D’Banj ya fitar da sabuwar waka
Fitaccen mawakin nan mai sun a D’Banj ya fitar da sabuwar wakarsa ta bana, mai taken ‘Raise Your Glass.’ D’banj ya fitar da wakar ne da hadin gwiwar kamfanin nishadantarwa na Hennessy a karshen makon da ya gabata.Tuni wasu gidajen radiyo suka fara sanya somin-tabin wakar don nishadantar da mutane a Legas da kuma jan […]

Fitaccen mawakin nan mai sun a D’Banj ya fitar da sabuwar wakarsa ta bana, mai taken ‘Raise Your Glass.’ D’banj ya fitar da wakar ne da hadin gwiwar kamfanin nishadantarwa na Hennessy a karshen makon da ya gabata.
Tuni wasu gidajen radiyo suka fara sanya somin-tabin wakar don nishadantar da mutane a Legas da kuma jan hankalin mutane game da abin da wakar ta kunsa.
Manajan kamfanin nishadi na Hennessy, Lere Awokokoya ya ce sabuwar wakar ta D’banj ta dace saboda irin abubuwan da ta kunsa na fadakarwa.
Ya ce: “Na yi imanin cewa mun sami abin da ya dace domin wakar ta dace da yanayi da kuma lokacin da aka yi ta. Babu shakka jama’a za su ji dadin wakar kuma za su amfana da ita.”
Kamfanin nishadantarwa na Hennessy ya dade yana hadin gwiwan da fitattaun mawaka a Najeriya kamar Banky W. da Eldee da M.I da NaetoC.
Sauran mawakan sun hada da Tiwa Sabage da Shina Peters da Nneka da sauran fitattun mawaka na ciki da wajen Najeriya.
Kamfanin ya fitar da wakoki daban-daban kamar wakar ‘Toast To The Goodlife’ wacce mawaki Banky W. da Eldee da Tiwa Sabage suka yi tare.