Dawowar Suntai ta raba Taraba

Komawar da Gwamna danbaba Suntai ya yi  Jalingo a Jihar Taraba bayan doguwar jinyar da ya yi a kasar waje ta jefa jihar  cikin rudani inda aka samu gwamnoni guda biyu kowanne yana cewa shi ne yake da ikon gudanar da gwamnatin jihar kuma aka samu baraka a majalisar dokokin jihar.A ranar Talata ne dai […]

Dawowar Suntai ta raba Taraba

Masu rufa wa Gwamna Danbaba Suntai baya suna tallafa masa wajen sauka daga jirgin sama a AbujaKomawar da Gwamna danbaba Suntai ya yi  Jalingo a Jihar Taraba bayan doguwar jinyar da ya yi a kasar waje ta jefa jihar  cikin rudani inda aka samu gwamnoni guda biyu kowanne yana cewa shi ne yake da ikon gudanar da gwamnatin jihar kuma aka samu baraka a majalisar dokokin jihar.
A ranar Talata ne dai gwamna Suntai ya aika wa majalisar dokokin jihar da wata wasika da ke sanar da ita cewa ya dawo daga jinya kuma ya samu saukin da zai ci gaba da gudanar da mulkin jihar, sai dai kuma saboda halin da aka ga gwamnan lokacin da ya sauka daga jirgin sama a Abuja da kuma Jalingo ya sanya mutane da dama suna tababar  bayanin da aka yi a wasikar cewa zai iya cigaba da mulkin jihar.
Wannan ne ya sanya Shugaban majalisar dokokin jihar Haruna Tsokwa  ya bayyana cewa ba za su amince da sahihancin takardar ba sai sun ga gwamna Suntai ko dai a gidansa ko kuma a majalisa domin su tabbatar cewa lallai ya samu lafiyar da zai iya cigaba da gudanar da aikinsa na gwamna.
A ranar Laraba kuma sai aka sake samun wata sanarwa da ta fito daga wani mashawarcin gwamna Suntai a kan hulda da kafofin yada labarai, Silbanus Giwa, da ke nuna cewa an rushe majalisar zartarwar jihar da kuma masu bayar da shawara ga gwamna tare da nada tsohon kwamishinan  shari’a, Timoty Katap  a matsayin sabon Sakataren Gwamnati,  sannan aka nada Aminu Jika a matsayin Babban Jami’in Gudanarwar Gidan Gwamnati. Sanarwar  ta ce Gwamna Suntai ya gode wa wadanda aka rushen tare da yi musu fatan alheri.
Wannan sanarwar ta saka jefa jihar a cikin rudani, domin a yayin da bangaren gwamna Suntai ke nuna cewa shi ne ke da iko a jihar, bangaren mukaddashin gwamna Garba Umar kuma ta bakin kakakinsa Kefas Sule cewa ya yi mukaddashin gwamnan ne yake cigaba da gudanar da mulkin jihar domin haka  gwamnati daya ce a jihar ,don haka ya shawarci kwamishinonin da aka ce an rushe da kuma sauran jama’ar jihar da su kwantar da hankalinsu zai fitar da wata sanarwa daga baya.
A ranar Larabar da ta gabata din nan ba a gudanar da taron majalisar zartarwa kamar  yadda aka saba ba, domin an yi tsammanin gwamna Suntai zai jagoranci zaman majalisar har ma ya rantsar da sabon sakataren gwamnati, amma hakan bai yiwu ba. Sai dai shi mukaddashin gwamna Garba Umar ya yi wata ganawa ta sirri da kwamishinonin jihar.
Majalisar dokokin jihar Taraba dai ta bayyana cewa  a saninta Gwamman Jihar Mista danbaba danfulani Suntai bai koma kan mulkin ba, bayan da ya koma gida daga jinya a Amurka, duk da ikirarin da mukarabbansa  suka yi na cewar ya koma bakin aikin. Majalisar  ta ce a saninta Mukaddashin Gwamnman jihar, Alhaji Garba Umar ne ke rike da ragamar mulkin jihar.
Shugaban Majalisar Dokokin jihar ta Taraba, Haruna Tsokwa ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai, sai dai kuma wadansu daga cikin ‘yan majalisar  a karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye sun nuna adawa da wannan matakin.
Tun farko dai an shirya a ranar Talata ce Majalisar Dokokin jahar ta Taraba za ta yi wani zama don duba bukatar Gwamna Suntai da ke kunshe a wasikar da ya aike mata cewa ya koma bakin aikinsa, amma hakan ba ta samu ba saboda rashin daidaiton da aka samu tsakanin ‘yan majalisar dokokin, inda rahotanni suka nuna cewa an yi ta ganawar sirri tsakanin bangarori daban-daban game da batun.
Rahotanni  sun nuna cewa an hana wadansu daga cikin ‘yan majalisar,  ciki har da Shugaban Majalisar da Mataimakinsa, ganin Gwamna Suntai lokacin da suka ziyarci gidan gwamnan domin duba shi. Inda ake zargin uwargidan Gwamna Suntai da cewa ita ce ta yi kane-kane ta hana ‘yan majalisar ganin gwamnan. Mista Suntai dai ya samu rauni a kwakwalwarsa ne cikin wani hadarin jirgin sama a Yola.
Gwamna Danbaba Suntai yana xaga wa jama’ar da suka je tarbarsa filin jirgin saman Abuja hannu jim kadan da isowa Najeriya daga AmurkaMajalisar  ta nuna  cewa sai ta tantance idan Gwamna danbaba danfulani Suntai ne ya rubuta wasikar da kansa kamar yadda doka ta tanada. Wadansu na zargin cewa wani ya kwaikwayi sanya hannun gwamna Suntai a wasikar da aka tura wa majalisar, zargin da Lauyan  Femi Falana ya bukaci babban sufeton ‘yan sandan kasar nan  ya bincika.
Gwamna Suntai dai ya kwashe kimanin watanni goma yana jinya a kasashen Jamus da Amurka kafin a dawo da shi gida ranar Lahadin da ta gabata amma cikin wani yanayi na rashin koshin lafiya.
Shugaban majaliisar  dokokin jihar Taraba ya bayyana cewa, “abin da muke bukata shi ne gwamnanmu wanda kowa yake kauna ya fito ya yi wa jama’ar jihar Taraba bayani a gaban wakilansu da suka zaba, idan ya kasa yin haka to ya nuna cewa ba zai iya gudanar da mulkin jihar ba ke nan sai majalisa ta ba shi izinin ya koma ya cigaban da jinya har sai ya samu lafiya.
Haruna Tsokwa wanda yake tare da mataimakinsa Josiah Sabo Kente, ya kara da cewa, Mukaddashin Gwamna Garba Umar ne zai cigaba da gudanar da mulkin jihar tun da ‘yan majalisar ba su tabbatar da samun lafiyar Gwamna Suntai ba.
Ya ci gaba da cewa, kaunar jihar  ce ta sanya suka nace sai Gwamna Suntai ya bayyana a gabansu tare da tunanin lafiyarsa da kuma kwanciyar hankalin iyalinsa.
Gwamna Suntai ya dawo Najeriya ne ranar Lahadin da ta gabata bayan ya kwashe watanni goma yana jinya a kasar waje a sakamakon raunin da ya samu lokacin da y a yi hadarin jirgin sama a kusa da Yolan jihar Adamawa a yayin da yake tuka wani jirgin sama a ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 2012, inda aka garzaya da shi wani asibiti a kasar Jamus daga bisani kuma aka koma da shi kasar Amurka a watan Maris din wannan shekarar, inda ya yi jinya har ranar da ya dawo.
Makusantan gwamna Suntai sun nuna cewa ya murmure sarai kuma zai iya ci gaba da aikinsa na gwamna, bayanin da ya jefa shakku a cikin zukatan jama’a, musamman lokacin da suka ga sai da aka agaza masa ya sauko daga jirgi a Abuja da Jalingo, kuma tun da ya dawo an hana mutane ganawa da shi.
Daga dama Obadiah Ando sai Darius Ishaku Minista a Ma’aikatar da ke raya yankin Neja-Delta sai Gwamna Danbaba Suntai sai Farfesa Jerry Ghana a filin saukar jirgin saman Abuja jim kadan da dawowar Gwamnan daga AmurkaShugaban majalisar dai yana ganin  wadansu ne suke so su yi amfani da dawowar gwamnan su haifar da baraka a tsakanin al’ummar jihar, don haka ya ce ya kamata a taka musu birki.
Ya yi nuni da cewa, wannan abun da ke faruwa a jihar Taraba kwatankwacin abin da ya faru ne a lokacin da marigayi Shugaban kasa Umaru Musa ‘Yar’aduwa ba shi da lafiya, inda wadansu na kusa da shi suka yi kane-kane suka hana mutane zuwa kusa da shi, al’amarin da ya kusa raba kan jama’ar kasar nan.
Idan za a iya tunawa a watan Fabrairun shekarar 2010 ne aka dawo da marigayi shugaban kasa Umaru ‘Yar’aduwa daga wani asibiti a kasar Saudiyya, duk da cewa bai samu murmurewar da zai iya gudanar da mulkin kasar ba, inda ya rasu bayanwatanni biyu da dawowarsa.
Saboda haka Shugaban majalisar dokokin jihar Taraba Haruna Tsokwa ya ce a matsayinsu na wakilan jama’a ba za su zura ido su bari a maimata irin haka a jihar Taraba ba.
Sai dai a ganin shugaban masu rinjaye na majalisar Joseph Albasu Kunini, tsarin mulki bai ce sai gwamna Suntai ya je gaban majalisa ba idan ya dawo daga jinya, abin da ake bukata kawai shi ne ya rubuta wa majalisa cewa ya dawo kuma zai ci gaba da aikinsa.
Ya bayyana wa sashin Hausa na BBC cewa, wannan shi ne abin da doka ta bukaci gwamna Suntai ya yi kuma ya yi hakan.
Amma Shugaban majalisa Haruna Tsokwa ya ce ba su bai wa shugaban masu rinjayen damar ya bayyana wa manema labarai cewa majalisar ta amince da wasikar da Suntai ya tura mata ba, haka kuma ya karyata zargin da shugaban masu rijayen ya yi cewa wai shi da mataikinsa sun gudu daga majalisar dominsu haifar da rudani.
Al’amura dai sun dagule a jihar Taraba a sakamakon dawowar gwamna Suntai saboda rashin tabbas game da ainihin wanda yake jagorancin jihar, gwamna Suntai ne wanda tun da ya dawo ba a ji ya yi magana  kuma bai bayyana a bainar jama’a ba ko kuwa mukaddashin gwamna Garba Umar ne wanda magoya bayan gwamna Suntai suke ganin maci amana ne da ya kamata a tsige shi, har ma suka hana shi ganin gwamna Suntai din?
Gwamna Danbaba Suntai a lokacin da ya isa Jihar TarabaMasu fashin siyasa dai  suna ganin wadansu mutane ne ‘yan kalilan suke son juya akalar jihar yadda suke so ta hanyar amfani da halin da gwamna Suntai yake ciki domin cim ma burinsu.