi fushi, ba ina nufin cewa ba za ka yi fushi ba kwata-kwata a rayuwarka, babban abin da ake nufi shi ne, kada ka sake ka dauki wani mataki ko ka zartar da hukunci alhali kana cikin fushi. Babu shakka duk wani dan Adam, akwai abin da zai iya bata masa rai ko ma ya harzuka shi. Idan haka ya faru, me ya kamata ka yi? Shi ne na ce maka ‘Kada ka yi fushi.’
“Me ya sanya fushi ya kasance abu mai muni, kuma marar alfanu ga mutum?” Tambayar da Malam Baba ya yi wa Baban Larai ke nan, amma bai jira ya ba shi amsa ba sai ya ci gaba da bayaninsa.
“Fushi dai, kamar yadda ingantattun bayanai suka gabata, daya daga cikin makamai ne na Shaidan. Haka kuma, daya daga cikin alburusan wuta ne. Idan mutum ya yi fushi, komai zai iya aikatawa, wanda kuma duk wani abu da za a aikata, idan dai a cikin fushi ne, to ba mai kyau ba ne. Duk wanda ya lizimci yanke hukunci ko aiwatar da wani abu, alhali yana cikin fushi, to zai yi nadama daga baya, domin kuwa babu alheri ga duk abin da aka aiwatar a cikin fushi.”
“To, ta yaya zan yi in magance matsalar fushi daga rayuwata, tun da dai ni dan Adam ne kuma abin zuwa yake kawai bagtatan, ba tare da mutum ya shirya zuwansa ba?”
“Yauwa dan uwa, wannan tambaya taka mai kyau ce, don haka sai ka kara saurare na da kyau. Yanzu za ka ji bayani, wanda in Allah Ya yarda zai taimaka.” Inji Malam Baba, yana magana cikin musrmushi.
“Mataki na farko da za ka dauka domin magance fushi shi ne, ka kasance mai juriyar hakuri a kowane lokaci. Idan kana yin hakuri da al’amuran da suka fuskance ka a kowane lokaci, to tabbas ba kowane abu ne zai bata maka rai ba, da har zai sanya ka fushi. Mataki na biyu shi ne, idan ma har wani ya harzuka ka ka yi fushin, to yi kokari ka mallaki kanka (zuciyarka). Kada ka aiwatar da komai a matsayin martani a lokacin. Mataki na uku shi ne, a lokacin da ka yi fushin nan, idan tafiya kake yi ka tsaya cik na dan takaitaccen lokaci. Idan a tsaye kake, ka samu wuri ka zauna kuma ka kama bakinka ka yi shiru. Kada ka furta komai. Idan Allah Ya yarda, fushin nan da ka yi zai sauka. Idan kuma harzukawar da ta sanya ka yi fushin mai tsanani ce, to idan ka samu wuri ka zauna, ka yi kokari ka yi alwala; sannan ka kurbi ruwan da ya rage na alwalwar sau uku. Babu shakka, za ka mallaki zuciyarka a wannan lokacin.”
“Na’am.” Inji Baban Larai. “Yanzu na kara fahimtar wannan batu mai cewa: ‘Kada ka yi fushi.’ Allah Ya ganar da mu, amin.”
“Wani karin bayani kuma game da wannan batu shi ne, ya kamata a kowane lokaci ka yi nazari game da sakamakon da fushi ke haifarwa. A duk lokacin da ka ji wata rashin jituwa ko fada ko husuma ta balle tsakanin wasu mutane ko al’umma, to matakin da aka dauka cikin fushi ne ya haddasa su. Idan miji ne, ka ji an ce saboda wani kankanin dalili ya saki matarsa, to fushi ne ya haddasa shi. Idan da za ka bincika, bayan ya dauki matakin, za ka same shi a matsayin mai nadama. Don haka, ‘Kada ka yi fushi!” Malam Baba ya sake jaddada bayaninsa, daga bisani kuma ya ci gaba da tariyar darussa uku da ya bayyana wa Baban Larai.
“Wani karin bayani da zan yi maka game da wannan shawara ta uku shi ne, idan ma ka lura da duniya da al’amuran da ke gabanka, ba ka da wani lokacin batawa wajen fushi. Ka duba dukkan matakan da na ce ka rika dauka a kullum, za ka ga suna da dangantaka da juna.
“Bari mu dauke su daya bayan daya mu gani. Na farko: ‘Ka tattara al’amuran rayuwarka, ka rayu a yau kadai.’ Na biyu: ‘Ka waiwayi baya, ka nazarci dukkan baiwa da ni’imomin da Allah Ya yi maka; sannan ka yi godiya a gare Shi.’ Na uku: ‘Kada ka yi fushi.’ A lokacin da ka wayi gari, ka kuduri aniyar aiwatar da al’amuranka a ranar cikin gamsuwa da biyan bukata, za ka shagaltu da wannan niyya taka. Wannan zai sanya lokaci ma ya yi maka kadan, ta yadda ba za ka samu damar yin wani abin banza ba. Idan kuma ka wayi gari, ka waiga baya cikin nazarin baiwa da kyauta da ni’imomin da Allah Ya ba ka, za ka samu kanka cikin godiya da gamsuwa da rayuwa. Wannan zai sanya ba za ka yi bakin cikin rasa wani abu ba, domin idan ka rasa wannan, to kuwa ka samu wancan. Haka kuma a lokacin da ka sanya wa ranka hakuri da dangana, sannan ka hana kanka yin fushi ko yanke hukunci a yayin fushi, babu shakka za ka gamsu da rayuwa, ba za ka yi bakin ciki ba.
“Don haka nasihata gare ka, ya kai Baban Larai, a kullum ka rika sanya wadannan abubuwa ko shawarwari guda uku a zuciyarka. Allah Ya sanya mu dace da kyakkyawar rayuwa, amin!”