Dauda Lawal ya gwangwaje ma’aikatan Zamfara da albashin wata guda

Gwamnan Zamfara ya ba wa ma’aikatan jihar da na kananan hukumomi albashinsu wata guda a matsayin kyautar karshen shekara.

Dauda Lawal ya gwangwaje ma’aikatan Zamfara da albashin wata guda

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ba da umarnin biyan ma’aikatan gwamnatin jihar da na kananan hukumomi albashinsu wata guda a matsayin kyautar karshen shekara.

A ranar Juma’a Gwamna Lawal ya umarci ma’aikatar kudin jihar ta biya alawus din da ake kira 13th Month ba tare da bata lokaci ba.

Shugaban ma’aikatan jihar, Ahmed Liman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Karo na farko ke nan da ma’aikatan Zamfara za su shaida irin wannan tagomashi, a cewar kakakin gwamnan, Sulaiman Idris.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito shi Sulaiman Idris na cewa gwamnan “ya amince da biyan ma’aikatan jihar da na kananan hukumomi alawus-alawus na karshen shekara ne da nufin kara musu kwarin gwiwa da kuma ba su tallafin kudi a lokacin hutu.

“Wannan matakin shaida ne kan muradinsa na aiwatar da tsare-tsare da za su inganta yanayin aiki, kara albashi, da samar da damar ci gaban sana’o’i ga ma’aikatan gwamnati.

“Biyan albashin 13th Month  daya ne daga cikin tsare-tsarensa na karfafa gwiwar ma’aikata da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar Zamfara.

’Yan Bindiga: An miƙa wa gwamnatin Kaduna mutum 58 da aka ceto

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna

Barikin Ladi: Asalin garin da yanayin rayuwar mazauna