Dattawan Kiristocin Najeriya ko ’yan siyasa Kiristoci?
A ranar Juma’ar da ta gabata wata kungiya da ta kira kanta kungiyar Dattawan Kiristoci ta Najeriya (NCEF) wadda akasarin mambobinta ’yan siyasa Kiristoci ne daga Arewa ta fitar da wani bayani mai ban tsoro da bai kamata ya fito daga mutumin da yake kiran kansa dattijo ba. Dattijo dai ko a gidan giya ne […]
A ranar Juma’ar da ta gabata wata kungiya da ta kira kanta kungiyar Dattawan Kiristoci ta Najeriya (NCEF) wadda akasarin mambobinta ’yan siyasa Kiristoci ne daga Arewa ta fitar da wani bayani mai ban tsoro da bai kamata ya fito daga mutumin da yake kiran kansa dattijo ba. Dattijo dai ko a gidan giya ne ya kamata ya fi sauran mutanen gidan giyar natsuwa domin ya samu tsawatarwa idan ya ga za a yi ba daidai ba.
Kalaman ‘dattawan’ na iya saka zaman lafiyar kasar nan a cikin hadari a daidai wannan lokaci da take fama da matsalolin tashin hankali da ayyukan ta’addanci.
Mutanen da suka kira kansu dattawan Kiristocin wadanda ban ga wani fitaccen limamin Kirista a cikinsu face ’yan siyasa da suka hada da Solomon Asemota da Manjo Janar Joshua Dogonyaro da Manjo Janar Zamani Lekwot da Laftana Janar T. Y. danjuma (masu ritaya) da Moses Ihonde da Shyngle Wigwe da tsohon Gwamnan Jihar Anambra Dokta Chukwuemeka Ezeife, sun ce wai an riga an kaddamar da ‘jihadi’ a kasar nan, kuma mutanen da ba su zabi wannan gwamnati ba sun kwace ta inda suka ce in ba a yi hankali ba kasar tana iya wargajewa.
Hakika ganin sunan Janar Theophilus Yakubu danjuma a cikin mutanen da aka ce sun ba da sanarwar ya ba akasarin jama’ar kasar nan mamaki. Domin ba a cikin aikin soja ba, a kowace harka ana daukar Janar T.Y. danjuma a matsayin uba, uba kuwa bai ware wani daga cikin ’ya’yansa ya nuna masa kiyayya, koda ya ga dan ya aikata abin da yake ganin ba daidai ba ne a kan sauran ’ya’yansa. Kuma uban kirki ba ya fitowa kan titi ya rika fadin munanan kalamai da barazana ko tashin hankali.
Na dauka kafafen watsa labarai ne suka shirga wa Janar T.Y. danjuma karya, don haka na zuba ido ko zai fito ya musanta hannunsa a waccan sanarwa da ‘dattawan’ Kiristocin Najeriya suka bayar, ganin rashin kan gadon da bayanansu suka kunsa. To amma tunda ya yi shiru ya nuna da hannunsa da yawunsa aka yi waccan magana.
Manyan abubuwa da ‘dattawan’ Kiristocin suka tabo su ne jihadi da makomar Fulani makiyaya da kuma siyasa. Sun ce: “Babbar matsalar kasar nan ita ce an rigaya an kaddamar da jihadi a Najeriya. Kuma masu kishin Musulunci suna tsoma baki a harkokin mulkin kasar nan ta amfani da “Takiyya” (yaudarar da aka halatta) kamar yadda suka fassara, a matsayin sabon salon jihadi na ’yan boko, yayin da Boko Haram da Fulani makiyaya kuma suke jihadin makami tare da sha alwashin kawar da dimokradiyya a Najeriya.”
Game da Fulani makiyaya sun ce: “Idan ya zama wajibi a samar wa Fulani gandun kiwo, madadin makiyaya ta zamani (Ranch) wadda ita ce ake ya yi a sauran kasashen duniya, to kungiyar NCEF tana bayar da shawarar a ba wa Fulani makiyaya dajin Sambisa.”
Sai kuma cewa: “Mutanen Najeriya su zauna cikin shirin hana yanayin da wani rukuni wadansu mutane da ba jama’ar kasa ne suka zabe su ba, su kwace mulki daga shugabannin da aka zaba…”
A duba jaridar banguard ta ranar 14 ga Yuli, 2017.
Bari mu fara da batun wadanda ba su zabi shugabannin gwamnati ba da ‘dattawan’ Kiristocin suke cewa za su kwace ta, ta hanyar amfani da ‘Takiyya’ wajen shiga gwamnatin suna kokarin musuluntar da ita.
Abin tambaya wane Musulmi ne yake tsoro a kasar nan da zai boye imaninsa? Shin Musulmin Najeriya ba su fito sun bayyana ra’ayinsu da kuma zabar jam’iyyar da suke so ba? A cikin mutanen da suka yi wannan zargi wane ne dan Jam’iyyar APC? Dukansu fa ’ya’yan Jam’iyyar PDP ne da ta sha kashi a zaben shekarar 2015, to mene ne nasu da za su yi kukan wadanda ba su zabi gwamnatin ba sun kwace ta? Shin dakataccen Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Dabid Lawal wanda shi ne ruhin gwamnatin Buhari ‘Takiyya’ ya yi ya kai kan wannan kujera ko yaya? Buhari ya ba shi wannan kujera mai muhimmanci ne, saboda adalci irin na Musulmi. Ko ya kawo mazabarsa ga APC ne? Kowa ya san mutanensa PDP suka zaba, kuma ba mu san wata gudunmawa da ya bayar ga Jam’iyyar APC ba.
Janar Dogonyaro da Zamani Lekwot, mazabunsu PDP suka yi, sanatocinsu na PDP ne, ’yan majalisar wakilansu PDP ne, gwamnoni ma ba domin Musulmin da suke zagi sun hada karfi da sauran masu son canji daga Kiristoci ba, da ba za su ci zabe ba!
A matsayin Janar T.Y. danjuma da Janar Dogonyaro da Zamani Lekwot na tsofaffin sojojin da suka yi yaki kafada-da-kafada da Musulmi domin kare kasar nan bai kamata su bari bukata ta siyasa ko wadansu ’yan siyasa su rika inginza su suna kokarin wargaza kasar nan ba.
Ko Janar T.Y. danjuma ya fusata ne saboda an yayata kisan kare-dangi da aka yi wa Fulani a yankin Mambila da ke jiharsa ta Taraba? Shin kashe-kashen yankin ne kawai aka yayata ko gwamnati ta dauki mataki a kai. Ko kuwa Janar T.Y. danjuma yana goyon bayan a kawar da Fulani ne daga bayan kasa?
Maganar kaddamar da jihadi ya kamata su Janar danjuma su fito su shaida wa duniya wadanda suke jagorantar wannan ‘jihadi’ kuma yaushe suka kaddamar da shi. Amma bai kamata mutumin da ya kira kansa ‘dattijo’ ya fito yana shirga karya da kazafin da za su iya jawo zubar da jini domin kawai wata bukata ta siyasa ko neman wani mukami ba.
Kan hare-haren da ake kaiwa ga jama’a da sunan Fulani makiyaya, dattijon arziki, dattijon gaskiya, mai kaunar kasar nan, tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon, ya riga ya nuna wadanda suke haddasa rikicin, wadanda ya bayyana da makiya kasar nan da suke shiga irin ta Fulani suna kashe mutane suna lalata dukiya. Jaridun kasar nan duk sun ruwaito haka a ranar 27 ga Afrilun, 2014.
Janar Gowon ya bayyana haka ne lokacin da ya jagoranci ayarin kungiyarsa ta yi wa kasa addu’a suka kai ziyara ga Gwamnan Jihar Ebonyi na lokacin, Mista Martin Elechi a Abakaliki, inda ya ce: “Na kasa gane yadda za a ce Fulani makiyaya wadanda galibinsu yara ne kanana a ce su ne suke aikata irin wannan muguwar ta’asa a sassan kasar nan. Yaran nan suna dauke ne da sanduna suna shiryar da shanunsu ga wuraren abinci, amma yanzu wadansu mutane suna shiga suturar Fulani suna tayar da rikici. Abin tambaya, shi ne yadda aka yi suka sauya daga kananan yara masu kiwon shanu zuwa manyan masu aikata laifi, sai mu ci gaba da addu’a Allah Ya taushi zukatan wadannan miyagun mutane su canja tunani.” A duba jaridar The Nation ta ranar 27 ga Afrilun 2014.
To idan masu wannan magana dattawa ne yaya za su ce a ba Fulani dajin Sambisa in ya zamo tilas ne su yi kiwo? Shin suna nufin Fulani makiyaya ba su da hurumi ko wani yanki na kasa ne a sauran sassan kasar nan?
Ya kamata wadannan ’yan siyasa da suka kira kansu ‘dattawan’ Kiristoci su fahimci cewa babu wani mutum da ya tsiro a kasa a inda yake yanzu, balle ya ce shi kadai ne mai wurin. Ya kamata su lura cewa ko a inda suke din tsirran da suke wurin sun bambanta, Allah Mahaliccin komai da kowa bai yi nau’in tsiro daya a wurin ba. Don haka kamar yadda ya yi tsirrai daban-daban, haka Ya yi mutane daban-daban. Koda kabilar Kuteb ko Jukun aka halitta a wurin su kadai, Allah ba zai daidaita tunani da fahimtarsu ba, Allah bai niyyar Ya halicci wata kabila ko al’umma da fahimta daya ba, ko ’ya’ya ka haifa, sai Allah Ya nuna maka ikonSa cewa sun bambanta a tunani da hankali da ilimi da fahimta da son zaman lafiya ko akasin haka. Don haka rikici magance shi ake yi, shi ne shugabanci shi ne dattaku ba wai a ruruta shi ba.
Domin haka, lokaci ya yi da ’yan siyasar da suka rasa tagomashi za su daina yin kalaman tunzura jama’a. ’Yan siyasa su daina wasa da rayuwar jama’a, domin neman mulki ba hauka ba ne. Rayuwar mutane ta fi duk wani mukamin muli da wani zai samu.
Su kuma talakwa Musulmi da Kirista da suka fito daga kabilu daban-daban su daina yarda ’yan siyasa suna gwara kansu suna kashe juna ko lalata duniyar juna domin biyan bukatun wadansu.
Lokaci ya yi da ’yan siyasa za su daina fakewa da addini da kabilanci suna kokarin tayar da zaune-tsaye a kasar nan.
Kalaman ‘dattawan’ girin ya nuna akwai alamar tambaya kan anya Boko Haram ba wani shiri ne na karya Arewa da Musulmi ba, inda aka fake da amfani da salon ‘da dan gari akan ci gari?’
Talakawan Arewa ku tuna wadanda suke ingiza ku kuna kashe kawunanku, su ne suka mulke ku a baya, ko tambaye su, mai suka shirya domin ci gaban ’ya’yanku da jikokinku?
Wadancan ’yan siyasa da suke kiran kansu ‘dattawa’ sun saye Najeriya tuntuni sun mallake dukiyar da zuriyarsu ma ba ta iya cinyewa balle su, don haka mu yi hattara!