daya daga ’yan fashin da ake nema ya shiga hannu

kungiyar ‘Yan Banga reshen jihar Edo karkashin jagorancin Shugabansu Alhaji Shuaibu Muhammed K.T. ta samu nasarar cafke daya daga cikin ’yan fashi da makami da suka addabe su, kuma wanda aka kama rikakke ne da ake nema ruwa a jollo mai suna Muhammadu Inuwa Dala dan shekara 30 wanda ke cikin ‘yan fashi 9 da […]

daya daga ’yan fashin da ake nema ya shiga hannu
daya daga ’yan fashin da ake nema ya shiga hannu

kungiyar ‘Yan Banga reshen jihar Edo karkashin jagorancin Shugabansu Alhaji Shuaibu Muhammed K.T. ta samu nasarar cafke daya daga cikin ’yan fashi da makami da suka addabe su, kuma wanda aka kama rikakke ne da ake nema ruwa a jollo mai suna Muhammadu Inuwa Dala dan shekara 30 wanda ke cikin ‘yan fashi 9 da ake nema.

‘Yan fashin da ake zargi, asirinsu ya tunu ne lokacin da suka tare wani dan kasuwa, Alhaji Hasana Gurgu a hanyarsa ta komowa gida, bayan ya kammala harkansa a kasuwar shanu ta Benin, inda miyagun suka gitta ta gabansa; daya daga cikinsu ya nuna masa Bindiga da misalin karfe tara na dare. Lokacin da suke kokarin ci ma sa mutunci sai ga ‘Yan Banga masu sintiri, suka bullo musu ta baya, daga nan kuma miyagun sai suka bar wannan dan kasuwar suka gudu. ’Yan bangar suka rufa musu baya suna gudu suna harbi, inda ’yan sintirin suka cin masu, a nan suka yi barin wuta, amma duk da haka ’yan bangan sun samu nasarar kame babbansu, sauran kuwa duk sun ranta a cikin na kare, inda suka boye cikin duhuwar kungurmin daji.
A Cikin wadanda ake nema, sun hada da Abdullahi da Emma da Yahya da Tanko da Saleh da Ibrahim da Silber da Prisesion. Kuma ‘’yan sanda ma na neman ’yan fashi a Jihar Edo
A cewar Alhaji Shu’aibu Muhammadu K.T., miyagun an ce sun fara farma wata mashaya ahanyar Benin zuwa Agbor daga bisani sai suka far wa wata mata mai saida abinci, wadda ba a fayyace sunanta ba, a cikin Benin kafin su tare wannan dan kasuwar a Unguwar Eyaen, wanda ba su samu nasara ba, har aka kama madugunsu.
‘’Lallai muna rike da wani matashi dasu ’yan banga suka kawo mana shi tare da makami na zamani wanda suke zargi dan fashi ne da makami mai suna Muhammadu Inuwa acikin mutum tara da suka kawo mana rahoto akansu don haka shi wanda yake ahannu yanzu za’mu kai shi hedikwatarmu ta yansandan jihar Sannan ahalin yanzu mun baje ma’aikatanmu domin neman sauran kuma na tabbatar za’mu samu nasaran kamesu a duk inda suka shiga acikin jihar nan ba da dadewaba saboda haka muna bukatar jam’a su taimaka su bamu hadin kai da goyon baya, tare da bayanan sirri na gaskiya akan miyagun mutane ako da yaushe inji shi.’’