Dattijo ka fi kukan aski

Janar Muhammadu Buhari ya nemi a tsawata wa wasu kafafen yada labarai saboda irin cin mutuncin da suke yi wa jama’a da sunan yakin neman zabe, musamman ma a gidan talbijin na kasa baki daya, watau NTA wanda ya zake wajen fifita aikace-aikacen jam’iyyar PDP da kuma na dan takararta a labarai da kuma sauran […]

Dattijo ka fi kukan aski
Dattijo ka fi kukan aski

Janar Muhammadu Buhari ya nemi a tsawata wa wasu kafafen yada labarai saboda irin cin mutuncin da suke yi wa jama’a da sunan yakin neman zabe, musamman ma a gidan talbijin na kasa baki daya, watau NTA wanda ya zake wajen fifita aikace-aikacen jam’iyyar PDP da kuma na dan takararta a labarai da kuma sauran shirye-shirye. Haka nan kuma gidan talbijin na African Independent Telebision, AIT shi ma yana wuce gona da iri wajen dakile bayanai game da dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar All Progressibe Congress, APC Janar Muhammadu Buhari da kuma jirkita dukkan bayanan da aka tabbatar za su yi masa tasiri a fafutukarsa na neman kwace mulki daga hannun Shugaba Jonathan.

Wannan ne ya sa wadancan kafafen yada labarai suka nuna wani shiri don cin fuskar Janar Muhammadu Buhari, abin da kowa da kowa ya tabbatar cewa an yi haka ne da gangan don a muzanta shi, a kuma bakanta shi, sa’annan a nuna cewa bai cancanci shugabancin jama’a ba balle jan ragamar wannan kasa. Sa’ilin da aka yi haka hukumar kula da kafafen yada labarai ta NBC, wacce ke karkashin gwamnatin Jonathan ba ta ce ko uffan ba, alhali kuwa a kullum sai ta rubuta takardar gargadi ga wasu kafafen yada labarai da ta raina.
Ana cikin haka ne sai ga shi nan jam’iyyar APC ta ce ba za ta amince dan takararta na shugabancin kasar nan ba ya halarci wata muhawara tare da sauran ‘yan takarar shugabancin kasa na wasu jam’iyyun, wacce wani kwamitin da ya kunshi shugabannin manyan kafafen yada labarai na kasar nan da kuma wasu kungiyoyi daban-daban ke shiryawa a kowace shekara. Dalilinta kuwa na yin haka shi ne daga cikin wakilan wancan kwamitin akwai shugabannin wasu kafafen yada labarai da suka fito firi-falo, suna nuna adawarsu muraran da Janar Muhammadu Buhari, kuma ta samu labarin cewa an kammala shirin tozarta shi da kuma ci masa mutunci idan har ya halarci muhawarar. Hakan kuma ya biyo bayan irin cin kashi da kuma yadda ‘ya’yan jam’iyyar PDP da wasu jaridun kasar nan masu goyon bayanta ke yi wa Janar Buhari, kuma babu wanda ya ce ta tafasa, a sauke.
Ko da wakilan wancan kwamitin muhawarar suka tashi nuna rashin jin dadinsu game da matsayar jam’iyyar APC dangane da muhawarar, ba su ma nuna cewa sun ji takaicin irin cin mutuncin da aka yi wa Janar Muhammadu Buhari ba a cikin waccan shirin da hukumar NTA da AIT suka bari aka yi ta gwadawa a tashoshinsu ba, balle su ba shi hakuri game da haka, domin da aka nuna a tashoshin talbijin din guda biyu ya karya dukkan dokokin yada labarai da kuma na kare hakkin dan Adam. Su bukatarsu ita ce a ci gaba da yin muhawarar, kuma ko an ci ma Janar Buhari mutunci sakamakon haka ba abin damuwa ne ba, domin da ma ba su dauke shi a bakin komai ba. Amma sai ga shi nan an dauki wannan maganar ta kin yarda a wulakanta Janar Buhari a wajen muhawara kamar an saba wa Mahalicci. Irin wannan muhawarar dai ba yau aka fara ta ba, kuma Janar Buhari ya sha halartar wadanda aka yi a baya, saboda haka nan idan an fahimci cewa za a karya masa irli muddin ya halarta a wannan karon, me zai kai shi, a wulakanta shi a banza? Ai ko a lokutan baya ma wasu shugabannin da ke rike da ragamar mulki sun kekasa kasa, sun ki halartar muhawarar, sama da kasa ba su hade ba.
Shi dai Janar Muhammadu Buhari dankali ne sha-kushe, ana cin moriyarsa, ana kuma tozarta shi. Idan har bai halarci waccan muhawarar da ake ta kwanzartawa ba, ba za ta yi wani armashi ba, amma an san da haka, aka kuma ki lallashinsa, don dai kawai a nuna masa iyakarsa. To ya gane wayon, ya kiya, ala bar shi a kai kasuwa. Ba ga wannan al’amarin ne ba kadai ake cin moriyar ganga, a yar da kwaurenta ba. Mutane da yawa sun sha neman kwance wa Janar Buhari zani a kasuwa, don su wulakanta shi, amma sai kaikayi ya yi ta komawa kan mashekiya.
A cikin ‘yan siyasar Najeriya kaf, na dauri da kuma na yanzu, babu wanda na hannun damansa suka caccaka masa wuka a baya kaman Janar Muhammadu Buhari, amma da yake bai kulawa da su, ya bar su da Allah, babu tabo ko guda a jikinsa, su kuma wadanda suka yi masa haka, ya bar su da halinsu, alhakinsa kuma yana nan yana ta bin su, kamar dan kwikwiyo.
Abin mamaki game da haka shi ne duk wadanda suka yi masa tujara, suka juya masa baya don son abin duniya, duk sun komo gare shi, ana tafiya tare, bayan sun gano kura-kurensu. Dalili kuwa shi ne Janar Buhari bai taba yi musu ramuwar gayya ba, bai kuma taba yin mummunan furuci game da kowannensu ba, haka nan ya hadiye bakin cikin da suka yi ta gunza masa, saboda dai ba domin tuwo kadai aka yi masa ciki ba. Wannan ita ce alama ta dattijantaka, ba kamar irin Shugaba Goodluck Jonathan ba, wanda ya bi tsohon ministansa, Labaran Maku har unguwarsu, a Jihar Neja, ya wanke masa hannu akai, don ya kaurace masa saboda abin da ya kira rashin adalcin da aka gwada masa da kuma rashin godiyar da aka nuna masa sa’ilin da yake ta tafutukar kare Jonathan, walau yana da gaskiya ko kuma idan ya kama hanyar karya da ta bata. Ta ko idan aka dubi halayyar Janar Buhari sai a tabbatar ya yi kama da rago wanda ake cewa bai kuka ko da ranar yankansa ne, domin kuwa ko da aka nemi a halaka shi a ‘yan watannin baya, a Kaduna bai nuna yatsan zargi ga kowa ba, ya bar ma Allah ne al’amarin. Ba shakka Janar Buhari dattijo ne wanda ya fi kukan aski.