Dattijuwa za ta kammala karatun digiri bayan shekara 64
Wata dattijuwa mai shekara 84 a kasar Turkiyya za ta kammala karatun digirinta a bana, bayan shafe shekara 64 da farawa a wata jami’a da ke birnin Istanbul, babban birnin kasar, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana. Dattijuwar mai suna Fatma Mihriban Aktari ta fara shiga Jami’ar Mimar Sinan ne a shekarar […]
Wata dattijuwa mai shekara 84 a kasar Turkiyya za ta kammala karatun digirinta a bana, bayan shafe shekara 64 da farawa a wata jami’a da ke birnin Istanbul, babban birnin kasar, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
Dattijuwar mai suna Fatma Mihriban Aktari ta fara shiga Jami’ar Mimar Sinan ne a shekarar 1951, an kore ta daga makarantar saboda yadda ta hada karatu da aiki a wani kamfani. A lokacin ta kasance marainiya kuma tana amfani da albashin da ta samu daga aikin wajen taimakon kanta da na mahaifiyarta. Yayin da ta kara komawa makarantar bayan shekara 60.
Fatma ta ce ta samu kwarin gwiwar koma wa makaranta ne domin karasa digirinta na fannin zane-zane (Fine Art) ne bayan da a shekarar 2011, gwamnatin kasar ta bayyana komar da duk wani da aka kora daga jami’ar domin ya samu damar kammala karatunsa.
Kuma duk da watsi da ta yi da takardun da ke nuna shaidar ta yi jami’ar a shekarun baya, hukumomin jami’ar taimaka mata wajen nemo sauran takardun da ke tabbatar da kasancewarta daliba a jami’ar.
Dattijuwar ta ce: “Na rasa inda zan sanya kaina saboda farin ciki lokacin da na samun labarin cewa an kara daukana a jami’ar.” Za ta dai kammala karatun ne a kakar bana.