Davido na shan suka kan bidiyon wakar ‘cin zarafin Musulunci’

Musulmi na ganin mawakin ya zarce iyakarsa game da sabuwar wakar da ya saki.

Davido na shan suka kan bidiyon wakar ‘cin zarafin Musulunci’

Shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, na ci gaba da shan suka daga Musulmai a shafukan sada zumunta, biyo bayan sakin wani bidiyon waka na tsawon dakika 45 a Twitter.

Musulmi da dama sun bayyana bidiyon wakar ta Logos Olori a matsayin abin takaici da kuma cin fuska ga Addinin Musulunci.

Tun da fari dai a cikin wakar a nuna wasu sanye da shiga irin ta Musulmai suna sallah kuma suna tikar rawa, lamarin da Musulmi ke ganin mawakin ya zarce makadi da rawa.

Sun zargi mawakin, wanda ke da mabiya kusan miliyan 14 a intanet, da rashin mutunta addinin Musulunci ta hanyar hada ibadarsu da al’adarsu tare da waka da raye-raye.

Sun kuma ja hankalin mawakin da ya goge bidiyon wakar tare da bai wa daukin Musulmi hakuri. Daga baya ya goge wakar.

Al’amarin dai na ci gaba da haifar da zazzafar muhawara da musayar ra’ayi a tsakanin mabiya Davido da wasu fitattun masu fada a ji Musulmi a kafafen sada zumunta.

Daga cikin su akwai Bashir Ahmad da fitaccen jarumin Kannywood da Nollywood, Ali Nuhu.

Da yake mayar da martani ga bidiyon, Bashir, Mataimaki na Musamman ga tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan harkokin sadarwa na zamani, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Akwai dalilai da dama da ya sa kowane Musulmi ke ganin wannan abun a matsayin rashin mutunci, da kuma batanci @davido. Ina tunanin kun san cewa mu Musulmi ba ma cudanya addininmu da wasa ta kowace hanya, musamman sallah, wadda aba ce mai girma kuma ta biyu daga cikin rukunan Musulunci guda biyar.

“Idan ana sallah, Musulmai suna tunawa da Ubangijinmu, Allah, suna nuna kauna da girmamawa a gare shi. Sallah na sa mutum ya fuskanci ubangijinsa ne. Abin da muka gaskata ke nan, kuma shi ne imaninmu. Ka girmama hakan. Babu wani musulmin da karbi wannan a matsayin girmamawa”.

Fitaccen jarumin fina-finan Arewa, Ali Nuhu, a wani sako da ya wallafa ta shafinsa na Instagram, ya shawarci mawakin da ya mutunta ‘addini da al’adar sauran mutane.

Ya wallafa hoton Davido mai alamar soke fuskarsa.

Ali Nuhu ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Na gamu da faifan bidiyo mai cike da cece-kuce wanda @davido ya wallafa, ya kamata mu koyi mutunta addini, al’ada da al’adar wasu. Wannan ba abin da za a amince da shi a Musulunci ba ne. M Ka cire wannan bidiyon ka bayar da hakuri kan cutar da al’ummar musulmi baki daya.”

Tuni dai kafafen sada zumunta suka dauki zafi kan bidiyon da mawakin ya wallafa, inda wasu suke ba shi shawarar sauke bidiyon don mutunta wadanda ke ganin an saba musu.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume