Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya
Mawaƙin ya ce zai yi cikakken bayani kan yadda tallafin zai gudana.
Fitaccen Mawaƙin Kudancin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da ‘Davido’, ya yi alƙawarin bai wa marayu tallafin Naira miliyan 300 a faɗin Najeriya.
Mawaƙin ya bayyana haka ne a shafinsa na X (Twitter), inda ya ce tallafin zai kuma taimaka wa wata ƙungiya da ke yaƙar matsalar shaye-shaye.
Ya ce zai fitar da cikakken bayani nan ba da jimawa ba, kuma zai yi amfani da gidauniyarsa ta Davido Adeleke Foundation (DAF).
Tun bayan kafa DAF a shekarar 2022, Davido ya kasance yana taimaka wa yara masu buƙata ta musamman.
A shekarar 2023, ya bai wa marayu tallafin Naira miliyan 200, wanda yara sama da 14,000 suka amfani da tallafin.
Ayyukan jin-ƙan da Davido ke yi, sun fara ne a shekarar 2021, lokacin da ya tara Naira miliyan 200 daga masoyansa domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Ya ƙara da Naira miliyan 50 daga aljihunsa, sannan ya bai wa marayu da wata ƙungiya da ke yaƙi da shaye-shaye.
Mawaƙin, ya ce ya ƙudiri aniyar ci gaba da inganta rayuwar yara ta hanyar ba su tallafi.