Datti Baba-Ahmed ya yanki katin jam’iyyar PRP

Ya zargi APC da mayar da hankali wajen gurgunta jam’iyyun adawa maimakon magance matsalolin tsaro da tattalin arziki.

Datti Baba-Ahmed ya yanki katin jam’iyyar PRP

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a Zaɓen 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PRP, inda ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar a Zaria.

Baba-Ahmed, tare da wasu abokansa na siyasa sun sanya hannu a rijistar mambobin jam’iyyar a sakatariyar PRP da ke Tudun Wada a ranar Laraba.

Da yake jawabi bayan kammala rajistar, ya zargi jam’iyya mai mulki APC, da mayar da hankali wajen gurgunta jam’iyyun adawa maimakon magance matsalolin tsaro da tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.

Ya ce jam’iyyun adawa da dama, ciki har da LP, sun fuskanci koma baya sakamakon wannan yanayi.

“Sun yi nasarar nakasa jam’iyyun adawa, har da tsohuwar jam’iyyata,” in ji shi.

Sai dai ya bayyana cewa PRP ita kadai ce jam’iyya mai inganci da za ta iya ƙalubalantar APC.

“Idan ana magana kan sahihiyar jam’iyyar adawa da za ta iya ƙalubalantar APC tare da maye gurbinta, to jam’iyyar PRP ce mafita,” in ji shi.

Baba-Ahmed ya kuma bayyana cewa PDP na fuskantar koma baya, yayin da ya nuna rashin tabbas kan makomar wasu jam’iyyu kamar ADC da SDP.

Ya kuma ƙara da zargin cewa akwai yunƙurin da ake yi da gangan domin tarwatsa jam’iyyar Labour, lamarin da ya ce ya taimaka wajen yanke shawarar ficewarsa daga jam’iyyar.

Tsohon jigon na LP ya bayyana ƙwarin gwiwa ga shugabancin PRP, yana mai cewa shugabanninta abin dogaro ne kuma ba sa cin hanci, tare da hasashen cewa ’yan Najeriya da dama za su shiga jam’iyyar cikin watanni masu zuwa.

Ya kuma ce sauya sheƙarsa ya riga ya fara jawo hankalin jama’a a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Datti Baba Ahmed, wanda ƙani ne ga shugaban jam’iyyar na ƙasa, Alhaji Hakeem Baba Ahmed, kuma tsohon mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, kuma jigo a ƙungiyar Dattawan Arewa ACF.