Davido ya goge bidiyon wakar ‘cin zarafin Musulunci’

Daga karshe mawakin ya goge bidiyon wakar da ya jawo cece-kuce.

Davido ya goge bidiyon wakar ‘cin zarafin Musulunci’

Davido

Fitaccen mawakin Kudancin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya goge bidiyon wakar da ya wallafa bayan shan suka daga Musulmai a shafukan sada zumunta.

Musulmi da dama sun bayyana bidiyon wakar mai suna ‘Logos Olori’ a matsayin abin takaici da kuma cin fuska ga Addinin Musulunci.

Tun da fari dai a cikin wakar an nuna wasu sanye da shiga irin ta Musulmai suna Sallah kuma suna tikar rawa, lamarin da Musulmai ke ganin mawakin ya zarce makadi da rawa.

Sun zargi mawakin, wanda ke da mabiya kusan miliyan 14 a intanet, da rashin mutunta addinin Musulunci ta hanyar hada ibadarsu da al’adarsu tare da waka da raye-raye.

Sun kuma ja hankalin mawakin da ya goge bidiyon wakar tare da bai wa daukin Musulmi hakuri. Daga baya ya goge wakar.

Al’amarin dai na ci gaba da haifar da zazzafar muhawara da musayar ra’ayi a tsakanin mabiya Davido da wasu fitattun masu fada a ji Musulmi a kafafen sada zumunta.

Daga cikin su akwai Bashir Ahmad da fitaccen jarumin Kannywood da Nollywood, Ali Nuhu.

Lamarin dai ya haifar da zazzafar muhawara a kafafen sada zumunta, sai dai daga karshe mawakin ya yanke hukuncin sauke bidiyon.

Wasu kuma na ganin duk da hakan akwai bukatar mawakin ya fito fili ya bai wa Musulmai hakuri kan bidiyon da ya wallafa.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa