Dembele ya lashe kyautar balon d’Or ta bana

Balon d’or ita ce lambar yabo mafi girma da ake bai wa ɗan wasan ƙwallon ƙafa mafi bajinta a shekara.

Dembele ya lashe kyautar balon d’Or ta bana

Ɗan wasan gaban PSG da Faransa, Ousmane Dembélé ya lashe kyautar Ballon d’Or ta bana.

An bayyana ɗan wasan a matsayin wanda ya lashe kyautar ne a bikin da aka gudanar yammacin wannan Litinin a ɗakin taro na Theatre du Chatelet da ke birnin Paris a ƙasar Faransa.

Balon d’Or dai ita ce lambar yabo mafi girma a duniyar ƙwallon kafa wacce ake bai wa gwarzon ɗan wasa na shekara.

Tuni dai Aminiya ta ruwaito cewa Dembele yana cikin jerin manyan ’yan wasa biyar da aka fi ganin suna da damar lashe ta bana.

Dembele ya taka rawar gani wajen kai PSG ga nasarar lashe kofuna uku – gasar Ligue 1, Coupe de France da kuma kofin Zakarun Turai na farko a tarihin kulob ɗin.

Dembele ya ƙwallo 21 a wasa 29 da ya buga a gasar Ligue 1, inda ya ƙarƙare gasar a matsayin wanda ya fi zura ƙwallo, sannan ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan gasar.

Haka kuma, shi ne gwarzon ɗan wasan gasar Champions League, inda ya zura ƙwallo takwas, sannan ya taimaka aka ci shida.

Sauran waɗanda aka sanya su cikin jerin masu takarar lashe kyautar ballon d’Or ta bana sun haɗa da Lamine Yamal, Vitinha, Mohammed Salah, Raphinha, Kylian Mbappe, Cole Palmer, Gigio Donnarumma, Nuno Mendes, sai Achraf Hakimi.