David Villa ya yi ritaya daga kwallon kafa

Tsohon dan kwallon Spain da FC Barcelona David Villa a shekaranjiya Laraba ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa. Ya yi ritayar ce a lokacin da ya cika shekara 37. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter daga kulob din da yake yi wa kwallo a Japan Bissel Kobe, ya […]

David Villa ya yi ritaya daga kwallon kafa

David Villa

Tsohon dan kwallon Spain da FC Barcelona David Villa a shekaranjiya Laraba ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa.

Ya yi ritayar ce a lokacin da ya cika shekara 37.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter daga kulob din da yake yi wa kwallo a Japan Bissel Kobe, ya ce ya yi ritayar ce don ya bai wa matasa dama.

Billa ya lashe kofuna da dama da suka hada da na La-Liga da na Zakarun Turai a FC Barcelona da kuma Kofin Duniya a 2010 ga kasarsa Spain.

Rahotanni sun ce ya buga wasa 752 kuma ya zura kwallaye 376 a raga.