Dattijan Yarbawa sun yi taron sake fasalin Najeriya

Dattijai masu fada aji da masana da kungiyoyin Yarabawa zalla sun yi babban taro a Ibadan, a inda suka tattauna a kan batun sake fasalin Najeriya, inda sakamakon bayan taron ya nuna matsayin kabilun Yarbawa da suka amince da sake fasalin kasar nan da zai mayar da Najeriya komawa ga tsohon tsarin jihohi 4 masu […]

Dattijan Yarbawa sun yi taron sake fasalin Najeriya

Dattijai masu fada aji da masana da kungiyoyin Yarabawa zalla sun yi babban taro a Ibadan, a inda suka tattauna a kan batun sake fasalin Najeriya, inda sakamakon bayan taron ya nuna matsayin kabilun Yarbawa da suka amince da sake fasalin kasar nan da zai mayar da Najeriya komawa ga tsohon tsarin jihohi 4 masu cin gashin kansu kamar yadda tsarin mulki na 1960 da 1963 ya tanadar.

Babban lauya, Afe Babalola da Dakta Kunle Olajide su ne suka sanya hannu a cikin takardar sakamakon bayan taron mai kunshe da bayanai 16 na matsayin Yarbawa a kan wannan batu. Kakakin kungiyar Afenifere, Mista Yinka Odumakin shi ne ya karanta sakamakon ga mahalarta taron.

Taron na Ibadan ya ce idan aka koma ga tsohon tsari mai shiyyoyi 4, wajibi ne a kyale kowace shiyya ta ci gashin kanta ta fannin tsara kundin tsarin mulki na kashin kanta da tara kudaden da take samu domin gudanar da ayyukan ci gaba a yankinta. Sun nuna rashin amincewa da kasancewar gwamnatin tsakiya da take mamaye komai a hannunta.

An gudanar da taron ne a filin wasa na Lekan Salami a karkashin shugabancin babban lauya Afe Babalola (SAN). Taron ya samu halartar Ooni na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi wanda ya nemi taron ya yi dogon tunani da yin taka-tsan-tsan da tabbatar da hada kan jama’a da kwatanta gaskiya da tsoma matasa a dukkan abubuwan da taron yake bukatar tattaunawa. Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya halarci wajen taron amma sauran takwarorinsa na jihohin Legas da Ogun da Oyo da Osun da Ondo ba su samu halarta ba sai dai sun aika da wakilai.

A daidai lokacin da ake cikin yin taron ne wani hargitsi ya barke a tsakanin bangarori biyu na ’yan bangar kungiyar OPC da suka kaure da fada a harabar shiga zauren taron wanda ’yan sanda suka hanzarta tarwatsa su kafin ya kai ga kazancewa.