dauraya kan tsokaci game da hanyar zuwa Aljanna (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.  Bayan haka, yau ga karashen […]

dauraya kan tsokaci game da hanyar zuwa Aljanna (2)
dauraya kan tsokaci game da hanyar zuwa Aljanna (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako. 

Bayan haka, yau ga karashen daurayarmu dangane da tsokaci game da hanyar zuwa Aljanna. A makon da ya wuce daurayar ta yi nisa ta yadda kusan ba inda ba a taba ba, sai dan kadan daga cikin sinadaran da ake tanada don gudanar da wannan tafiya da zuwa shiga Aljanna, wadanda suka hada tun daga tushe, wato Musulunci da abin da ya kunsa na hukunce-hukunce.
Muka ce sauran sinadaran da za su tallafa mana wajen karasa tafiya kuwa sun hada da tsare kwakwalwa daga mummunan tunani na gudanar da abin da ba shi da kyau. Kunnuwanmu su ma mu tsare su daga jin abubuwan da ba su da kyau da suka jibinci karya ko batacciyar magana ta cutarwa ko alfasha, ko wake-wake na banza da kade-kade ko giba da makamantansu.
Sannan mu kiyaye ganinmu (idanunmu) daga kallon abin da bai halatta mu kalla ba. Bayan nan, mu tsare harshenmu daga magana ta alfasha ko batsa, ko mummunar magana ta gatse ko dai wata magana mai ban haushi. Ko karya, ko zur (mu fadi ko mu yi shaida kan abin da ba mu ji ko mun gani ba). Ko yin giba (yi da wani) ko hada wani da wani don a saba da sauransu.
Sannan mu tsare cikinmu daga sanya masa abinci ko abin sha da yake haram, ta fuskar cin riba ko cin mushe ko cin alade, ko shan duk abin da ke bugarwa ya fitar da mutum daga hayyacinsa, kamar giya (ko abin da ya yi kama da ita na daga abubuwa masu bugarwa).
Bayan nan, mu tsare farjojinmu daga yin zina. Kada mutum ya kusanci wata matar da ba tashi ta shari’a ba, ko mace ta nemi mijin da ba nata ba.
Sannan mu kiyaye hannayenmu daga cutar da wani, wajen dukan da ba na shari’a ba, ko kisa ko abin da ya yi kama da shi, wanda shari’a ta hana, na daga daukar dukiyar wani (sata), ko coge wajen rubuta abin da yake batacce, ko karya.
Sannan mu tsare kafafuwanmu wajen tafiya da su wurin wasan banza, wanda yake batacce. Kada mu je wajen abin da zai jawo mana wata fitina ko fasadi (barna) ko sharri.
Mu tsare alkawari da shaida da amana. Kada mu warware wani abu da aka kulla da mu na alkawari. Kada mu warware alwashin da muka yi. Kada mu ci amana. Duk abin da aka kulla da mu, to mu cika shi har zuwa karshensa, saboda Allah! Mu tuna cewa babu addini ga wanda ba shi da alkawari kuma babu imani ga wanda ba shi da amana. Wajen shaida kuma kada mu yi shaidar zur (abin da ba mu ji ba, ba mu gani ba, mu ce mun ji mun gani). In an ba mu amana kada mu yi yaudara game da ita, sai dai mu bayar da ita yadda take, yadda ya kamata a cikin mutunci da sanin ya-kamata!
Lallai mu tsare dukiyarmu. Gyara kayanka ba zai zama sauke mu raba ba. Kada mu wulakanta dukiyar da Allah Ya ba mu, lallai mu yi tattalinta. Kada mu wuce wuri wajen yin amfani da ita, kuma kada mu bar ta haka nan, ba mu jujjuya ta don ta karu. Misali, kada mutum don takamar yana da Naira miliyan goma, ya koma ya yi zaman dirshan, yana bushasha da ita har ta komo Naira miliyan daya. A’a, lallai ne ka samo hanyoyin da za ka habaka ta don ta karu! Tanaji babban al’amari ne a rayuwa, saboda haka sai a kula, amma fa kuma kada a yi rowa – a rika yin kyauta da sadaka da sauran ayyukan alheri, wadanda shari’a ta nuna, ta yarda da su.
Mu kiyaye iyali da ’ya’ya! Mu tsare mutuncinsu da jikunansu, musamman ma yara kanana. Duk abin da aka ga dalili a kansa cewa yaro zai iya ya ji ciwo a cikin gida ko a waje, lallai a tabbatar an kawar da shi, an kai shi inda ba zai kai gare shi ba. Kada a aje duk wani kayan jin rauni, kamar su wuka ko reza ko allura, musamman ma ta asibiti domin kada, in ba kowa, yaro ya dauka ya tsira wa wani ya ce wai zai yi masa allura ne saboda ya ga ana yi a asibiti. Yaro abin da ya gani a aikace, sai ya ce shi ma zai kwatanta! Kada a aje magani inda zai ji mai dadi, ya dauki kwalbar gaba daya ya kwankwade. In an lura, har a jikin kwalaben magunguna ana rubuta cewa kada a aje inda yaro zai dauka.
Mu kiyaye iyali dangane da hankulansu – kada a bari su rika shaye-shayen kayan maye da gusar da hankali! A kula da akidarsu – kada a bari su zama karkatattu kuma batattu, wadanda ba su bin tafarkin sunnar Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam). Lallai a tabbatar suna kan wannan tafarki na akidar Ma’aikin Allah, mai tsira da amincin Allah, wadda ya karantar da sahabbansa har suka gama rayuwarsu a kanta.
Mu kula kuma mu kiyaye halayensu, mu kare musu duk abin da zai cutar da su a rayuwa, balle har mu bari ya bata musu rayukansu. Mu tunkude musu duk abin da zai jawo musu halaka a nan duniya, wanda har zai iya jawowa su kasance ’yan wuta a Lahira. Babu dadi a wayi gari ka auro mace, ta haifi da, ka yi dalilin da suka koma Lahira suka shiga wuta. Lallai idan ba a shiryar da su kan hanya madaidaiciya ba, to ai an ci amanarsu. Ka ga kuwa ashe dole ne a tsare wadannan abubuwa. Allah Ya tallafa mana!
A karshe dai gaba dayan al’amari shi ne mutum ya mayar da hankali wajen tabbatar da neman ilimin addini da sanin makamarsa dangane da yadda zai gudanar da rayuwarsa a karkashin inuwar addinin Musulunci, wanda, kamar yadda aka bayyana tuna farko, shi ne asali.
Tauhidi – kadaita Allah cikin bauta (ibada) – shi ne ginshikin al’amari, wanda domin tabbatar da shi ne ma Allah Ya saukar da littattafai kuma Ya turo manzanni don su nuna yadda za a yi bautar, wadda ta kunshi Sallah, Azumi, Zakkah, Hajji, kyautata wa iyaye da makwabta da bako da sauran mu’amaloli – kai da dai duk wani nau’i na ibada, wanda ba ya inganta, sai an gina shi a kan tauhidi.
Nan za mu takaita a kan wannan maurdu’i, sai a lokaci na gaba, in Allah Ya kai mu, za mu gabatar da wata makalar. Muna rokon Allah, don tsarkin sunayenSa, Ya ba mu lafiya da zaman lafiya, a kasarmu da ma duniya baki daya.
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!