Dattijon ƙasa Muhammad Jibo ya rasu

Marigayin ya rasu bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Dattijon ƙasa Muhammad Jibo ya rasu

Allah Ya yi wa ɗaya daga cikin dattijan ƙasar nan, Alhaji Muhammad Jibo, rasuwa.

Ya rasu ne a ranar Laraba sakamakon rashin lafiya a gidansa da ke tudun wada, Zariya, a Jihar Kaduna.

Ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya 10 da jikoki da dama.

Daga cikin ’ya’yansa akwai marigayi Yusuf Jibo, ƙwararren ɗan jarida da ya yi aiki da Hukumar Gidan Talabijin ta Ƙasa (NTA), da kuma gidan talabijin na CNN.

Daga baya ya zama Shugaban Hukumar Yaɗa Labarai ta Jihar Kaduna (KSMC).

Marigayin ya kasance shugaban dattijai na Tudun Wada, a Zariya.

Marigayin tsohon gogaggen ma’aikacin gwamnati ne da ya yi aiki da hukumar jiragen ƙasa ta ƙasa da Gwamnatin Arewancin Nijeriya.

Har wa yau, ya yi aiki a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sannan ya zama babban kwamishina a hukumar EFCC.

Alhaji Jibo, ya kuma samun lambar yabo daga Gwamnatin Tarayya ta MFR.

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

An haramta wa ma’aikatan Asibitin Tarayya yin ‘kirifto’ a wurin aiki