Daurin auren dan Sanata Barau Jibrin ya tara manyan Najeriya a Kano

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ne ya zama waliyyin angon, Abdullahi Barau Jibrin.

Daurin auren dan Sanata Barau Jibrin ya tara manyan Najeriya a Kano

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, na da daya daga cikin manyan bakin da suka halarci daurin auren dan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin a Jihar Kano.

An daura auren Abdullahi Barau Jibrin da amaryarsa, Bilkisu, diyar Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai, Aliyu Sani Madaki.

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas da gwamnoni da manyan ’yan siyasa sun halarci taron daurin auren da aka gudanar a Masallacin Sheikh Isiyaka Rabi’u da ke Goron Dutse bayan sallar Juma’a.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ne ya zama waliyyin angon, yayin da Shugaban Majalisar Wakilan ya zama waliyyin amarya a kan sadakin N500,000.

An daura auren ne kamar yadda addinin Islama ya tanadar bisa jagorancin Babban Limamin Masallacin, Sheikh Abdullahi Mahmud Salga.

Wadansu daga cikin mashahurai da suka halarci daurin auren sun hada Sanata Ali Ndume, Kawu Sumaila, da kuma kusoshin gwamnatin Kano.