Daukar doka a hannu: An kashe mutum 73, an raunata 31 a shekara daya
Jihohin Legas da Bayelsa da Birnin Tarayya, Abuja da Kuros Riba ne kan gaba wajen masu daukar doka a hannu, yayin da aka kama wadanda ake zargi da aikata laifi. Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa akalla mutum 105 suka gamu da fushin masu daukar doka a hannu a jihohi 25 cikin 36 […]
Jihohin Legas da Bayelsa da Birnin Tarayya, Abuja da Kuros Riba ne kan gaba wajen masu daukar doka a hannu, yayin da aka kama wadanda ake zargi da aikata laifi.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa akalla mutum 105 suka gamu da fushin masu daukar doka a hannu a jihohi 25 cikin 36 da ake da su a Najeriya daga watan Janairu zuwa Disamban bara.
Bincike ya tabbatar da cewa hatta Birnin Tarayya Abuja bai kubuta daga ta’asar daukar doka a hannu ba. Yawan mutanen da aka kashe ko aka raunata ya kunshi wadanda gidajen jaridu suka bada rahotonsu ne kwai, akwai daruruwa wadanda ba a bada rahoton su ba a sassan Najeriya.
Yawan daukar doka a hannu da ake yi a Najeriya na jawo shakku kan ’yancin dan Adam da tsarin mulkin Najeriya ya fayyace a sashi na 33 (1). Dokar ta ce: “Dukkan dan kasa yana da ’yancin rayuwa sannan ba wanda za a jefa rayuwarsa cikin hadari, ko tseratar da shi daga hukuncin kisa da wata kotu ta yanke masa wanda aka same shi da aikata babban laifi a Najeriya.”
Wani nazari da Aminiya ta yi ya gano cewa yawan mutanen da suka fada hannun ’yan daba ko masu daukar doka a hannu a bara, ya hada da mutum 73 da aka kashe da mutum 31 da suka samu munanan raunuka ta hanyar lakada musu duka.
Mutanen da suka hadu da fushin masu yanke wa kansu hukuncin sun hada da wadanda ana zargi da fashi da makami ko garkuwa da mutane da sauran laifuffukan da ake zarginsu da hakan ke jawo a auka musu da jifa ko banka musu wuta.
In da abin ya fi kamari shi ne Jihar Legas sai Bayelsa sannan Abuja take biye sai Kuros Riba da Binuwai sai Jihar Delta. Ragowar jihohin da ake samun yawaitar daukar doka a hannu da ke kaiwa ga asarar rayuka sun hada da Anambra da Ondo da Katsina da Ekiti da Edo da Enugu da Abiya da Kwara da Oyo da kuma Nasarawa.
Akwai kuma jihohin Ebonyi da Zamfara da Kaduna da Imo da Akwa Ibom da Kogi da Neja da Ogun da Filato.
Wadanda hadarin ya fi shafa su ne jami’an tsaro da sababbin shiga fashi da makami da masu ’yan luwadi da masu satar shanu.
Daya daga cikin ayyukan wadannan ’yan dabar ko masu daukar doka a hannu da ya fi ban mamaki shi ne wanda ya faru a Jihar Legas a watan Afrilun bara, inda aka kama wani matashi da ake zargi da damfara ta Intanet ‘Yahoo Boy’ aka yi masa dukan kawo wuka aka yi masa tsirara.
Wani da ake zargi da tsafi kuma an auka masa ba tare da ba shi dama ya kare kansa ba, matashin an yi masa dukan tsiya sannan aka yi masa zigidir kamar yadda lamarin ya kewaya a shafukan sada zumunta.
Sannan wani abin takaici shi ne daukar doka da wadansu matasa suka yi a wani kauye da ke Karamar Hukumar Yala a Jihar Kuros Riba a ranar 29 ga Mayun bara, inda suka binne wani matashi da ransa saboda zarginsa da kisan dan uwansa. Mutumin an ce an binne shi tare da gawar dan uwan.
Nazarin da Aminya ta yi ta kuma gano cewa wani matashi da ake zargi da sata a Karamar Hukumar Cele-Ijesha a Jihar Legas mai suna Temitope Adeoye, an banka masa wuta wace ta yi silar mutuwarsa a ranar Litinin 11 ga Fabrairun bara, matashin yana aiki ne a yankin Tin Can Island a tashar jiragen ruwa ta Apapa, yana hanyarsa ta komawa gida ne daga ofis a wannan yammaci ya gamu da ajalinsa.
Kafin mutuwarsa bayan ya sauka a tashar mota ta Cele-Ijesha, yana jiran wata motar da za ta karasa da shi gida, sai kawai ya ji wadansu samari suna ihu barawo-barawo kafin ya yi aune sai suka nuna shi nan da nan mutane suka far masa da duka sannan suka banka masa wuta.
Wani abin takaicin kuma da ya faru shi ne lokacin da wadansu ’yan daba suka kashe wani matashi mai suna Olamide Omolede, mai shekara 22 bisa zarginsa da satar wayar hannu a yankin Badore da ke Karamar Hukumar Ajah a Legas.
Daga cikin batutuwan wadanda daukar hukunci a hannu ya shafa da Aminiya ta yi bincike a kai akwai wani da ake zargin dan fashi da makami ne da ya addabi kauyen Dakwa a Karamar Hukumar Tafa a Jihar Neja wanda jama’a suka kashe ranar 25 ga Janairun 2020.
An zargi mutumin da kwace babur din wani dan acaba a kauyen, sai mutanen kauyen suka ankara da haka suka bi sawunsa cikin gaggawa suka cimma masa; inda suka lakada masa dan karen duka tare da cinna masa wuta.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Mohammad Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce ba su kama kowa ba, sakamakon tserewar gungun jama’ar da suka aikata danyen aikin.
Har ila yau kuma, Aminiya ta yi nazari kan makamancin wannan lamari da ya faru a kauyen Tsambe Tsauni a yankin Mallamawa a Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina, inda ka bayar da rahoton wadansu matasa cike da fushi sun kashe mutum uku bisa zargin suna bayar da bayanan sirri ga barayin mutane.
An sake samun irin wannan hukunci a ranar 29 ga Satumban bara a Abuja, lokacin da gungun jama’a suka kone wadansu da ake zargi masu satar mutane ne a Dutsen Alhaji. Lamarin an ce ya faru ne a karkashin gadar Dutse yayin da aka jiyo wata mata tana kukan a kawo mata dauki lokacin da take cikin wata motar fasinja da ke kan tafiya. Bayanai sun ce an yi gaggawar fizgo ta daga cikin motar tana ihu wanda hakan ya sanya wani mutum cikin motarsa ya sha gaban motar da matar ke ciki, bayan ya lura da lamarinta, inda ya toshe hanyarta a karkashin gadar.
Kafin a ce kwabo, ’yan acaba sun yi wa wurin tsinke, suna zargin mai motar da kasancewa dan gungun barayin nan da ake kira One Chance, sai suka rufe su da duka tare da cinna musu wuta hade da motar suka kone.
Dalilin da daukar doka a hannu ke samun gindin zama a Najeriya –Masana
Wadansu masana shari’a da tsaro sun bayyana dalilan da daukar doka a hannu ke neman zama yayi a Najeriya. Olalekan Ojo (SAN) wani babban lauya ne da ya tsaya wa manyan shari’o’i da dama, ciki har da shari’ar da ta yi suna ta Chukwuemeka Ezeugo (Rabaran King). Ya ce babu kan cewa akwai batutuwan daukar doka a hannu masu yawa a Najeriya. “Idan ka dubi abin ta fuskar zamantakewa, ba abu ne da za a lamunta ba, saboda babu wani mahaluki da yake da ikon daukar ran dan uwansa, sai dai shari’a,” inji shi.
Da aka tambaye shi me ya sa daukar doka a hannuke karuwa kamar wutar daji, sai ya ce: “Hakan na nuni ne da cewa a wasu wurare mutane ba su da kwarin gwiwa kan yadda ake tafiyar da shari’o’in da suka shafi aikata danyen aiki a kasar nan.”
Ya kara da cewa, “Akwai kararraki masu yawa da ko dai ba a gabatar da su gaban kotu yadda ya dace ba ko ma ba a gabatar da su ba kwata-kwata, saboda dalilan rashin isassun shaidu da makamantansu.
Don haka sai ka ga mutanen da ya kamata a ce kotu ta yanke musu hukuncin kisa an zartar da shi, amma suna ta yawo, saboda an sake su bayan da suka shafe shekara uku zuwa hudu a gidan yari saboda kawai babu kwararan hujjojin yi musu shari’a.”
Sa’annan ya ce a irin wannan sai a tarar mutumin ya sake komawa ruwa, wanda hakan zai jawo mutane su yi tunanin daukar mataki da kansu, wanda aikata haka ma laifi ne.
Dangane da rawar da lauyoyi ya kamata su taka kuwa, Ojo ya ce, rashin yin komai daga gare su bai ci karo da shari’a ba, sai dai ba dabi’a ce mai kyau ba lauyoyi su ki karbar hanzarin wadanda ake zargi domin jin ta bakinsu, koda kuwa al’umma ta riga ta shafa musu bakin fenti. “Kuma babu wani mahalukin da yake da ikon ayyana wane a matsayin mai laifi. Domin za a iya samu a wasu lokutan wanda aka zarga da aikata laifi; ko dai yana da tabin hankali ko ya aikata a matakin abin da ya yi amanna na kare kai ne. Idan doka ta ce ta wanke wane daga laifi kaza; to akwai lauyan da ya isa ya ce ai mai laifi ne shi?,” inji shi.
Game da ko gwamnoni na jan kafa wajen zartar da hukuncin kisa kan wadanda aka samu da laifi aka yanke musu hukuncin a kotu, babban lauyan cewa ya yi Sashi na 407 na Dokar Gudanar da Manyan Shari’o’i, ACJA, ya tanadi mafita game da hakan. Ya kawo wata sadara da ta yi bayani dalla-dalla game da batun, inda ya ce, “Takaddar shaidar yanke hukuncin kisa da alkali ya rubuta ita kawai ta wadatar a zartar da hukuncin kisa a kan mai laifin; har sai in an yafe masa ko kuma an sallame shi.”
Martanin ’yan sanda kan yadda lamarin ya zama ruwan dare
’Yan sanda sun maida martani kan zargin cewa dalilan da suke haddasa hakan akwai rashin gabatar da kara yadda ya dace wanda hakan ke haifar da tafiyar hawainiya a shari’ar miyagun laifuffuka, inda daga bisani ke sanya jama’a tunanin daukar doka a hannu.
Babban Jami’in ’Yan sandan a Sashin Shari’a na Rundunar da ke Abuja, CSP James Idachaba, ya ce matsala ce mai fuskoki uku; ba ta ta’allaka kan masu shigar da kara kawai ba. Idachaba, wanda ya jagoranci masu shigar da kara a shari’ar Maryam Sanda, ya ce wani lokacin ma bangaren wanda ake kara ne ke kawo tafiyar hawainiya a shari’a ta hanyar gabatar da hanzari na shirme kuma su kansu kotunan kan kawo tsaiko a shari’a sakamakon yadda suka tara kararraki a gabansu.
Ya ce su masu kara na bai wa ’yan sanda ciwon kai wajen gabatar da kara, domin a cewarsa, wani lokacin idan suka nemi bayanai daga masu kara ko kuma mutum ya bayar da shaida gaban kotu sai ka ga mutum yana ta rabe-rabe.
Da aka tuntube shi mece ce matsayar ’yan sanda kan daukar doka a hannu, Kakakin Hedkwatar ’Yan sandan Najeriya DCP Frank Mba, ya ce babban laifi ne aikata haka. “Matsayinmu a fili yake, jama’ar gari za su iya kama wadanda ake zargi sun aikata laifi; sai dai da zarar sun kama lallai ne su mika su ga ’yan sanda. Aikata duk wani abu koma bayan haka ba daidai ba ne a shari’a,” inji shi.
A bangaren Kwamishinan ’Yan sandan Birnin Tarayya, Bala Chiroma, ya ce babu hujjar daukar doka a hannu kuma abin Allah wadai ne; ya ce ya kamata a yi binciken kwakwaf domin gano wanda ya aikata laifi kuma a ina ya aikata domin kauce wa kashe ran da bai ji ba bai gani ba.
Yadda za a shawo kan daukar doka a hannu
Masanin harkar tsaro, Dokta Amaechi Nwaokolo, ya ce idan har za a shawo kan wannan dabi’a to lallai ne a farfado da tsarin shari’ar miyagun laifuffuka ta yadda zai zama yana aiki sosai. Ya ce, akwai bukatar hukumomin da lamarin ya shafa su kara himma wajen wayar wa jama’a kai tare da jan kunnensu su kauce wa daukar doka a hannu. “Domin kauce wa daukar doka a hannu a Najeriya, lallai ne tsarin shari’ar kasar ya farfado da karsashinsa ta yadda masu gabatar da kararraki za su samu kwarin gwiwar kai kokensu. Wajibi ne a sakar wa bangaren shari’a da kuma na tsaro mara su gudanar da ayyukansu yadda ya dace.
“Akwai bukatar hukumomin da lamarin ya shafa kamar Hukumar Wayar da kan Jama’a ta Kasa (NOA), su tashi tsaye wajen nusar da ’yan Najeriya kan su kauce wa daukar doka a hannu; kuma su zamo masu kai kokensu gaban hukumomin da suka dace,” inji Nwaokolo.