Dasuki ga Gwamnati: Zan fasa kwai

Tsohon Mai Bai Wa Shugaban kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Kanar Sambo Dasuki, ya yi barazanar cewa zai fasa kwai kuma ya bukaci ’yan Najeriya da kada su gasgata duka zarge-zargen da ake yi masa a halin yanzu.  Ya ce akwai dimbin wasu abubuwa da bayanai da ba zai iya bayyana su ga duniya ba, […]

Dasuki ga Gwamnati: Zan fasa kwai
Dasuki ga Gwamnati: Zan fasa kwai

Tsohon Mai Bai Wa Shugaban kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Kanar Sambo Dasuki, ya yi barazanar cewa zai fasa kwai kuma ya bukaci ’yan Najeriya da kada su gasgata duka zarge-zargen da ake yi masa a halin yanzu. 

Ya ce akwai dimbin wasu abubuwa da bayanai da ba zai iya bayyana su ga duniya ba, saboda tsoron kada ya jefa tsaron kasar nan cikin hadari. “A shirye nake na gurfana a gaban kuliya a kan duka zargin da ake mini domin in tabbatar wa da ’yan Najeriya cewa ban aikata ba daidai ba, lokacin da nake ofis. Ina da tabbacin cewa za mu hadu a kotu. Ina da labari a bakina, domin akwai wasu manyan jami’ai a wannan gwamnati da suke da hannun a al’amarin,” inji shi.
A wata sanarwa da ya fitar shekaranjiya Laraba, Sambo Dasuki ya ce shi ba ya tsoron gurfana a gaban kuliya saboda shi ba barawo ba ne, kamar yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari da na kusa da shi suke yadawa. Har ila yau, ya bayyana yadda fadar shugaban kasa take yada labarin zargin da take masa da kuma wasu wadanda ba a bayyana sunansu ba da “wasan kwaikwayo.”
Ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasa ya bayar da umarnin cafke Sambo Dasukin da duk mutanen da aka samu da hannu a badakalar sayen makamai domin yaki da ta’addanci daga shekarar 2007 zuwa bana. Kuma ya bayar da umarnin kama shi ne bayan karbar kwarya-kwaryar rahoton kwamitin da ya gudanar da binciken.