Dattijon da ya shekara 55 na sayar da jarida ya rasu

Allah Ya yi wa Shugaban Masu Sayar da jaridu na Lardin Zazzau, kuma wanda ya shafe shekara 55 yana sana’ar sayar da jarida Alhaji Saleh Umaru rasuwa. Da yake jawabi kan rasuwar, Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi. Farfesan ya bayyana haka ne lokacin da ya kai […]

Dattijon da ya shekara 55 na sayar da jarida ya rasu

Marigayi Alhaji Saleh Umaru

Allah Ya yi wa Shugaban Masu Sayar da jaridu na Lardin Zazzau, kuma wanda ya shafe shekara 55 yana sana’ar sayar da jarida Alhaji Saleh Umaru rasuwa.

Da yake jawabi kan rasuwar, Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi.

Farfesan ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar ta’aziya ga iyalan marigayin a gidansa a Zariya.

Farfesa Ango ya ce tsawon shekara 50 suna tare da marigayin sanadiyar sayar da jarida domin shi ke kawo masa jarida a ofishinsa da kuma gida a kowace rana. Ya ce Alhaji Saleh Umaru mutum ne mai amana, sai ya yi fatar Allah Ya gafarta masa.

Abokin harkar marigayin, Malam Sama’ila Ibrahim wanda aka fi sani da Malam Bawa da ke sayar da jarida a Gidan man Total da ke PZ ya ce sun shafe tsawon shekara 49 suna  sayar da jarida tun ana sayar da jarida kwabo biyu, inda ya ce saboda nagarta da amanar marigayin suka zabe shi a matsayin shugabansu. Sai ya yi fatar Allah Ya gafarta wa marigayin.

Marigayin ya rasu a ranar Alhamis din makon jiya bayan gajerira jinya, ya rasu yana da shekara 80 kuma ya bar mata biyu da ’ya’ya 14 da jikoki 69. An yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musunlunci ya tanada.