dauraya kan tsokaci game da hanyar zuwa Aljanna

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinqai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.  Bayan haka, idan mai karatu […]

dauraya kan tsokaci game da hanyar zuwa Aljanna
dauraya kan tsokaci game da hanyar zuwa Aljanna

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinqai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako. 

Bayan haka, idan mai karatu na biye da mu, zai ga a makon da ya wuce mu kai qarshen hanyarmu ta zuwa Aljanna har ma mun je bakin qofa, muna jira kawai a bude mu shiga, to yau za mu yi daurayar abin da muka keto tun makonni goma da suka shige. Muna fata Allah Ya sa mu kasance cikin qarin natsuwa da lura don mu qarfafa himmarmu ta ganin lallai muna kan wannan hanya matuqar rayuwarmu.
Tun farko dai, kamar yadda aka ce, kullum abin da mutum zai yi ta addu’a game da shi, shi ne Allah Ya taimake shi ya rayu a kan Musulunci har iyakar rayuwarsa. Sannan sa’ar da mutuwa za ta zo (masa), ya mutu yana Musulmi, a karbe shi yana mumini. Idan ya je Lahira da wannan matsayi, to duk matsalar da za a samu, insha Allahu mutum zai tsallake (ya tsira). Allah Ya sa mu dace da haka don tsarkin sunayenSa.
Hanyar dai sananna ce ba boye take ba. Sannan ita tafiya a kan hanyar tana da mataki-mataki har guda hudu, wadanda lallai a samu tabbataccen haquri wajen gudanar da ita, mutum sai ya yi ta fata Allah Tabaraka wa Ta’ala Ya ba shi tabbata da daidaito a kanta.
Musulunci dai shi ne tushe, kuma wanda aka aiko shi da shi, shi ne za a yi koyi da shi don a cimma wannan manufa. Duk wanda yake so ya tsira ko wane ne shi, komai matsayinsa da muqaminsa, dole ne sai ya bi tsarin da dan aiken da aka turo da Musuluncin nan ya zayyana. Shi ya sa ma a qarshen daya daga cikin Hadisai biyun da aka gabatar a farko tsokacin da ya gabata, ya ce, “Duk wanda ya yi mini biyayya, ya bi abin da na karantar, ya shiga Aljanna; wanda kuwa ya saba mini, wannan ya ce ba ya son Aljanna kawai kai-tsaye.”
Ita shari’ar Musulunci qa’ida ce wadda aka gina ta a kan abubuwa biyu kacal: (1) Yi don Allah kadai (ba shirka) da (2) Kwaikwayon Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam).
Wannan tafiya da za a yi an jera ta ne ta yadda tana nan tsakanin kalmomi hudu, wadanda za mu riqe, mu qanqame kuma mu lura da su, domin su ne kayan tafiyar, su ne guzuri. Biyu wadanda ake korewa ne, ba a son mu aikata su. Sauran biyun kuma so ake mu yi su, mu riqe su kam-kam, kada mu rabu da su, har mutuwa.
Wadanda ba a so, su ne ‘Shirka (hada Allah da wani a cikin bauta maSa) da sabon Allah (qin bin umurninSa – gaba daya ko yadda ya dace).’
Su kuma wadanda ake son mu riqe mu qanqame su, mu yi ta yi har iyakar rayuwarmu su ne ‘Imani (wanda yake da ginshiqai guda shida) da ayyukan qwarai (wadanda suke da yawan gaske, sai mutum ya yi matuqar qoqari wajen gudanar da wadanda yake iyawa – saura kuma ya bar wa Allah al’amarinSa)!’
Farkon hanyar ita ce – Aqidah – wato ambato da qudurcewar ‘La’ilaha illallah Muhammadur rasulullaah’! (Babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah, Muhammadu Manzon Allah ne). Wannan bangare na aqida in babu shi, to duk ayyuka babu su, ko an yi su, to duk sun lalace. Shirka, idan an yi ta, to komai na aikin ibada ya lalace.
Imanin nan shi ne qudurcewa cewa Mahaliccinmu, Allah Tabarka wa Ta’ala, Shi ne Wanda Ya halicci dukkan halittu gaba daya kuma Yake gudanar da su yadda Ya so (Rububiyyah). Shi ne ke da cancantar a bauta maSa, Shi kadai (Uluhiyyah) kuma Yana da Sifofi Madaukaka da Sunaye Kyawawa (As’ma’u wa Sifaat).
Sannan imani da Manzanni (wato’yan aiken Allah kan yadda za a bauta maSa); sai Littattafan da aka aiko su da su; sai Mala’iku (da aka halitta daga haske, su ba maza ba ne kuma ba mata ba, ba su ci ba su sha, cinsu da shansu shi ne bautar Allah); sai Ranar Lahira (ranar qarshen kowace rayuwar duniya da ta barzahu, yayin da za a yi wa kowa hisabin abin da ya gabatar a nan duniya); sannan sai imani da qaddara ta alheri ko ta sharri!
Lura da wadannan jerin abubuwa guda shida, idan aka dube su za a ga al’amura ne da suka tattaro imani ingantacce. Tsare su shi ne cin rubu’in (kashi daya cikin hudun) tafiya zuwa Aljanna!
Sannan sai ayyuka wato tsare Sallah; ba da Zakkah; azumtar watan Ramadan da kuma gudanar da aikin Hajji.
Daga nan sai gudanar da ayyukan da suka jibinci mu’amala, kamar yi wa iyaye da’a; sadar da zumunta; kyautata maqwabtaka; girmama baqo; girmamawa da kyautata wa ’yan uwa Musulmi. Sannan kuma mu kasance masu yin adalci cikin zantuttukanmu da ayyukanmu na yau da kullum.
Bayan wadannan kuma abin da ya shafi shirka, lallai ne mu tsarkake Allah cikin duk abin da ya gabata din nan na bauta, kada mu ba kowa wani haqqi na Allah, duk yadda al’amari ya juya, muna masu neman taimakon Allah a kan haka. Kada mu kuskura mu yi wani aiki na ibada (bautar Allah) don wanin Allah.
Yin haka da kuma tsarewa shi zai kai mu ga matakin tafiya na tsakiya, wato an ci rabin tafiya zuwa shiga Aljanna.
Sauran sinadaran da za su tallafa mana wajen qarasa tafiyar kuwa sun hada da tsare qwaqwalwa daga mummunan tunani na gudanar da abin da ba shi da kyau. Kunnuwanmu kuma mu tsare su daga jin abubuwan da ba su da kyau da suka jibinci qarya ko batacciyar magana ta cutarwa ko alfasha, ko waqe-waqe na banza da kade-kade ko giba da makamantansu.
Sannan mu kiyaye ganinmu (idanunmu) daga kallon abin da bai halatta mu kalla ba. Bayan nan, mu tsare harshenmu daga magana ta alfasha, ko batsa, ko mummunar magana ta gatse ko dai wata magana mai ban haushi ko qarya, ko zur (mu fadi abin da ba mu gani ba). Ko yin giba (yi da wani) ko hada wani da wani don a saba da sauransu.
Mu kwana nan, sai mako mai zuwa za mu qarasa daurayar, in Allah Ya so. Wassalamu alaikum warahmatullah!