De Gea na fatan dawo da tagomashinsa a Man U.

Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da ke Ingila De Gea ya ce yana jin dadin zama a kungiyar kuma yana fatan zai dawo da tagomashinsa a kokarin da yake yi na dawowa buga mata kwallon kafa.De Gea mai shekara 24, bai buga wa Man. United kwallo a bana ba, yayin da […]

De Gea na fatan dawo da tagomashinsa a Man U.
De Gea na fatan dawo da tagomashinsa a Man U.

Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da ke Ingila De Gea ya ce yana jin dadin zama a kungiyar kuma yana fatan zai dawo da tagomashinsa a kokarin da yake yi na dawowa buga mata kwallon kafa.
De Gea mai shekara 24, bai buga wa Man. United kwallo a bana ba, yayin da mai horar da kungiyar Man U, kamar yadda ake kiranta a takaice Mista Louis ban Gaal ya ce golan yana bukatar natsuwa saboda zawarcinsa da Real Madrid ta yi masa a lokacin.
Sai dai kuma De Gea ya fara buga babban wasa a bana, inda ya buga wa tawagar kungiyar kwallon kafa ta kasar Spain wasa a fafatawar da ta yi da kasar Macedoniya a wasan neman gurbin shiga gasar cin Kofin Nahiyar Turai a ranar Talata.
Saura kiris De Gea ya koma Madrid da taka leda a bana, bayan da United ta amince golan ya koma Spain da wasa, amma kungiyoyin biyu suka makara wajen saka hannu kan yarjejeniyar sayar da shi.
Sabon mai tsaron raga da Man. United ta dauko dan kasar Ajentina Sergio Romero ne yake kama wa kungiyar wasa.