DBN ta karrama FCMB kan bunƙasa ƙananan sana’o’i a Najeriya
Hukumar ta ce bankin ya taka rawar gani wajen hana durƙushewar ƙananan sana’o’i.
Bankin First City Monument (FCMB), ya samu lambar yabo sakamakon yadda yake tallafa wa ƙananan sana’o’i, su samu bunƙasa da ci gaba a Najeriya.
A taron 2024 na Bankin Ci Gaban Najeriya (DBN) da aka gudanar a Legas, FCMB ya samu lambar yabo guda biyu.
- Tinubu ya kunyata waɗanda suka kyautata masa zato — Sarkin Yaƙin Yarbawa
- DAGA LARABA: Ribar Da ’Yan Najeriya Za Su Samu Daga Hulda Da China
An karrama shi kan tasirinsa wajen bai wa ƙananan sana’o’i bashi, da kuma bayar da gudunmawa wajen samar da ayyukan ci gaba.
A farkon shekarar 2024, FCMB ya bai wa ƙananan sana’o’i daban-daban bashin sama da Naira biliyan 180.
Wannan ya nuna jajircewar bankin wajen taimaka wa ƙananan sana’o’i da kuma gudunmawarsa ga ƙoƙarin ɗorewa muhalli a Najeriya.
Manajan-Daraktan Bankin, Hajiya Yemisi Edun, ta gode wa hukumar kan wannan lambar yabo da ta ba su.
Ta bayyana cewa bankin zai ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa ƙananan sana’o’i domin su taka muhimmiyar rawa wajen inganta tattalin arziƙin Najeriya.
Ta kuma ƙara da cewa bankin na da burin samar da alaƙa tsakanin mutane, kuɗi da kasuwanni a faɗin Afirka.
A cewar Hukumar Kula da Kididdiga ta Ƙasa, ƙananan sana’o’i suna bayar da gudunmawar kashi 48 na kuɗaɗen shiga a Najeriya.
A gefe guda, bankin ya ce wannan ya yi daidai da manufarsa ta bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.
Bankin ya kuma samu tallafin dala miliyan 280 daga Cibiyoyin Kuɗi na Ci Gaba (DFIs), a 2023 domin tallafa wa ƙananan sana’o’i, musamman na mata, da kuma ayyukan makamashi.
Tsarin ‘Quick-Loans’ na bankin, wata hanyar sadarwa ce, wadda ke sauƙaƙa wa ’yan kasuwa samun bashi, inda dubban mutane suke samun bashi kowane wata.
Daga watan Janairu zuwa Yunin, 2024, tsarin ya samar wa masu ƙananun sana’o’i biliyoyin Naira domin bunƙasa kasuwancinsu.
Taron na DBN wanda ke gudana duk shekara, na zaɓar bankunan da suka yi bajinta wajen tallafa wa ƙananan sana’o’i.
A taron na bana an yaba wa FCMB bisa jagorancinsa a ɓangaren bayar da bashi don samun ci gaba mai ɗorewa.