Dawo da darajar karatu
Duk lokacin da aka yi maganar karatu, a kan yi tunanin malamai, makarantu ko marubuta, amma a zahiri abin da ya kamata ya fara fado wa mutum idan ya ji kalmar karatu ita ce karanta rubutu ko kuma littafi! Tabbas karatu da rubutu suna tafiya tare, sun dogara da juna, wajen haifar da fahimta da […]
Duk lokacin da aka yi maganar karatu, a kan yi tunanin malamai, makarantu ko marubuta, amma a zahiri abin da ya kamata ya fara fado wa mutum idan ya ji kalmar karatu ita ce karanta rubutu ko kuma littafi! Tabbas karatu da rubutu suna tafiya tare, sun dogara da juna, wajen haifar da fahimta da ilimi don inganta rayuwa.
Za a iya cewa littattafai wasu tarin takardu ne masu ba da ma’ana, wadanda aka rubuta don a karanta a ilimantu. Kafin zuwan sadarwar zamani ba inda za ka samu bayanai sai a laburari, domin a wancan lokacin har jaridu da mujallu ake saya a kai laburari, kuma koyaushe za ka ga majalisu da matasa a cikin laburari.
Tabbas kowace sana’a na bukatar karatu da lissafi, walau welda da tela da noma da kiwo da kafinta da dai sauransu. A dalilin haka karatu da rubutu suka wajaba ga kowa, kuma hakan ke tabbatar da cewa ilimi ya wanzu. Rayuwar yara ta kan dogara ga rubutu da karatu kafin su hau kurangar samun ilimi. Kuma hakan ke yaye hadarin jahilci.
Amma abin takaicin shi ne a ‘yan shekarun da suka shude al’adar karance-karance ta ja baya a Najeriya, musamman a Arewacin kasar, inda ba yaran ba, ba matasan ba, ba dattijan ba, ba daliban ba. Adabin Kano ya shiga hunturu!
Yayin da a kwanannan an fi dogaro da radiyo ko talabishin, kallon fina-finai a kan karatu ko zuwa wajen malamai, akan ba kanzon kurege muhimmanci wajen yada sakonni! Hakan ya zama barazana ga bunkasar ilimi da ci gaban dalibai, domin ko akwai laburari, sai ka iske ba wanda yake zuwa, an mayar da shi mabuyar beraye ko dandalin shakatawar bata gari!
Idan muka lura yara wadanda basu sami horo wajen karatu ba, kan zama koma baya a azuzuwa, yayin da hakan kan haifar da nadama nan gaba, inda dan talaka shi ne na dari a aji, ko na karshe, talaka shi ne wutsiya! Kuma su zama masu yiwuwar zama marasa amfani a al’umma, su ne mugaye masu zaluntar ‘yan uwansu da mafadata da mayaudara da gwanayen satar jarrabawa.
dalibai a gaba da sekandare kan gwammance su mausayar da mutuntukarsu don samun sakamako a jarrabawa, su wa laccara kawalci ko su biya malamai, a yi zuku, wasu ma kan wa malaman barazana idan ba a hayar da su ba, su far wa malamin, irin wadannann daliban basu da lokacin karatu!
Amma yayin da yara suka sami horon karatu da rubutu tun suna kuruciya, suka giga a makarantar nasari, sai su ci gaba da fahimtar sauran darusan a makaranta har su kai ga jami’a. Yayin da ko sun kai wannan matakin sai sun yi dacen kayan aiki kamar littattafai, jaridu, taswirar duniya, kamus, kundin ilimi, da sadarwar zamani a dunkule.
Duniyar karatu ta bunkasa, kuma tana zaman kanta. Akwai masu sayar da littattafai, wanda sun mayar da littattafai jarinsu ta wannan harkar suke samu su ci su gina rayuwarsu, banda wannan rukunin akwai masu buga littattafai, ta hanyar a dauki ma’aikata, a sami jari a habaka, ilimi ya bunkasa.
Bayan duk ka samu wadannan wani abin da yake karanci a kasar nan musmaman a Arewaci shi ne karanci dakunan karatu, da rashin kai ziyara, wai ina laburarin, ina littattafan suke? Wa zai je laburari? Duk da babatun gwamnati na wadata makarantun sakandare da laburari.
Babu shakka ilimi wata harka ce da ake yi ga baki daya rayuwa, ba lallai ba sai a makarantu ake samun ilimi! Tafiya ma mabudin ilimi ce! Duk kasar da ta bunkasa ilimi ga matasa, kasar zata ci gaba, amma a halin yanzu ba za a iya jera Najeriya ba a matsayin kasar da ta ci gaba ba a kowane fanni, saboda matasa basu daukar karatu a sunan komai, an ba neman kudi da siyasa fifiko. Sannan rashin karatun ya sa ba a cin jarrbawa ba tare da sata ba! Cin hanci da rashawa da ake zargin manyan ma’aikata, ya shafi dalibai wani lokacin yara ‘yan firamare!
An lakutawa ‘yan kasa zuma a baka, ana cewa za a bunkasa ilimi, a zamanantar da kiwon lafiya da harkar ilimi, amma a rabin zangon ba a cimma manufa ko daya ba, don jin dadin ‘yan kasa, ma’aikatan nawa aka dauka, kashi nawa ne cikin darin matasan Najeriya? An tsallake dafke, an fada rijiya!
Akwai dalilai da dama da ya kamata a tabbatar da cewa an farfado da al’adar karance-karance, da farko malamai, manazarta da dalibai duk sun tabbatar da cewa babu littattafan karantawa a makarantu ko shagunan sayar da littattafai, kuma an san da gangan gwamnati ke kauda kai. Idan muka dauki makarantun gaba da sakandare, kusan an daukesu mafi koma baya a duniya don babu littattafai babu ingantaccen laburari. Akan sami ‘yan Najeriya masu hazaka, amma wannan baiwa ce, ba wai kokarin mahukunta ba ne.
Haka idan aka yi maganar daukar aiki, muna fuskantar koma ba, ba kishin juna, sai kishin aljihu. Abin takaicin shi ne wadanda muka zaba don sun zamanantar da ilimin sun dauke ‘ya’yansu daga makarantun gwamnati. Nan gaba ba zamu amince da wani ya mulke mu ba, sai wanda ya je makarantun gwamnati, kuma wanda ‘ya’yansa ke karatu da ‘ya’yan talakawa, ai su ma ‘yan kasa ne. Idan ya ci, ya ce zai mayar da ‘ya’yansa makarantun kudi ko kasashe ketare, ya ketara kar ya dawo. Ya ba mu wakilcinmu da mukami ko sarautarmu, shikenan, Kar a mayar da gyara harkar ilimi wasikar jaki!
Wani mataki na dawo da dakunan karatu shi ne a gina laburari a kananan hukumomi 774 a duk jihohin kasar. Kuma kafin a rantsar da caiman ya dauki alkawali haka gwamnoni da shugaban kasa na zamanantar da ilimi a zahirance. A ci gaba da gasa tsakanin marubuta, da jawo yara da matasa harkar rubuce-rubuce.
Kan farfado da ilimi ya zama gaba-gaba a cikin bukatun majalisar tarayya, abin kan zama labari, domin ba hobbasa, amma da za a sayo littattafai, a kawo kayan aiki makarantu, sannan a inganta malamai, tabbas hakan zai farfado da ilimi.
Su kansu kungiyoyin marubuta sun fada rububi, maimakon habaka rubutu ko littattafai sai a buge da neman kudi da kamun kafa. Za a iya karfafawa marubuta matasa ta hanyar buga littattafansu, shirya gasa, koya fassara da yin fassarar. Gayyatar marubuta da manazarta don a saurari bita da tarrurukan ji ka karuwa.
Rashin littattafai ba laifin matasa bane, ko dalibai, laifin malamai ne da manazarta, me yasa ba a rubuta littattafan da zasu ja hankalin makaranta ba? Sannan me gwamnati ta yi da sauran ministocin kamar na ilimi, na matasa da wassani da na yada labarai me suka yi wajen jan hankalin mu ga karance-karance.
Lokaci ya yi da mahukuna, malamai a kowane mataki da ‘yan siyasa za a yunkuro don wadata kauyuka, birane, makarantu da laburari. Duk da burin farfado da laburari, a wannan zamanin ana bukatar a bunkasa kundin intanet da rubuce-rubuce domin dalibai sun fi dogara da sadarwar zamanin wajen neman ilimi ba littattafai ba, amma duk wanda zai ci ribar ilimi sai ya duba littafi.
Modoji, Katsina. Buhari Daure <[email protected]> [email protected]