Daya daga cikin Alhazan Kano ta rasu bayan kammala Aikin Hajji a Saudiyya

Tuni aka yi jana’izarta a masallaci Harami na Makkah

Daya daga cikin Alhazan Kano ta rasu bayan kammala Aikin Hajji a Saudiyya

Filin Arafa

Allah Ya yi wa daya daga cikin alhazai mata da suka je Aikin Hajjin bana daga Jihar Kano rasuwa a birnin Makkah na kasar Saudiyya.

Ta rasu ne a daren Talata, bayan ta kammala Aikin Hajjinta.

Shugaban Hukumar Jindadin Alhazai na Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ne ya sanar da hakan yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Makkah.

Danbappa ya cewa marigayiyar mai suna Hadiza Isma’il da ta je daga Karamar Hukumar Madobi, ta yi fama da jinya kafin rasuwar tata.

Shugaban ya yi addu’ar nema wa marigayiyar rahama wajen Allah tare da addu’ar Allah Ya ba iyalanta hakurin jure rashinta.

Tuni dai aka yi jana’izarta a Masallachin Harami mai alfarma da ke birnin Makkah.

Idan dai za a iya tunawa, kimanin alhazan Najeriya 7 daga jihohi daban-daban na fadin kasar ne suka rasa ransu a kasar kamar yadda shugaban tawagar jami’an kiwon lafiya na Najeriya a kasa mai tsarki, Dokta Usman Galadima, ya tabbatar wa Aminiya.

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta

Jerin Manyan Dambarwan Kano a 2024