‘Dauda mai cin zali’
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Tare da fatan kuna cikin qoshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Dauda mai cin zali ne.’ Labarin ya qunshi yadda cin zali ke sanya mutum fadawa cikin mummunan hali. A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi Dauda ya kasance mai cin zali a makarantarsu. Don haka yara da […]
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Tare da fatan kuna cikin qoshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Dauda mai cin zali ne.’ Labarin ya qunshi yadda cin zali ke sanya mutum fadawa cikin mummunan hali. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Dauda ya kasance mai cin zali a makarantarsu. Don haka yara da dama ke tsoronsa kuma duk abin da yake so dole yaran makarantar su ba shi.
Akwai wata yarinya A’isha duk makarantar ba wanda ya kai ta ilimi. Ga shi kuma ajinsu daya da Dauda.
Ran nan malaminsu ya ba su aiki su yi a gida. Kamar kullum A’isha ta kammala nata ta kawo makaranta washegari. Da Dauda ya hango ta sai ya karbe takardarta kuma ya kwafe duk abin da ta yi kafin su miqa wa malaminsu.
Da Malamin ya lura abin da suka rubuta ya zo daya sai ya kira A’isha da Dauda don ya tuhume su. Malamn ya tambaye su wane ne a cikinsu ya kwafi na wani?
Ita kuma A’isha saboda tsoro sai ta nuna ita ta kwafi na Dauda. Daga nan sai Malamin ya sake ba su sababbin takarda inda ya umarci kowa ya sake rubuta amsar a gabansa.
Nan take Malamin ya gano cewa Dauda ne ya yi qarya kuma ya sa aka yi masa bulala goma daga nan ya sanar da iyayen Dauda halin da dansu yake ciki.
A gida iyayen Dauda suka sake zane shi, kuma suka yi masa gargadi ya mayar da hankali wajen yin karatu.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi daga wannan labari.