Dawayya ta haihu ranar Arfa a Saudiyya
Tsohuwar shahararriyar jarumar fim din Hausa Rukayya Umar Santa, wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya ta haife jaririnta a kasar Saudiyya.Dawayya ta haife jaririn nata ne a Asibitin kwararru na Wuzaratil Sihha da ke kasar ta Saudiyya a ranar Arfa.A tattaunawar da Aminiya ta yi da ita, mai jegon wacce a yanzu haka take […]

Tsohuwar shahararriyar jarumar fim din Hausa Rukayya Umar Santa, wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya ta haife jaririnta a kasar Saudiyya.
Dawayya ta haife jaririn nata ne a Asibitin kwararru na Wuzaratil Sihha da ke kasar ta Saudiyya a ranar Arfa.
A tattaunawar da Aminiya ta yi da ita, mai jegon wacce a yanzu haka take Saudiyya ta bayyana cewa tun da farko ta tafi can Saudiyya ne da niyyar haihuwa sai kuma ta yi amfani da damar don samin dacewa da lagwadar da ke cikin watan Zul Hijja: “Duk da cewa na je Saudiyya ne don na haihu, sai kuma na yanke shawarar yin amfani da damar don yin aikin Hajji. Nagode Allah bisa kyuta da rahamar da ya yi min. Ni kaina ina ji a raina Allah Ya yi min babbar baiwa, nagode maSa.” Inji ta
Rukayya Dawayya ta bayyana cewa ma’aikatan asibitin da suka karbi haihuwarta sun taimaka mata kwarai da gaske inda bayan ta haihu suka dauke ita da jaririnta suka kai ta filin arfa inda ta gudanar da tsayuwar Arfa wanda babban rukuni ne daga cikin rukunan aikin Hajji.
Ta ce tana sa ran dawowa gida Najeriya a karshen wannan watan inda take da niyyar shirya gagarumin taron suna a Kano: “Idan Allah Ya yarda a karshen wannan watan zan dawo Najeriya inda kuma zan shirya gagarumin bikin suna a Kano. Haka kuma ina so na sanar da jama’a cewa tuni aka rada wa jaririn suna Umar Arfat Adamu Teku” Inji ta.
Binciken Aminiya ya gano cewa shirye-shirye sun yi nisa inda ’yan uwa da abokan arziki suka fara zumudin taryar tsohuwar jarumar tare da jaririnta zuwa gida Najeriya.
Idan dai za a iya tunawa a ranar 6 ga watan Yulin shekarar bara ne mai jegon ta yi aure da wani dan kasuwa mazaunin Abuja mai suna Alhaji Muhammad Teku, bayan rasuwar tsohon saurayinta Mustapha Aliyu Tsanyawa, wanda dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Tsanyawa da kunci a Majalisar Dokokin Jihar Kano, watanni kadan kafin lokacin da aka sanya na bikinsu.