Dattijuwa mai shekara 60 ta kashe kanta
An tsinci gawarta rataye a bishiya bayan kwana biyu ana neman ta
Wata dattijuwa mai shekara 60 ta kashe kashe kanta inda aka tsinci gawarta a rataye tana lilo a jikin wata bishiya.
An tsinci gawarar tsohuwar ce a safiyar Alhamis bayan ta bar gida tun ranar Talata cewa za ta je gona amma ba ta koma gida ba.
- Gobara ta tashi a masana’antar rigakafin COVID-19
- An cafke jami’in tsaron ABU da ke hada baki ana garkuwa da mutane
- Abubuwan da ke raba tsakanin masoya
‘Yadda muke shiga kunci yayin zaman zawarci’
Rashin komawarta ya sa aka bazama neman ta, inda aka tsinci gawarta a safiyar ranar Alhamis rataye a jikin reshen bishiya.
Shaidu sun ce an iske jakar kayan zuwa gonan tsohuwar a kusa da bishiyar da ake zargin ta rataye kanta.
Sai dai mazauna sun bayyana shakkunsu, kasancewar inda aka tsinci gawar na da nisa bayan an wuce gonar dattijuawa.
Haka ya sa ake zarkin kashe tsohuwar aka yi aka dauke gawarta zuwa inda aka rataye ta a jikin bishiyar domin batar da sawu.
Wani mazaunin unguwar ya ce, “Ban yarda ita ce ta kashe kanta ba. Igiyar ta yi gajarta kuma kafafunta sun yi kusa da kasa; Na fi zargin kashe ta aka yi aka je aka rataye gawar a bishiyar.”
Bayan faruwar lamarin a unguwar Amachai da ke garin Okpanam, Karamar Hukuamr Oshimili ta Arewa da ke Jihar Delta, an dauke gawar dattijuwar zuwa wani dakin ajiyar gawa a wani Asibiti.