Darussan shekarar 2014

Editan Aminiya, hakika shekara ta 2014 ta kasance shekara ma fi muni a tarihin dimokuradiyyar Najeriya, da rayuwar talakawan kasar, musamman kuncin rayuwa da al’ummar ke fama da shi, ga matsalar tsaro da ta karade Arewacin kasar nan, musamman Arewa maso Gabas. Mun ga yadda aka raba masu aiki don talakawa daga kujerunsu a dalilin […]

Darussan shekarar 2014
Darussan shekarar 2014

Editan Aminiya, hakika shekara ta 2014 ta kasance shekara ma fi muni a tarihin dimokuradiyyar Najeriya, da rayuwar talakawan kasar, musamman kuncin rayuwa da al’ummar ke fama da shi, ga matsalar tsaro da ta karade Arewacin kasar nan, musamman Arewa maso Gabas. Mun ga yadda aka raba masu aiki don talakawa daga kujerunsu a dalilin bayyana almundahana. ‘Yan uwanmu da dama da muke tare da su mun rabu a dalilan gudun hijra, wasu sace su aka yi, inda dubbai suka rasa rayukansu. Mun ga yadda matasa suka rasa rayukan su a wajen neman aiki a hukumar shige da fice ta kasa, a karshe suka tashi a tutar babu; mun ga yadda jami’an tsaro suka sauya aikinsu daga masu kare al’umma, zuwa masu kare wata jam’iyya, wadannan da wasu abubuwa na takaici duk sun wakana a Najeriya cikin shekarar 2014. Da wannan nike kira ga talakawa cewa, Ya kamata mu koyi darrusa, mu kuma nemi hanyar gyara kuskurenmu. Allah ya zaunar da kasar mu lafiya, a zaben da za a gudanar muke fatan za a yi a kare lafiya, ba tare da magudi ko tashin hankali ba. Amin. Daga Usman Bin Affan Damaturu 08038001563

Sakonnin waya

Ga Gwamna Lamido
Gwamna  Sule  Lamido  mun ji  ka ce  talakawa  suna  zagi  da  sukan shugabanni,  har  ka kamanta  kalaman  Gwamna Shema,  inda  ya ce talakawa  kyankyasai ne  a rinka  tattake su.  Daga  Garba  Ssabiola  Sa’idawa  Gashu’a  08096284154.

Ziyarar Jonathan ga IBB
Ziyarar da Shugaba Jonathan ya kai wa tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida a gidansa da ke Minna. Domin neman goyon bayan Babangidan a zaben da ke tafe.
Mu talakawan Nigeria bai zo mana da mamaki ba, domin Goodluck Jonathan da Janar Babangida, dukkansu danjumma ne da danjummai. Hasali ma Janar Babangida ne kanwa uwar gami wajen jefa talakan Najeriya a matsaloli iri-iri. Daga Isah Ramin Hudu, Hadejia. 08060353382.

Ga Ahmad Garban Bichi
Aminiya a mika min godiya ga damo sarkin hakuri Ahmad Garban Bichi, tsohon manajan Kasko, tsohon sakataren kogin Hadejia Jama’are, tsohon ministan kasuwanci da zuba hannun jari da ya amsa kiranmu na tsayawa takarar majalisar wakilai a Abuja. Allah ya ba da sa’a amin.
Daga Sani Bichi 09029693423

Wa’azi ga kowa
 Ko yau ko gobe Allah na iya daukar ranka, komin kudinka, kuma komin mulkinka. Wallahi Allah zai yi maka tambayoyi zafafa, musamman ma wadanda suka tara dukiya, sai dai idan ta hanyar halaka ka tara; za ka amsa tambayoyin, amma idan kudin na shan jini ne ko fillar kai da yanke al’aurar ’yan mata ne; ko kuma na danne hakkin talakawa ne; ko na ci da addini ne; ko kuma kudin riba ne? Wallahi za ka ga ’yan uwanka na dago maka hannu daga aljanna kaico! Kana cikin halaka! Daga Isma’il Lawal Bakori 08032619334.

Zabin Lamido ya yi
Editan Aminiya, zan yi tsokaci akan dan takarar Gwamnan Jigawa, Malam Aminu Ibrahim, zabo shi da Maigirma Sule Lamido ya yi, ya dace. Don shi ne shugaban ma’aikatan gidan gwamnati a zamanin Saminu da Lamido, ya yi musu biyayya; da shi aka aza dukkan harsashin ci gaban Jigawa,yasan al’ummun Jigawa kauye da birni, tunda a cikin ta yake tun farkon rayuwarsa. Kuma dan siyasa ne sak. Ana yi masa zaton zai dora akan ci gaban da Lamido ya kawo Jigawa ta zama yadda take ayau, Allah yayi mana zabi mafi alheri.Daga Idris Tela Gilima 08098012082.

Buhari ne mafita ga Najeriya
Edita, ka ba ni dama in yi tsokaci game da zaben shugaban kasa, ganin yadda aski ke kara matsowa gaban goshi. ‘Yan Najeriya hankalinsu ya karkata ga wannan zabe, saboda shi ne kawai hanyar da talakawa za su huce takaicin ukubar da talakawan suke ciki. Mu yi addu’a da fatan Allah Ya sanya zaben Janar Muhammadu Buhari shi ne mafita a garemu, tunda mun dandana zakin wahalar mulkin dimokuradiyyar PDP. Allah Ya kawo mana sauyi mai amfani. Amin. Daga Hajiya Aisha Kyauta 07055903345.

Ta’aziyyar mutanen Gombe
Allah ya jikan mutanen da suka rasa rayukansu, a harin bam din tashar mota, a garin Gombe. Da fatan Allah ya yi mana maganin duk wata kungiya ko mutum da ke da hannu a wannan hare-haren ta‘addanci da ya ki ci, ya ki cinyewa a Arewacin Najeriya.
Daga Isah Ramin Hudu, Hadejia. 08060353382.

Ta’aziyya ga al’umma
Edita don Allah ka mika min sakon ta’aziyya gsa al’ummar Musulmi game da hare-haren da suke halaka dimbin mutane. Ina kuma mika ta’aziyya ga Kannywood, bisa rasuwar jarumin nan Ibro. Allah Ya jikansu da rahama, Ya gafarta musu. Daga Ummi T/Wada Kd 08122687452.