Daukar Fansa: Matasa sun binne mutum da ransa
Wasu matasa a kauyen Liokom da ke gundumar Wanihem, yankin karamar hukumar Yala Jihar Kurosriba da suka fusata sun birne wani matashi mai suna Ojemba da ran sa a kabari tare da yayansa mai suna Obok, da ya datse wa kai babu gaira babu dalili. Wannan al’amari ya faru ranar Laraba bayan ’yan kwanaki da […]
Wasu matasa a kauyen Liokom da ke gundumar Wanihem, yankin karamar hukumar Yala Jihar Kurosriba da suka fusata sun birne wani matashi mai suna Ojemba da ran sa a kabari tare da yayansa mai suna Obok, da ya datse wa kai babu gaira babu dalili. Wannan al’amari ya faru ranar Laraba bayan ’yan kwanaki da mutuwar mahaifiyar su yaron Ojemba ya datse kan dan uwan nasa.
Yadda har hakan ya faru kanen ya datse kan yayansa kamar yadda Aminiya ta samu rahoto daga can kauyen saboda haka babu wani rikici ko ’yar hatsaniya da ta hada su shi da dan uwan nasa kuma kanen ya sare wa wansa kai. Lamarin ya fusata ’yan uwa da dangin iyalan hatta matasan kauyen ma abin ya basu takaici.
Wani mazaunin kauyen Liokom, da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidawa wakilin Aminiya cewa, “Ojemba shi ne kanen Obok bayan yayansa wato Obok ya dawo gida daga mujami’a ibada dawowarsa gida keda wuya yana hutawa kafin nan matarsa da gama masa abinci ta bashi yagama cin abincin yana kokarin tafiya gona ciro doya shi da kanin sa wato Ojemba ya karbi adda daga hannun dan uwansa Obok yana wasata bayan ta wasu ta yi kaifi irin yadda ake so sai ya yi kamar zaije ciro doya shima sai ya yi wuf ta baya ya farwa wansa Obok da sara sai da ya yi masa sara biyu da addar, a sara na uku ne bayan ya fadi ya sare masa kai,” in ji majiyar.
Bayan barnar ta faru sai matar Obok ta fara kuka tana ihu. “Zo a kawo mata dauki ga abin da kanen mijinta ya aikata nan da nan jama’a suka cika gidan aka yi sa’ar damke Ojemba.”
Wannan kazamin al’amari kamar yadda majiyar mu ta ci gaba da fada shi ne na farko a wannan karkara. “Sai matasan kauyen suka yanke shawarar gaskiya wannan mugun abu ya yi yawa abin kunya ne ace haka ya faru a kauyen nan matasa su kuma suka taru suka yanke shawarar cewa, dole shima sai ya mutu tare da dan uwansa shi yasa suka kama shi suka cusa shi kabari daya da dan uwansa da ya kashe, sai suka daure hannuwansa da kafafuwan sa suka jefa ramin kabarin dan uwan tare da gawar suka mayar da kasa suka rufe su tare.”
Duk da irin kururuwa da rokon da Ojemba ya rika yi wa, matasan nan da su yi masa ahuwa su yi masa rai suka yi biris da shi suka maka shi rami suka birne. Wakilin mu ya tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kuros Riba, Irene Ugbo ta tababtar da faruwar hakan ta ce, an tura jami’an su domin su binciken abin da ya faru a kauyen.