Dattawan Borno sun bukaci a hukunta tsofaffin hafsoshin sojin Najeriya
kungiyar Dattawan Borno ta bukaci gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bincika tare da hukunta tsohon Shugaban kasa Jonathan da tsofaffin manyan hafsoshin sojin kasar nan, kuma a tilasta musu biyan diyya ga mutanen da aka kashe ’yan uwansu da sunan Boko Haram.Dattawan Bornon sun fadi haka ne a wata takardar sanarwar da suka raba wa […]
kungiyar Dattawan Borno ta bukaci gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bincika tare da hukunta tsohon Shugaban kasa Jonathan da tsofaffin manyan hafsoshin sojin kasar nan, kuma a tilasta musu biyan diyya ga mutanen da aka kashe ’yan uwansu da sunan Boko Haram.
Dattawan Bornon sun fadi haka ne a wata takardar sanarwar da suka raba wa manema labarai a Maiduguri dauke da sanya hannun Shugaban kungiyar Ambasada Gaji Galtimari.
kungiyar ta kuma bukaci tsofaffin jami’an gwamnatin su nemi gafarar al’ummar da yakin Boko Haram ya shafa, saboda furucin da tsohon Hafsan Tsaron Najeriya Iya Cif Marshal Aled Badeh ya yi a bikin ajiye aiki a makon jiya, kuma aka yada shi a kafafen watsa labarai, inda ya ce ya jagoranci yakin da babu makamai kuma babu kudin gudanarwa.
Datawan sun ce a baya manyan hafsoshin sun sha fadin cewa akwai kayan aiki da kudin gudanarwa, da za su yaki Boko Haram, “Wannan ya nuna cewa manyan hafsoshin
makaryata ne kuma sun yi sakaci da aiki, inda suka bari aka yi ta kashe mutane babu gaira babu dalili. Za a iya cewa da hadin bakinsu aka rika aikata wannan mummunan aiki, don haka muna bukatar gwamnatin Buhari ta dubi wannan lamari da idon rahama ta hukunta duk wani jami’in gwamnati da yake da hannu a ciki,” inji dattawan.