Dattijon Neja Delta Edwin Clark ya rasu

Cif Edwin Clark ya rasu yana da shekaru 97 a duniya

Dattijon Neja Delta Edwin Clark ya rasu

Jagoran al’umar yankin Neja Delta, Cif Edwin Clark ya rasu yana da shekaru 97 a duniya.

Marigayin wanda tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Tarayya ya rasu ne a cikin daren ranar Litinin, 17 ga watan nan na Fabrairu, 2025.

Kafin rasuwarsa, shi ne Shugaban Kungiyar Gamayyar Al’ummar YankiN Neje Delta (PANDEF)

Iyalan Cif Edwin Clark sun sanar da rasuwar tasa ce ta wanta sanarwa a safiyar Talata.