Dattijon da ya zana tutar Najeriya ya makance

Dattijo Pa Taiwo Akinkunmi, mai shekaru 77, wanda ya zana tutar Najeriya a shekarar 1959, ya samu lalurar ciwon makanta. Pa Taiwo ya ziyarci majalisar dokoki ta Jihar Oyo ne a makon jiya, inda wakilan majalisar suka amince da taimaka masa da Naira dubu dari biyu da hamsin (N250,000) domin saukake wadansu daga cikin matsalolinsa. […]

Dattijon da ya zana tutar Najeriya ya makance

nShugabar majalisar dokoki ta Jihar Oyo, Hajiya Monsurat Sunmonu ce nan daga hagu tare da Pa Taiwo Akinkunmi da Barrister Ishola Bankole (na farko daga dama) da shugaban wakilai masu rinjaye, Mista Oyeniyi Oyeniran, suna riqe da tutar Najeriya a lokacin da Pa Akinkunmi ya ziyarci zauren majalisar a Ibadan.Dattijo Pa Taiwo Akinkunmi, mai shekaru 77, wanda ya zana tutar Najeriya a shekarar 1959, ya samu lalurar ciwon makanta.
Pa Taiwo ya ziyarci majalisar dokoki ta Jihar Oyo ne a makon jiya, inda wakilan majalisar suka amince da taimaka masa da Naira dubu dari biyu da hamsin (N250,000) domin saukake wadansu daga cikin matsalolinsa.
Bayan tallafin, majalisar ta nemi gwamnatin Abiola Ajimobi ta hanzarta taimaka  masa, musamman dangane da irin halin kunci da yake ciki. Ta ce ya kamata gwamnatin ta yi wani muhimmin abu kan Pa Taiwo da za a rika tunawa da shi a kan aikin da ya yi wa kasar haihuwarsa.
Haka nan majalisar ta nemi gwamnati ta gyara hanyar da ta isa gidan Pa Akinkunmi, mai nisan mita 20 daga babbar hanya. Honorabul Ibrahim Bolomope, wanda ya gabatar da shawarar ya ce, majalisar da ta shude ce ma ta fara tattaunawa kan taimaka wa dattijon, sai dai ba ta iya cimma burinta a lokacinta ba, saboda haka ya kamata wannan majalisa ta aiwatar da dukkan abin da ya kamata ga Pa Akinkunmi.

…Wani beben dattijo kuma ya rataye kansa

Kabir Yayo Ali, Daga Ibadan

Wani bebe, mai shekaru 58 mai suna Yemi Michael, ya rataye kansa a cikin gidansa da ke a unguwar Oremeji-Agugu, a Ibadan.
Wannan al’amarin ya bayyana ne da misalin karfe 9 da rabi na ranar Talatar makon jiya, a lokacin da daya daga cikin ’ya’yansa mai shekaru 16, mai suna Lekan Michael, ya gano gawar mahaifin nasa a rataye a cikin dakinsa, ya sanar da makwabta.
Wani makwabcin marigayi Yemi, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Ba shi da wata alamar damuwa, domin a kowace rana muna zaman hira da shi duk da babe ne amma, a wannan ranar har wasan ‘draft’ muka yi da shi. Daga baya muka samu danyen labarin mai ban mamaki da damuwa.”
Sai dai, bayanan da suka fito daga bakin dan nasa Lekan, sun nuna cewa, baban nasa ya sha fada masa yana so ya kashe kansa. Da yake yi wa ’yan jarida bayani, Lekan ya ce, “Ko a jiya Talata, mahaifina ya umarce ni da samo masa wani abu da zai yi amfani da shi wajen kashe kansa, amma na shaida masa ba zan iya ba. Hasali ma sai na fice daga dakin, domin ba ranar ce ya fara yi mini irin wannan magana ba. Ba dade ba, na koma kamar yadda na saba, don jin ko yana da bukatar wani abu kafin ya kwanta barci, sai na taras da gawarsa tana rataye.”
Marigayi Yemi bai tare da mata, sai mahaifiyarsa da dan nasa a cikin gidan nasu da yae na gado. Wata kanwar marigayin ta hana ’yan jarida zantawa da mahaifiyar tasu.
A yayin da wakilinmu ya tuntubi rundunar ’yan sandan Jihar Oyo, sun ce ba su samu rahoto dangane da wannan al’amari ba.